← Book details Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 55

Sashe 22

Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau ya kama ranar Juma'a, sati biyu da haɗuwarsu A'isha da Umar. Da yamma Inna tana wanka A'isha ta lallab'a ta fita ƙofar gida ta tsaya tana kallon hanya kamar mai ganin masu wucewa, Umar yana bakin masallaci ya hango ta, da yake masallacin opposite ɗin layinsu Aisha yake. Cikin mamakin yanda ta iya fitowa ya miƙe ya ƙarasa ƙofar gidan nasu. Tana can duniyar tunani ba ta ma san ya ƙaraso ba, key ɗin ɗakinsa ya ɗauko a aljihunsa ya shiga karkad'awa a wajen kunnanta. Ɗan zabura ta yi fuskarta na nuna alamun tsoro ta ja baya. A hankali ya ce. "I'm sorry na tsora ta ki ko?" Ajiyar zuciya ta sauke ba ta ce komai ba sai ɓata fuska da ta yi. Murmusawa ya yi ya ce. "Tunanin me kike har na zo nan ba ki sani ba?" Canzawa fuskarta ta yi ta koma kalar damuwa, cikin sanyin murya ta ce. "Jarrabawa za mu fara ranar Monday, ni kuma ban san ta yaya zan yi ba." Kama hannunta ya yi suka zauna akan dankalin dake ƙofar gidan ya ce. "Kafin nan, wa ya fito da ke nan?" Ta ce. "Da kaina na fito." Ya ce. "Amma Mama ba ta sani ba ko?" Ta ce. "Eh wanka take yi, ni kuma na gaji da zaman gida." Ya ce. "Ta yaya kika fitowa?" Ta ce "Ai na san hanya, kawai bi nake yi a hankali." Shiru ya yi yana kallon ta cike da tausawa na wasu sakanni sannan ya ce. "Me yasa idan kika gan ni ba kya gaishe ni?" Cikin shagwab'a ta ce. "Kai ma ai baka mun magana sai dai ka gaishe da Inna kawai." Ya ɗan lumshe ido ya buɗe ya ce. "To na daina, daga yau zan dinga yi miki magana, ai mun zama Friends ko?" A'isha ta ce. "Kai! ta yaya? Kai fa Namiji ne." Ya ce. "Eh duk da haka, ni dai kin zama ƙawata." Dariya A'isha ta yi ta ce. "Tab', so kake Inna ta zane ni ina abota da Namiji?" Ya ce. "Ai zan faɗa mata da kaina." A'ishah ta ce. "Wai kai ina ne gidanku?" Ya ce. "Gidan Sarki." A'isha ta ce. "Amma ya aka yi ban san ka ba tun daa? Inna ma haka." Ya ce. "Wasa nake miki, gidanmu ba'a nan garin yake ba, wani abu ne ya kawo ni garin nan akan karatuna." A'isha ta ce. "To a ina kuke?" Ya ce. "Kaduna State, kin san garin?" Girgiza masa kai ta yi ta ce. "Sarkin Ɗan'uwanku ne?" Ya ce. "Abokin Abbanmu ne." Ta ce. "Me kake yi a garin nan to?" Ya ce. "Gona nake zuwa da sassafe kullum ina duba abu." Ta ce. "Yaushe zaka tafi?" Ya ce. "Sai an ɗan daɗe." Dai-dai nan Inna ta lek'o dan duba A'isha, ajiyar zuciya ta sauke ta ce. "Sannu A'isha." A'isha ba ta ce komai ba dan ta san ta yi laifi, shi kuwa ƙasa ya yi da kansa ya gaishe da Inna, ta amsa cikin fara'a sannan ya tashi ya tafi, yana jin zuciyarsa cike da Nishad'i sanadiyyar kasancewar su da A'isha. Ita ma ji ta yi dama kar ya tafi ya zauna su yi ta hira, tunda su Ma'u suka tafi ba ta da abokin hira, ko a makaranta sai dai ta zauna ta yi shiru ita kaɗai. Jiki a sanyaye ta tashi Inna ta kama hannunta suka shige gida. A hankali a hankali Umar yake shiga jikinsu Inna, dan kullum sai ya zo har gida ya gaishe da Inna tare yi musu Alkhairi. Cikin lokaci kaɗan suka saba da shi sosai, Inna ta yaba da hankali da nutsuwarsa shi yasa ta saki jiki da shi, zuciya tana son mai kyautata mata, Umar sai ya zamowa A'isha tamkar madadin Ma'u, dan mayar da kanshi yake yaro kamarta su yi ta hira cikin barkwanci. Cikin wata guda ya fahimci irin rayuwar da suke yi a cikin garin ta matsin rayuwa da ƙyarar su da ake yi, tausayinsu ne ya ninku a cikin zuciyarsa, hakan yasa ya ɗauki damarar taimaka musu har sai inda ƙarfinsa ya ƙare. Tun daga kan kayan abinci da komai na buƙatar rayuwa ya siyo mai ɗan yawa musu ya kawo musu, Inna ta dinga yi masa faɗa tana cewa kayan sun yi yawa ita baza ta karɓa, daƙyar ya lallab'a ta, ta karɓa. Ai kuwa ya sha addu'oi da tarin godiya. Mutan gidan sai yawo suke yi da inna a cikin gari suna cewa daga yin baƙo daga birni Inna ta lashe masa kurwa kullum yana jikinsu yana yi musu uban hidima yana wahala da su. Sarki kuwa yana sane da duk abun da yake faruwa, hakan ma shi daɗi ya yi masa, ya dinga sakawa Umar albarka akan taimakon su inna da yake yi. Su A'isha sun yi jarrabawa a makaranta, amma ita ba ta yi ba tunda ba ta gani, an yi hutu, hutun kuma mai yawa kasancewar idan an dawo sabon aji za'a shiga. Tunda aka yi hutun kullum da safe sai Umar yake yiwa A'isha lesson da baki (Oral), kuma Alhamdulillah tana ganewa, dan har words ɗin English yake koya mata, da yamma kuma su yi karatun Alkur'ani da tarihin Annabawa, da karatun su fiqhu.

Yau da safe wajen ƙarfe goma sha ɗaya na safe A'isha na zaune akan tabarma a tsakar gida tana aikin b'ab'b'ata fuska tare da turo baki gaba, saboda Inna ta yi mata faɗa akan barnar ruwan da ta yi mata da sunan zata yi mata wanke_wanke ba tare da ta saka ta ba, Umar ne ya shigo gidan cikin shirinsa na manyan kaya, ya yi kyau sosai ya fito a matashinsa na ɗan 25 years. Tun kafin ya ƙaraso cikin zagayen su Inna ƙamshinsa ya riga shi zuwa, cikin kamilalliyar muryarsa ya yi sallama. Suka amsa mata a tare. Cikin girmamawa ya tsugunna ya gaishe da Inna dake cikin madafi tare da yi mata sannu da aiki, ta amsa cikin fara'a sannan ya ƙarasa ya zauna a kusa da A'isha. A hankali ya ce. "Good Morning." Shiru ta yi masa. Yana kallon yanda ta cukule ta kumbura k'iris take jira ta fashe ya danne dariyar dake cin sa ya ce. "Yau babu magana ne Indo?" Kamar za ta yi kuka ta ce. "Ya Umar na ce ka daina ce mun Indon nan?" Ya ce. "To ai na fi son na kira shi da sunan ya fi mun daɗi." Cikin shagwab'a ta ce. "Ni dai gaskiya bana so, sai ka ce wata tsohuwa?" Shiru ya yi yana kallon ta tare da sauraren yanda zuciyarsa ke bugawa a hankali. After some seconds ya sauke ajiyar zuciya ya ce. "To na daina HUMAIRAH." murmurshi ta yi ta ce. "Yawwa Yayana, ai gara Humairan da wani Indo." Murmurshi ya yi tare da yin ƙasa da murya ya ce. "Kin yi kyau sosai Bestie." A'isha ta ce. "Amma ban kai ka ba ko? Na san kai kyakkyawa ne." Ya ce. "Taɓ, a yi shiru dai kawai." Kallon sa ta yi ta ce. "Ina son na gan ka Ya Umar." Yanda ta yi maganar cikin raunin murya sai ta tsinkar masa da zuciya, a hankali ya ce. "Za ki ganni watarana soon Insha Allah." Ta ce. "Allah yasa." Lesson ɗin ya shiga yi mata bayan sun ɗan yi revision akan na jiya ya ƙara tuttuna mata abun da ta manta. Suna cikin karatun wayarsa ta yi ƙara alamar shigowar kira, ɗaukowa ya yi ya duba, ganin mahaifiyarsa ce ya daga ya kara a kunne tare da yin sallama. Daga can bayan ta amsa sallamar ta ce. "Ka kira ni ina part ɗin Abbanku, wayar kuma tana ɗaki sai yanzu da na dawo na gani." Ya ce. "Ok, an tashi lafiya Mom? Ya su Abban da Mufeedah?" Ta ce. "Suna nan lafiya ƙalau, da fatan kai ma haka?" Ya ce. "Alhamdulillah, sai dai kewar ku kawai da nake yi Mom." Mom ta ce. "Yaushe zaka dawo ne? Na ji Abbanku yana wai sai nan da 1 month." Ya ce. "Eh haka ne." Mom ta ce. "Uwar me zaka yi har na 3 months a wannan ƙauyen? Me yake damun ka ne Faruq?" Cikin kwantar da murya ya ce. "Mom ban gama abun da na je yi ba ne." A fusace ta ce. "Ai baza ka taɓa gamawa ba, ko aikin uban me ne ai zuwa yanzu ya ci ace in ma haddacewa ne ka yi ba iyawa kaɗai ba. Kawai kana son ka ɓatan rai ne Faruq, amma ka san ba son zamanka a ƙauyen nan nake ba, yanzu kafin ka dawo na san duk sai ka yi baƙi ka fita daga hayyacinka ka koma kalar ƴan garin." Umar ya ce. "Haba Mom dan Allah ki yi hak'uri, garin fa akwai daɗin zama, yanda kike tunaninsa ba haka yake ba, dan suna da abubuwan...." cikin hasala ta katse shi da faɗin. "Kai ka san wannan, ni dai abun da zan faɗa maka nan da 1 week ka haɗa kayanka za'a zo a ɗauke ka, zaman ƙauyen naka ya ishe ni haka. Ko ka gama abun da ka je yi ko ba ka gama ba is not my concern." Cikin damuwa ya ce. "Amma Mum......" A fusace ta ce. "Umarni nake baka Faruq, idan kuma ban Isa ba ne sai in ji......Ka je ka zauna a ƙauye for almost two months bai ishe ka ba sai ka ƙara wasu kwanakin, salon ka saba da ƴan garin har bayan ka dawo ka dinga mu'amala da su....To ba zai yiyu ba wallahi, wannan zaman ma da ka yi ba ƙaramin hak'uri na yi na danne zuciyata ba, dan dai babu yanda zan yi ne tunda Mahaifinka ya ce dole sai ka je. Sanin kanka ne ka san ni sarai bana son tarayya da TALAKA da duk wani abu da ya danganci TALAUCI, balle kuma TALAKAN ma na ƙauye!" K'wafa ta yi ta cigaba da magana cikin ɗacin rai da faɗin. "Kamar ni a ce ɗana ya tafi wani ƙauye yana rayuwa a can na tsawon watanni? this is too much shameful thing for me." Shiru Umar ya yi ya rasa me zai ce mata, tsaki ta ja tare da kashe wayarta............✍️

*FAUZARH ORGANIC SKINCARE*
_PRESENT_

*5️⃣ DAY'S SKINCARE ONLINE TRAINING*

*💗ABUBUWAN DA ZAN KOYAR💗*
Chapter 22 · 0% Book details