← Book details Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 55

Sashe 19

Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

...........Daren yau Inna ba ta iya runtsawa ba saboda tunanin wannan lamura iri_iri da suke faruwa da su, Tunda Ubangiji ya kawo su cikin garin nan zuciyarta ba ta huta ba, kullum da sabon al'amarin da yake riskar su na tashin hankali, amma duk ciki babu abun da ya fi firgita ta da tsorata ta kamar wannan yunk'urin yiwa A'isha fyaɗen aka yi, imagine take inda hakan ya kasance wataƙila da tuni tana k'iyama, dan ta san tsaf zuciyarta za ta iya bugawa saboda baƙin ciki. Ga wani tashin hankalin da yake risko su a gaba, wato dawowar Ƴaƴan Iya Maza gida da k'annen Malam waɗanda suke kasuwanci a Lagos, a bakin matan gidan ta ji suna zancen dawowar tasu. Duk ba su fiya shiga harkar ta ba amma Iya na zuga su su yi mata wulaqanci da tijara, guda ɗaya ne mai suna Yunusa wanda shine autansu Malam yake yi mata mutunci a cikin Mazan gidan.....Lokuta da dama idan abu ya ishi Inna ta kan ji dama su tattara kayansu su bar garin, kamar yau da aka yi yunk'urin ɓata mata rayuwar ƴa, sai dai idan ta tuna ba ta da gurin zuwa idan ta bar nan ɗin yakan saka dole ta hak'ura su ci-gaba da zaman. Washegari A'isha ta tashi da zazzaɓi da ciwon kai da ciwon jiki duka. Wajen ƙarfe takwas na safe Inna ta siyo musu koko da k'osai a gurin matar da ita kaɗai take siyar musu a cikin garin, dan Inna ba ko ina take zuwa siyayya a siyar mata da abu ba. Amma saboda rashin kunya ita a lokacin da ta yi sana'o'inta sai a zo a siya, saboda araha take yi sosai a kayan nata. A lokacin innar Ma'u kan yi dariya ta ce. "Gaskiya halin mutane sai su, suna ƙin ka da gudun ka rab'e su amma saboda son banza idan kana siyar da abu da sauƙi sai a zo gurinka a siya, idan har ƙin na Allah ai ko kyauta ka kasa abu ba'a zo a ɗauka ba." Inna kan yi murmushi kawai idan ta faɗi haka.

Bayan Inna ta d'ibarwa A'isha abun karinta ta zauna a gabanta cikin kulawa ta ce. "A'isha daure ki tashi ki karya, kin ga babu komai a cikinki, jiya ma haka kika ƙi cin funkasau da na zo da shi." Cikin muryar marasa lafiya A'isha ta ce. "Inna ba zan iya ci ba, bakina ɗaci." Inna ta ce. "Daurewa za ki yi ki sha ko kokon ne." Girgiza kai A'isha ta yi tare da kawar da kai. Daƙyar Inna ta lallame ta, ta sha kokon kaɗan ta koma ta kwanta. Ganin haka Inna ta ce. "Bari na yi wanka sai na je na siyo miki maganin zazzaɓin idan masu chemist ɗin sun fito." Gyaɗa mata kai kawai A'isha ta yi. Bayan Inna ta yi wanka ta gama kimtsa gidan ta karya sai ta nemi guri ta zauna, jin shiru_shiru A'isha ba ta ji Inna ta ce za ta tafi gidan Hajiya Talatu ba, ta daure cikin magana daƙyar ta ce mata. "Inna sai rana ta yi ba ki tafi gidan abincin sadakar ba?" Inna ta ce. "Ba zani ba A'isha tunda ba kya jin daɗi." A'isha ta ce. "Inna akan me? Ba sai in zauna ki je ki dawo ba?" Inna ta ce. "Zance ma kenan, ai ko nan da can ba zan ƙara tafiya in bar ki ba, tunda an fara farautar rayuwarki, hanyar lafiya a bi ta da shekara, da dai ma lafiyarki ƙalau ne sai in saka ki a gaba mu tafi tare." Cikin wauta A'isha ta ce. "Inna kashe ni suka so yi ko? Tunda sun kwantar da ni sun daddanne ni, ina jin ma da wuk'a a hannunsu yanka ni suka so yi." Inna ta ce. "Uhm." Kawai. Aisha ta ce. "Mugaye kawai, ina jin wannan mutumin mai ƙamshin nan ne ya gan su ya k'wace ni." Inna ta ce. "Kin fara jin sauƙi kenan tunda har kike wannan surutun." Shiru A'isha ta yi ba ta kuma magana ba, sai bayan kusan mintuna biyar ta ce. "Inna ki tafi gidan aikinki kawai, sai ki kulle ni a ɗaki ki je ki dawo." Inna ta ce. "Saboda gani kuntacciya ko? Baki da lafiyar zan kulle ki a ɗaki in tafi wani gurin, idan wani abun ya same ki fa?" A'isha ta turo baki ta ce. "To Inna idan ba ki je ba a ina za mu samu kuɗi? Kuma ni abincin sadakar nan kawai nake son ci yau." Shiru Inna ta yi tana kallon A'isha, tabbas maganganunta suna kan turbar gaskiya, dan ɗan kuɗin da ta samo jiya babu abun da zai yi musu a cikin sati guda, amma idan ta je aikin ta ƙara samowa za su ɗan rage. Miƙewa ta yi ta ce. "Bari na kai ki gidan Sahura mai k'osai ki zauna a can kafin na dawo, na san za ta kula da ke yanda ya kamata. Sai na yi sauri na kammala aikina na dawo da wuri."

Ƙarfe goma sha biyu na rana Matashin nan ya fito daga cikin gidan Sarki. Sanye yake cikin ƙananun kaya wanda suka matuƙar yi masa kyau, sai tashin daddaɗan ƙamshinsa yake yi. Cikin nutsuwarsa yake tafiya zuwa gidansu A'isha, a ƙofar gidan ya tsaya yana kalle_kalle ko Allah zai saka ya ga wani yaron ya aika shi ya yi masa magana da Inna. Cikin ikon Allah sai ga wani yaro ya fito daga cikin gidan. Kiransa ya yi sai kuma ya rasa wa zai ce ya kira masa, yana son ya tuno sunan da Inna ta kira A'isha da shi jiya amma ya kasa. Sai kawai ya cewa Yaron. "My friend Matar gidan zaka yi mun magana da ita idan tana nan." Yaron ya ce. "Wacce daga ciki? Dan matan gidan nan sun fi goma." Shiru ya ɗan yi na wasu sakanni sannan ya ce. "Ban san sunanta ba, amma fara ce mai ɗan jiki, tana da yarinya mai kyau, yarinyar kuma kamar ba ta gani." Yaron ya ce. "Oh wai Asabe Mayya kake nufi?" Cikin mamaki Matashin ya ce. "Mayya kuma?" Yaron ya ce. "Eh, ai Mayya ce, A'isha ma da ba ta gani ai idon wasu suka cinye aka dawo musu da abun kansu, da alama kai baƙo ne a cikin garin nan shi yasa baka sani ba." Kallon yaron kawai yake with more shocked bai ce komai ba, yanda yaron ya dage yana yi masa bayani sai ka ce wani babba. Murmurshi ya yi ya ce. "Yanzu dai tana nan ka yi mun magana da ita?" Yaron ya ce. "Tab', ai ba ma yi musu magana saboda kar su cinye mu, an hana mu gaskiya." Daga haka yaron ya yi gaba abin sa, bin sa ya yi da kallo maganganun yaron na yi masa yawo a cikin kai, musamman sunan A'ISHA da yaron ya ambata. Yana nan tsaye sai ga su Inna su karyo kwana ita da A'isha dake tafiya daƙyar. Ajiyar zuciya ya sauke ya ƙurawa A'isha ido gabansa na fad'uwa. Tunda Inna ta hango shi ta gane shi, A'isha da ba ta gani suna ƙarasowa kusa da shi ta ce. "Laa Inna na ji ƙamshin mutumin jiya." Inna ba ta ce mata komai ba, shi kam murmushi ya yi cikin girmamawa ya ce. "Sannu da zuwa Mama, Ina Yini?" Cikin fara'a Inna ta ce. "Yawwa, lafiya ƙalau, ka zo kenan? Allah yasa ba ka dad'e kana jira na ba." Kansa a ƙasa ya ce. "A'a ban jima da zuwa ba." Inna ta ce. "Bismillah mu shiga daga ciki to." Sai da suka shige sannan ya bi bayansu. Inna ta shimfid'a masa tabarma a tsakar gida ya zauna, duk da tsakar gidan ƙasa ne babu siminti amma Inna ta yayyafa masa ruwa ta share shi tass, sai ƙamshin ƙasa ne ke tashi a cikinsa. Inna ba ta zauna ba sai da ta kawo masa ruwan randa mai sanyi gami da abincin da suka shigo da shi. Ruwan kawai ya sha ya yiwa Inna godiya sannan ya gyara zama ya ce. "Mama dama na zo ne akan abun da ya faru jiya, ban sani ba ko A'isha ta faɗa miki?" Inna ta sauke numfashi ta ce. "Ta sanar mun da komai." Ya ce. "Amma Mama ba ta gani me yasa ake barin ta take fita ita kaɗai?" Inna ta ce. "Ba ta zuwa ko'ina ita kaɗai wallahi, jiyan ma tsautsayi ne Allah ya kawo, amma insha Allah hakan ba za ta kuma faruwa ba." Ya ce. "Allah yasa, Allah ya kiyaye gaba." Inna ta ce. "Amin, Amin, na gode sosai fa Allah ya saka da Alkhairi." A hankali ya ce. "Amin." Yana satar kallon ɗakin Inna da A'isha ke ciki, wadda tunda ta ji muryarsa ta yi tsit kamar ruwa ya cinye ta. Inna ta ce. "A'isha ta faɗa mun kai ka k'wace ta daga hannun azzaluman ko?" Gyaɗa mata kai ya yi sannan cikin sanyin murya ya ba ta labarin abun da ya faru. With more shock and concern Inna ta ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, Ɗan_juma kuma? Yanzu duk bibiyar yarinyar nan da yake yi dama da wata mummunar manufa ne?" Matashin ya ce. "Ya daɗe yana bibiyar ta ne dama? Amma ba ku ɗauki mataki ba?" Inna ta ce. "Nunawa kawai yake yi yana son ta tun tana ƴar ƙanƙanuwarta, ashe son ba na Allah ba ne." Girgiza kai ya yi ganin yanda hankalin Inna ya tashi ya ce. "Ok, babu damuwa, insha Allah komai ya zo ƙarshe Mama, zan sanar da Baba Sarki duk abun da ya faru, na san kuma zai ɗauki mataki akan hakan." Inna ta ce. "To na gode sosai, Allah ya saka da Alkhairi." Miƙewa ya yi ya ce. "Bari na wuce Mama, na ga lokacin Sallah ya gabato." Inna ta ce. "Har zaka tafi ba, to ba ka ci abincin ba kuma." Murmusawa ya yi ya ce. "Alhamdulillah, na gode." Inna ta ce. "To ka gaida gida, Na gode sosai."
Chapter 19 · 0% Book details