← Book details Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 55

Sashe 53

Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da suka hau titi Safwan ya dubi Ummi ya ce. "Ina kwana." Ummi ta ce. "Lafiya ƙalau, ya aiki?" Ya ce "Alhamdulillah."
"Yau ka je aikin kenan?
Ya ce. "A'a, ban koma ba sai this coming Monday in sha Allah, saƙo Mum ta aike ni na kai mata gidan wata friend ɗinta." Gyaɗa kai Ummi ta yi tare da juyawa baya ta kalli A'isha da ta tsit kamar ba ta Motar, ta ce. "Nana ba ki gaishe da Yayanku ba." Numfashi ta sauke cikin sanyin murya ta ce. "Ina kwana." Ya amsa da "Lafiya." A taƙaice. Ba ta kuma magana ta mayar da idanunta ta lumshe, ƙamshinsa da ya kama motar da sanyin ac na ratsa ta. A lokacin kiran Mommy ya shigo wayarsa, dubawa ya yi, ganin ita ce ya ƙi ɗauka don ya san kwanan zancen. Ita kuma sai kira take ba ƙaƙƙautawa. Ganin haka ya sa Ummi ta ce masa. "Ka ɗaga kiran da ake maka mana." Yana sauke numfashi ya ce. "Mommy ce, idan muka ƙarasa zan kira ta."

A matuƙar hasale ta janye wayar daga kunnenta ta mayar da akalar kiran ga Khaltum. Ringing ɗaya ta ɗaga tare da faɗin. "Su Caska sun kira ni, wai har yanzu ba su ƙarasa ba." Kamar Mommy za ta yi kuka ta ce. "Ai komai ya wargaje Khaltum, wai Safwan ne ya tafi kai su."
"What? Safwan kuma? A kan me? Ko uban ne ya ce ya kai su?" Cikin ɗunbun baƙin ciki Mommy ta ce. "Ina fa? A yadda Buhari driver ya ce mini wai shi ya ce su fito ya kai su da kansa, tun ba yau ba nake faɗa matar nan fa ta asirce mini ɗa, tun yana rarrafe idan na aika aka ɗauko mini shi daga gurinta sai ya ƙara rarrafawa ya koma, na rasa yaya zan yi matar nan ta bar mini ɗana." Khaltum ta ce. "Kar ki damu Saratu, Gobe zan je gurin na kan tudu, zan saka a yi musu farraƙu, wannan duk ba wata matsala ba ne. Damuwata yanzu wargajewar aikin nan wallahi. Amma kuma ai kin faɗa mini likitar da ta yi wa yarinyar gwaje-gwaje last time da suka je kin san ta ko? Ta kira ni ta faɗa miki." Mommy ta ce. "Eh, ƙanwar Hajiya Zubaida ƙawata ce, tunda suka je ta gan su take kira na a waya ba ta same ba, sai bayan kwana biyu take faɗa mini." Khaltum ta ce. "To ai ta kwana gidan sauƙi, me zai hana mu haɗa baki da ita a ƙara lalata idon yarinyar." Murmushi Mommy ta yi ta ce. "Maganar da muke yi da ita kenan, don ta sanar mini tana sane ta ce su dawo bayan sati ɗaya saboda su zo ranar dutinta, ita duk ɗaukar ta ma Yarinyar Mufeedah ce." Khaltum ta ce. "Ni ma farko da na ga Yarinyar ranar da na zo na ɗauka ita ce, saboda suna kama sosai." Haka kawai Mommy ta ji gabanta ya faɗi da ta hasaso fuskar A'isha a cikin ranta, don ba ƙarya aka yi ba suna yanayi da Mufeedah ƴar Ummi. Kalar da fatarsu da girman jikinsu ɗaya. Taɓe baki ta yi ta ce. "Su suka sani, yanzu dai zan kira Doctor Zulaihat ɗin, duk yadda muka yi da ita za ki ji." Khaltum ta ce. "Ina sauraren ki." Daga haka suka yi sallama. Zama Mommy ta yi a kan kujera tare da dafe kanta, ta rasa me ya sa A'isha ta tsaya mata a rai, ba iya ƙin ta da take mata na talauci ne kawai ya sa ba ta son zamanta a gidan ba, har na fargabar da take ziyartar ta a duk lokacin da ta tuna da yarinyar ba tare da ta son dalili ba, shi ya sa ta damu ta bar gidan, saboda ko ma mene ne idan ta tafi shikenan.

Wani balaraben doctor suka samu yau, ya duba A'isha ya ƙara yi mata text a idon sannan ya ce su jira shi. After 1 hour ya fito da result ɗin abin da ke damun idon ya ba su bayan ya yi wa Ummi bayanin yadda yake. Ya ƙara da ce mata aiki za a yi wa idanun, ya faɗa mata kuɗin aikin tare da ba ta takardar da za a biya kuɗin. Farinciki sosai Ummi ta yi, tare da addu'ar Allah ya sa a yi aikin cikin nasara. Safwan yana mota suka fito hannunta riƙe da na A'isha. Tana buɗe baya za ta saka A'isha ta ce. "Safwan I'm sorry, na tsayar da kai kana ta jira." Murmushi ya yi ya ce. "Haba Ummi, babu komai ai." Takardun hannunta ta miƙa masa ya karɓa ya duba, bayan Ummi ta shiga front seat ta ce. "Daɗina da Asibitin nan komai nasu babu ɓata lokaci, idan muka yi payment a gobe cikin satin nan ma za su iya yi mata aikin." kallon A'isha ya yi ta madubi, ba tare da ya ɗauke idonsa daga kanta ba ya ce. "Allah ya sa a yi a sa'a." Ummi ta ce. "Amin, ka kai mu gidan Ruƙayya kawai mu ajiye ta a can, sai mu wuce ka sauke ni a school." Gyaɗa mata kai ya yi tare da kunna motar.

Aunty Ruƙayya tana sharar parlour suka shiga da sallama. Amsa musu ta yi tare da faɗin. "Sannun ku da zuwa, tun ɗazu nake dakon zuwan ku, na san yau ce ranar dawowar ku asibiti." Ummi ta zauna tare da faɗin. "Kuma da ba za mu zo nan ɗin ba wucewa za mu yi."
"Saboda me?"
"Kawai, har na cewa driver ya kai ta gidan Hajiya Zainab ta zauna kafin na dawo daga school, da ke kwana biyu can nake kai ta idan zan fita."
Aunty Ruƙayya ta ce. "Da ba ki kyauta mini ba kuwa."
"Ina kwana Aunty." A'isha ta faÉ—a cikin sanyinta."
"Lafiya ƙalau Mamana, ya fuska?"
"Alhamdulillah."
Ummi ta ce. "Cikin satin nan za a yi aiki ma in sha Allah." Aunty Rukayya ta ce. "Masha Allah, Allah ya sa a yi a sa'a." Suka amsa da Amin. Ummi ta ba ta takardun ta duba tare da faɗa mata yadda suka yi da likitan. Aunty Ruƙayya ta ce. "Haka na san asibitin Makka ba su da wasa, kana zuwa ana duba ka za a saka maka ranar aiki idan ciwon na aiki ne, shi ya sa na yi mamaki da kika ce an ba ku har 1 week ku dawo karɓar result." Ummi ta ce. "Ni ma na yi mamaki, har Abbansu sai da na yi wa complain, ya ce to ya za mu yi tunda haka suka ce." Aunty Ruƙayya ta ce. "Haka ne." Miƙewa Ummi ta yi tana duban A'isha ta ce. "Zan wuce Nana, Khalifa ko driver za su zo su ɗauke ki." Gyaɗa mata kai ta yi a hankali ta ce. "Allah ya kiyaye." Ummi ta ce. "Amin." Tare da juyawa ta fita, Aunty Ruƙayya ta bi bayanta don yi mata rakiya. Ajiyar zuciya ta sauke tana jin yadda tsoron aikin da aka ce za a mata ya cika mata zuciya, gani take kamar ko an yi aikin idon ba zai buɗe ba. Amma tana addu'ar Allah ya sa a yi cikin nasara, ita ma ta cigaba da gani kamar kowa. Numfashi ta sauke tana tuno mutane masu ƙololuwar daraja a cikin rayuwarta, wanda suke fata da burin ganin ranar barin ta daga makanta. Inna ce farko, wadda Ubangiji ya rubuta ba za ta ga wannan ranar ba, sai Umar da ba za ta taɓa mantawa da shi a cikin rayuwarta ba, duk da abin da take ji a kansa a cikin zuciyarta kaso mai yawa ya ragu, amma duk da haka ba za ta manta da Alkhairinsa ba, sai Innar Ma'u da ita kanta Ma'un, su kuma ba ta san a ina za ta gan su ba.

Lokacin da Safwan ya koma gida Mommy ba ta nuna masa ɓacin ranta ba a kan kai su Ummi asibiti da ya yi, saboda tsananin so da ji da shi ɗin da take ya sa ba ta iya yi masa faɗa. Sai dai tay ta zagin Ummi a gabansa tana cewa ba ƙaunar shi take ba, lunbu-lunbu take masa take jan shi a jiki, cikin ranta kuma tana da wani mugun nufin a kansa. Shi dai ba ya tanka mata idan tana maganganunta.

Salma na tsaye a gaban mirror tana kwalliya, wayarta dake kan mudubin ta fara ruri. Ɗauka ta yi ganin Fadeela ce tare da faɗin. "Ba dai har kun shirya ba?" Fadeela ta ce. "Tun yaushe? Ke kaɗai muke jira." Cikin fariya ta ce. "No ku wuce kawai ba sai kun jira ni ba, Mine ne zai kawo ni." Baƙi Fadeela ta taɓe ta ce. "Ok." Tare da katse kiran.

Ihsan tana koya A'isha karatun Alkur'ani a baranda Safwan ya shigo gidan. Tun kafin ya ƙaraso inda suke ƙamshinsa ya ziyarce su. Da sauri A'isha da ta san me ƙamshin ta ɗago kanta duk da gani take ba. Sallamarsa cikin kaushin murya ta saka Ihsan ɗagowa ta dube shi, cikin girmamawa ta ce. "Sannu da zuwa."
"Yawwa." Ya amsa idanunsa a kan wayarsa dake hannunsa. Miƙewa Ihsan ta yi tana faɗin. "Yayanku ya zo daukar ki, bari na sanar da Mami." Gyaɗa mata kai kawai A'isha ta yi tare da yin ƙasa da kanta. Kamar mai tsoron magana ta ce. "Ina yini?" Duk da ya san da shi take amma ko ɗagowa bai yi ba balle ya amsa. Ɓata fuska ta yi don ta tsani ta yi wa mutum magana ya ƙi amsawa, yadda ƙamshinsa ya cika mata hanci ta san yana kusa da itan da idan ta yi magana zai ji. Dawowar Ihsan da Aunty Ruƙayya ya sa ta sakin ajiyar zuciya, don duk jin ta take a takure kasancewar su kaɗai a guri ɗaya.
"Safwan kai ta kuma tasowa?" Cewar Aunty Ruƙayya tana duban shi.
Murmushi ya yi ya ce. "Ina yini?" Ta ce. "Lafiya ƙalau." Tare da mayar da duban ta ga Ihsan ta ce. "Kama hannunta ki raka su mota, kin ɗauko mata saƙonta dai ko?" Ihsan ta ce. "Eh gasu nan." Ta kama hannun A'isha da ta miƙe tsaye. Aunty ta ce. "To Mamana, ku gaida gida."
"Zai ji in sha Allahu, na gode Aunty."
Chapter 53 · 0% Book details