Sashe 42
Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Ƙarfe takwas da mintuna Khalifa ya ɗauko Ya Maamah daga airport, direct asibitin ya wuce da ita. Da kwatancen da Abba ya yi masa suka ƙarasa har ɗakin da suke. Ummi tana waya suka shiga da sallama. Bayan ta gama ta amsa musu tare da faɗin. "Sannun ku da zuwa, I'm sorry Ina waya ne da can school Ina sanar musu ba zan samu zuwa ba yau, kin sauka lafiya Maamah?"
"Lafiya ƙalau Ummi, ashe abin da ya faru kenan? Allah ya kiyaye gaba" Ummi ta ce. "Amin, abun ba daɗin ji, amma babu yadda za mu yi tunda Ubangiji ya ƙaddaro." Ya Maamah ta ce. "Haka ne, wannan ce yarinyar?" Ta ƙarasa maganar tare da tashi ta koma gaban gadon da A'isha take.
"Ita ce, wadda ta rasun kuma Mahaifiyarta ce, ƙarin abun tausayi ashe makauniya ce." Da sauri Khalifa da ya ƙura wa A'isha ido ya ce. "Wace makauniyar?" Ummi ta ce. "Yarinyar."
"Innalillahiwa'inna'ilaihirra'ji'un, Allah Sarki, Allah ya ba ta lafiya." Ya Maamah ta faÉ—a cikin tausayawa. Ummi ta amsa da "Amin." Khalifa kam kasa magana ya yi saboda tsananin mamaki da tausayi. Idanun Ya Maamah a kan A'isha ta ce. "Ba a samu Æ´an'uwansun ba har yanzu?"
"Ba a samu ba, ita yarinyar da aka tambaye ta ma cewa ta dinga yi ba su da kowa, amma ta faɗi daga inda suke, wani gari ne a cikin Kanon nan Kumurya." Da mamaki Khalifa ya ce. "Ai kuwa ina jin sunan garin nan, amma na rasa a inda na san shi." Ummi ta ce. "Abbanku ya ce babu nisa, tun jiya ma ya so su je, amma yanayin jikin yarinyar ya sa ya ce a bari ta samu lafiya sai su tafi har ita." Jinjina kai Ya Maamah ta yi, ita kam ta kasa daina kallon A'isha, lokaci ɗaya tausayi da ƙaunar ta suka cika mata zuciya. Wajen ƙarfe tara Aunty Ruƙayya ƙanwar Ummi ta zo asibitin ita ƴaƴanta, a kallon farko da ta yi wa A'isha ta ji gabanta ya faɗi ba tare da ta san dalili ba, ba ta ɗauki hakan da wata manufar ba ta zauna aka cigaba da jajanta al'amarin. Sai bayan Azhar A'isha ta farka, Alhamdulillah ta farko cikin hayyacinta. Ummi ta haɗa mata tea ta rarrashe ta, ta sha kaɗan da ƙyar. Ba jimawa ta ƙara komawa bacci, saboda Allurar da aka mata ba ta gama sakar ta ba.
Bayan kwana uku
Jikin A'isha ya yi sauƙi sosai, ta daina koke-koken da take yi. Sai dai ba ta magana kwata-kwata, duk abin da aka ce mata sai dai ta gyaɗa kai. Kulawar da su Ummi suke ba ta ya sa ta fara samun nutsuwa a cikin ranta. Ga Abba kodayaushe idan ya zo asibitin cikin yi mata nasiha akan yarda da ƙaddara yake, hakan ya sa ta fara dangana da rashin Inna, amma da zarar ta tuno ba ta kowa a duniya a halin yanzu kuma ba ta san inda rayuwarta za ta kaya mata ba sai hankalinta ya yi mugun tashi. An yi wa Inna Addu'ar uku da safe a masallaci gami da abubuwan toye-toye na sadaka. Kafin Azhar aka sallami A'isha. Da yamma bayan ta yi wanka ta rama sallolin da suke kanta Ummi ta kama hannunta suka je parlour'n Abba. Suna zaune da shi da Khalifa suka shiga, tunda suka shigo Khalifa ya ƙura mata ido cikin wani irin yanayi. Yadda take tafiya da yin komai a sanyaye shi yake ƙara masa tausayin ta a cikin ransa. A kan carpet Ummi ta zaunar da ita. Cikin sanyin muryar da ta dashe ta ce. "Ina Yini." Abba ya amsa mata cikin kulawa sannan ya ɗora da faɗin. "Yaya jikin naki? Ina fata yanzu kin daina jin jirin da nauyin ƙirjin?" Ɗaga masa kai ta yi a sanyaye.
"Ciwon kan fa?"
"Shi ma ya daina sai kaɗan-ƙadan." Ta faɗa kamar mai koyon magana. Cikin jin daɗi Abba ya ce. "Masha Allahu, Allah ya ƙara lafiya." Gabaɗaya suka amsa da Amin. Gyara zama Abba ya yi tare da fuskantar ta sosai ya ce. "Yau kwana uku da rasuwar mahaifiyarki, kuma har yanzu cikin danginku babu wanda ya sani, na so a ce mun je garin naku tun ranar da al'amarin ya faru don mu sanar musu, amma saboda rashin sanin Ina za mu tunkara idan mun je ya sa muka dakata har ki samu lafiya ki yi mana jagora. Kuma yanzu nake son mu tafi, ba na son a ƙara kwanaki ba mu je ba, saboda sanin yanzu duk wani makusancinku hankalisa a tashe yake da rashin sanin inda kuke."
Hawaye masu É—umi ne suka sauka a kan kuncinta, cikin rawar murya ta ce. "Ba mu da kowa, ko an mun je garin ban san wurin wanda zan kai ku ba." Shiru Abba ya yi yana nazari akan maganar ta, a hankali ya sauke numfashi ya ce. "Ina mahaifinki?"
"Ya rasu."
Ta ba shi amsa cikin kuka. Girgiza kai Ummi ta yi ta ce. "Yi haƙuri ki bar kukan haka ki yi mana yadda za mu gane, saboda babu yadda za a yi a ce kuna rayuwa ku biyu babu dangi, ina ƴan'uwan mahaifinki da na mahaifiyar taki?" Cikin sheshshek'a ta ce. "Duk ban san su ba, ban san inda suke ba, Innata kawai na sani."
"Kuma ba ta faÉ—a miki inda suke?"
Abba ya tambaye ta cikin mamaki. Gyaɗa masa kai ta yi. Ummi ta ce. "Ikon Allah, ku kaɗai kuke zaune a gidanku kenan?" Girgiza mata kai ta yi alamar a'a. Abba ya ce. "Allah ya kyauta, amma na kasa gane kan wannan al'amarin." Ajiyar zuciya A'isha ta sauke tare da share hawayen fuskarta ta fara ba su labarin rayuwarsu da irin wahalar da suka sha, don ta sauƙaƙa musu tambayoyin da suke mata. Bayan ta gama ta ɗora da faɗin. "Don Allah kar ku mayar da ni gurinsu, wallahi kashe ni ne kawai ba za su yi ba saboda ba sa san mu, ku bar ni kawai na tafi wani gurin." Ta ƙarashe maganar cikin gunjin kuka. Cikin matuƙar tausayawa Ummi ta rungume ta tare da faɗin. "Ki kwantar da hankalinki Mamana, babu mai mayar da ke gurinsu kin ji?" Ajiyar zuciya ta sauke tare da ƙara fashewa da kuka, kewar Inna da zafin mutuwar ta na ƙara cika mata zuciya. Numfashi mai zafi Khalifa ya fesar cikin takaicin jahilcin wasu mutanen, daga mutane sun zo garinku cin arziƙi don ba ku san su ba sai su zama abin muzantawa da ƙyara a gurinku? Saboda rashin ilimi. Abba da yake jin kamar ya zubar wa A'isha hawaye saboda tausayi ya ce. "Allah ya ji ƙan mahaifiyarki, ya inganta rayuwarki har ki zamo abar alfahari. Ki daina kukan nan haka kar ciwon ki ya dawo." Jinjina masa kai ta yi amma ta san ba za ta iya tsayar da hawayen dake fita daga idonta ba a yanzu.
"A'isha!"
Abba ya kira ta cikin taushin murya.
ÆŠagowa ta yi daga jikin Ummi ta amsa masa a raunane.
"Na'am."
"Kin tabbata labarin da kika ba mu gaskiya ne?"
"Gaskiya ne Abba, idan ba ka yarda ba ka je garin ma ka tambaya za a faÉ—a maka."
GyaÉ—a kai ya yi cikin gamsuwa sannan ya dubi Khalifa ya ce. "Je ka kirawo mini Maamah da Baby da Saratu." Cikin ladabi ya amsa tare da miÆ™ewa ya bar parlour'n........âœï¸
*💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖
*_Zeey Kumurya_*
*ELEGANT ONLINE WRITER'S*
*2ï¸âƒ£5ï¸âƒ£*