← Book details Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 55

Sashe 2

Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A'isha kuwa bayan barin ta ɓangaren su Ramatu cikin gida ta nufa tana bi ɓangare_ɓangare tana a ba su aran ashana, duk inda ta je da bak'ar magana da cin zarafi ake koro ta, amma hakan ba ya hana ta ƙara shiga wani gurin ta tambaya, dan ita burinta kawai ta samo ashana ta kaiwa Innarta ta yi ta hura wuta abun da ta ɗora ya dahu ta ci. Jiki a sanyaye ta dawo ɓangaren nasu, ta tarar wutar ma ta ruru Inna tana aikin azawa. Zama ta yi a ƙasa ta fara hawaye. Inna ta dube ta bata ce komai ba ta cigaba da abun da take yi. Tana hawayen ta ce. "Inna a ina kika samu ashanar?" Inna ta ce. "Ban sani ba, ina kiran ki dan iskanci shine kika yi gaba ko?" A'isha ta ce. "Ban ji ba fa Inna, kuma na je Innar Ma'un bata nan, na manta da safe dana biyawa ma'u makaranta ta ce baza ta je ba za su je unguwa." Inna ta ce. "Da kika ga bata nan sai kika je inda ban aike ki ba ko?" Shiru A'isha ta yi bata ce komai ba. Tana nan zaune har dankalin ya dahu Inna ta juye mata duka a roba ta bata, sannan ta shiga ɗaki ta ɗauko wani guntun k'uli_k'uli ta kawo mata dan ta haɗa ta ci da shi. Cikin sauri_sauri A'isha take cusa dankalin a bakinta tana ci, Inna tana zaune akan langa ta yi tagumi tana kallon ta, tunanin abun da zata yi na sana'a take yi dan zaman nan haka ba zai musu ba, Tunda Malam ya rasu suka shiga taskun rayuwa, abun da za su ci ma wataran gagarar su yake yi. Ta yi sana'oi da dama domin ta samu abun da za su rufawa kansu asiri amma kamar wadda aka sakawa hannu abun ba ya ci, sai ta fara an fara ciniki rumi_rumi Masha Allah sai abun ya lalace, wataran idan ta yi abun sai dai su cinye ta rabar da guntun dan ko na biyar babu wanda zai zo ya ce a ba shi. Ta rasa ma ina zata saka ranta...... "Inna gashi na ƙoshi ke ma ki ci." A'isha data ajiye mata guntun dankalin a gabanta ta katse mata tunani da faɗin haka. Inna ta sauke numfashi tana kallon kwanon dankalin ta ce. "Har ya ishe ki?" A'isha ta ce. "Eh na ƙoshi Inna." Inna ta sauke numfashi ta ce "Ɗauko murfi ki rufe kya ci anjima." A'isha data nufi gurin randa dan ɗiban ruwa ta sha ta ce. "Inna ki ci mana." Inna ta girgiza mata kai kawai bata ce komai ba. A'isha ta ɗibi ruwan ta sha ta yi hamdala sannan ta shiga ɗaki ta cire uniform ɗin jikinta ta zira kayan gida ta fito tsakar gida. Inna ta dube ta ta ce. "Ga ruwa nan akan wuta na ɗora miki, idan ya yi d'umi sai ki juye ki yi wanka kafin ki tafi karatun, ki je ɗaki zaki ga Naira goma a kan window, ki ɗauko ta sai ki ɗauki botikan can ki kai ki saka mana a layin fanfo, zan zo in ɗauka idan an zuba ruwan." A'isha ta turo baki gaba ta ce. "Inna da safe fa kafin na tafi boko na yi wanka, kuma yanzu in ƙara sakewa?" Inna ta ce. "Zaki yi abun da na ce ne ko kuwa?" Kamar zata yi kuka ta koma ɗaki ta ɗauko kuɗin ta fito ta sungumi bokatan guda biyu ta fice. Miƙewa Inna ta yi ta shiga ɗaki ta kwaso uniform ɗin da A'isha ta cire ta fito da su dan ta ɗauraye mata su bayan rufe guntun dankalin da A'ishan ta rage.

Gurin ɗiban ruwan a cike yake da mutane ƴan ɗiban ruwa yara da manya, mata da maza. Tunda A'isha ta ga haka ta ɓata fuska, dan ta tsani duk abun da zai haɗa ta da taron mutane a cikin garin, domin ta san baza su taɓa gwanyewa lafiya ba, tunda babu mai k'aunar su a cikin garin sai waɗanda baza a rasa ba, dan ba duka aka haɗu aka zama ɗaya ba, shi yasa bata k'aunar Inna ta turo ta gurin fanfon nan. Kasancewar garin suna da wahalar ruwa yasa aka yi tanki a wajen gidan mai gari, to duk mutanen dake kusa a nan suke ɗiban ruwa, shi yasa kusan kodayaushe gurin a cike yake da mutane. Kanta a ƙasa ta ƙarasa ta je gurin wanda ake bawa kuɗin ruwan ta gaishe shi tare da ba shi kuɗin. Ya amsa mata tare da karɓar kuɗin sannan ya nuna mata ƙarshen layi ya ce ta je ta saka buckets ɗinta. Bata yarda ta kalli kowa ba a gurin ta ƙarasa ta ajiye bokitan a hankali, duk da yanda kusan kowa na gurin yake kallon ta. Ta koma gefe ta tsaya kafin layi ya zo kanta. Mintuna biyu da tsayiwarta ta ji tsayuwar mutum a gaban ta, ko da ba'a faɗa mata ta san waye, Ɗan_juma ne ɗan gidan Mai gari, matashin Saurayi mai tashe a cikin garin, wanda bai da kirki da mutunci ko kaɗan, tun A'isha tana ƴar ƙaramarta ya takurawa rayuwarta, shi a dole son ta yake yi. Ɓata fuska sosai A'isha ta yi tare da kawar da kanta gefe. Ɗan_Juma ya riƙe k'ugu ya ce. "Ke! Dan na zo gurinki shine zaki wani kawar mun da kai kina wani ciccin magani, eye? A'isha ta watsa masa harara ta ce. "To Ni ina ruwana da kai, ba Innata ta ce karka ƙara kulani ba?" Ɗan_juma ya yi wata ƴar dariya ya ce. "Babu wanda ya isa ya hana ni kula ki A'isha duk garin nan wallahi, na gani kuma na yaba dole na samu, lokaci kawai nake jira ki ƙara girma a sha bikinmu." Turo baki A'isha ta yi ta ce. "To ni bana son ka, Allah ya sauwak'e na aure ka, kuma kar ka ƙara kula ni." Ɗan_juma ya haɗe rai sosai ya ce. "Ke! dan ma kin samu zan taimaka in aure ki shine kike faɗa mun magana? Wace ce ke?" A'isha ta murgud'a masa baki ta ce. "Mutum ce ni ƴar mutuwa jikar rasuwa kakar jana'ida." Kasancewar da ƙarfi Ɗan_juma yake magana yasa hankalin mutanen gurin gaba-d'aya ya dawo kansu. Wata budurwa ce wadda baza ta wuce 16 years ba ta ƙaraso inda suke tana faɗin. "Ni wallahi Ɗan_Juma na rasa me ka gani a jikiy wannan ƙwailar *MAYYAR* Yarinyar ka na ce mata haka, yarinyar da *SHEGIYA* ce *MARA ASALI*, ga mu nan ƴanmata birjik a cikin garin nan sai ka zaɓa ka darje amma ka bi ka lik'e mata." Ta ƙarasa zancen tana karkad'a ƙirji tare da jifan A'isha da wani mugun kallo. A kufule A'isha ta dube ta, ta ce. "Ke Hindu kar ki ƙara ce mun Mayya ko shegiya, ni ba Mayya ba ce kuma ba Shegiya ba ce." Kamar Hindu zata kai mata duka ta ce. "An faɗa ɗin Shegiya Mayya me zaki yi mun? da mece ce ke idan ba mayyar ba, kuma idan ke ba Shegiya ba ce waye Ubanki a cikin garin nan?" A'isha ta fashe da kuka ta ce. "Wallahi ni ba Mayya ba ce, kuma Baba Malam shine Babana.".........✍️

_*Tafiyar fa mai nisan zango ce, Allah ya bani ikon yin posting kullum🥹*._

*By*
*Zeey Kumurya*
*💖 KOMAI NISAN DARE.....! 💖*

_By_
_Zeey Kumurya_

*ELEGANT ONLINE WRITER'S*

*0️⃣2️⃣*

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 08066268951

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
Chapter 2 · 0% Book details