← Book details Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 55

Sashe 51

Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tana haÉ—a kaya a wardrobe ya shiga bakinsa É—auke da Sallama. Ba tare da ta bar abin da take ta amsa masa ba yabo ba fallasa.
"Sannu da aiki Ummi." Ya faÉ—a yana zama a kan carpet É—in dake gaban gado.
"Yawwa." Ta amsa masa still tana cigaba da shirya kayanta. Ganin yanayinta ya san fushi take da shi akan abin da ya faru. Cikin murmushi ya ce. "Zuwa fa na yi mu yi hirar yaushe gamo Ummina." Ummi ta ce. "To Bismillah mu yi mana, ya hanya? Da fatan kun dawo lafiya?" Cikin jin daɗin yadda ta saki fuska ya ce. "Lafiya ƙalau Alhamdulillah, da fatan mun same ku lafiya?"
"Alhamdulillah, ai na É—auka Æ´ar gold É—in ba za ta bar ka, ka zo ka gaishe ni ba."
Ya gane Salma take nufi, don haka ya yi shiru bai ce komai ba. Girgiza kai kawai ta yi ta zauna suka cigaba da gaisawa. Tana son Safwan sosai don duk abin da za ta yi ba ta banbanta shi da su Khalifa. Shi ma kuma haka, duk abin da ya yi wa mahaifiyarsa na kyautatawa to sai ya yi wa Ummi. Wannan dalilin yake ƙara yawaitar tsanar Ummi a cikin ran Mommy, Ta yi iya yinta don ta ga ta raba su amma Ubangiji bai ba ta nasara ba. Dole ta haƙura, amma duk da haka ko part ɗin Ummi ya je idan ta samu labari sai ta yi masa sababi ranar. Hakan ba ya hana shi ya ƙara zuwa ko ya yi mata abin Alkhairi. Sai da aka fara kiran Sallah sannan ya yi wa Ummi sallama ya tafi masallaci. Lokacin da ya fito A'isha ta gama cin abincin ta kwanta. Bai kalli inda take ba ya fice abinsa.

Abba na dawowa Mommy ta tare shi da ƙorafin Khalifa ya mari Salma, da yake ta karɓi girki yau. Da mamaki Abban ya ce. "Mari kuma? A kan me?"
"Wa ya san masa Alhaji? Yaron nan fa dama can ba mutunci gare shi ba." Abba ya ce. "Gaskiya akwai abin da ya faru, haka kawai Khalifa ba zai mari matar yayansa ba, amma bari na kira shi a waya na ji ba'asin zancen." Cikin takaici Mommy ta ce. "Kamar ya sai ka kira shi ka ji ba'asin zance? Akwai ba'asin da ya wuce wanda na faɗa maka? Ko kuma zan maka ƙarya ne?"
"A gabanki aka yi marin ne?"
A shaƙe ta ce. "A'a." Abba ya ce. "To kuma, ko shaidar zur za ki bayar?" A ƙufule ta ce. "Amma ka san shi ma dai ba zai faɗi gaskiya ba ko? Kansa kawai zai kare"
"Idan ma ya yi ƙaryar zan gane." Abba ya faɗa tare da kara wayarsa a kunnensa.

Khalifa yana parlour'n Ummi a lokacin yana tambayar A'isha yaya take jin jikinta a yanzu. A hankali ta ce masa. "Kaina da wuyana ne suke mini ciwo." Taune lips ɗinsa ya yi yana ƙara jin zafin Salma a ransa ya ce. "Sorry, kin sha magani?" Ta ce. "Eh Ummi ta ba ni." Cike da kulawa ya ce. "Ko kina son cin wani abu na siyo miki." Ta girgiza masa kai alamar a'a.
"Ki faÉ—a mini dai, me kike son ci zan siyo miki ko mene ne Nana." Yadda ya yi maganar cikin wani irin yanayi sai ta ji tamkar Umar, ta rasa me ya sa kalamansa da muryarsa suke mata shige da na Umar sometimes. Numfashi ta sauke ta ce. "Babu komai fa, bacci kawai nake son yi." Ya ce. "Mu je na raka ki É—aki ki kwanta to."
"Ummi ta ce na bari a yi Sallar Isha'i sai na yi baccin." Ta ba shi amsa cikin jin daÉ—in yadda yake nuna damuwa a kanta. Fitowar Ummi daga kitchen ya saka shi fasa faÉ—ar abin da ya yi niyya.
"Ka je Abbanka na kiran ka, ya kira ka ba ka É—auka ba."
Da to ya amsa mata tare da miƙewa ya fice ba tare da ya bari sun haɗa ido ba.

Mommy na zaune har lokacin tana cika tana batsewa ya shiga, Abba da suke gaisawa da Safwan ya dube shi tare da amsa sallamar da ya yi.
"Sannu da zuwa Abba." Ya faɗa lokacin da yake zama. Abba ya ce. "Yawwa." Duban Safwan ya yi ya gaishe shi tare da yi masa sannu da zuwa, a maimakon ya sai harara ya wurga masa. Tambayar shi Abba ya yi akan abin da ya faru ya faɗa masa duk abin da idanunsa suka gane masa cikin nutsuwa. Jinjina kai Abba ya yi cikin gamsuwa ya ce. "Me ya sa ka mare ta? Duk da ka girme ta ai Yaya take a gurinka yanzu." Khalifa ya ce. "Wallahi Abba ban je inda suke da niyyar taɓa jikinta ba, na yi na yi ta sake ta ne ta ƙi, ban ma san lokacin da zuciya ta ɗeɓe ni na mare tan ba." Ƙwafa Mommy ta yi tana hararar shi ba ta ce komai ba. Safwan kuwa danne zuciyarsa kawai yake don a gaban Abba ne, amma da sai ya rama wa Salma marinta, kuma idan ya tashi ba ɗaya zai masa ba, sai ya ninka marin sau uku.
"To ka ja masa kunne Abba, kar ya ƙara gigin kai hannunsa jikin matata." Safwan ya faɗa a fusace.
Abba ya ce. "Ita ma ka ja mata kunne akan ta dinga bin komai a sannu, ba wai abu bai kai ya kawo ba ta hau dokin zuciya, don watarana zai kai ta ga da na sani." Cikin jin haushin maganarsa Mommy ta ce. "Alhaji kana nuna masa abin da ya yi fa daidai ne, Salma ce ke da laifi kenan?" Abba ya ce. "Eh." Ganin yadda ya yi maganar fuska a haɗe ya sa ba ta kuma magana ba, amma a ranta ta ƙudurce Khalifa bai mari banza ba, za ta ɗauki mataki da kanta. Duk da Abba ya ce ya kashe maganar kar wanda ya ƙara taso ta.

Salma tana mayar da rigarta Fadeela ta fito daga toilet tana faÉ—in. "Wai da gaske Salma tafiya za ki yi?" Ta ce. "Eh mana."
"Duk missing É—in namu da kika ce kin yi iya baki ne kenan? I thought a nan za ki kwana?"
Tana taje gashin dokin dake kanta ta ce. "Gidan Mama za ni." Rukky dake kwance a kan gado tana sauraren su ta ce. "Sai yaushe kuma? Ko mu zo gidanki gobe?" Tsayawa ta yi da tazar da take cikin waro ido ta ce. "What? Gidana fa kika ce, kar ma ku soma, don Mine yana nan, kuma kun fi kowa sanin bana barin a zo mini gida idan yana nan, saboda bana ƙaunar duk wani abu da zai haɗa shi da wata mace komai ƙanƙantar shi." Dariya Ramcy ta yi ta ce. "Me a kai kenan? Idan kin ɓoye shi a gida a gurin aikinsa fa? Likita ne fa shi, likitan ma na mata, ai babu wanda zai kai shi hulɗa da mata kala-kala ma." Salma ta yi murmushi tare da faɗin. "Wannan na san aikinsa kawai yake ba ya bi ta kansu, ke koma yana bi sai dai ya gani ya ƙyale, don ba aura zai yi ba, saboda babu macen da ta isa na haɗa miji da ita duk duniyar nan. Safwan nawa ne ni kaɗai, don ni kaɗai aka halicce shi." Fadeela ta ce. "Easy bab, ba a kuri a kan namiji."
"Ni na yi na kuma yi, ku zuba ido ku yi kallo, ko mutuwa na yi Safwan ba zai so wata mace ba, balle kuma ina raye." Ta ƙarashe maganar tare da ɗaukar jakarta ta juya ta fice bayan ta ɗaga musu hannu. Da kallo suka bi ta da shi. Haleemah ba ta tanka musu ba tun ɗazu ta ce. "Iska na wahalar da mai kayan kara, wato ita har ta manta baƙar wahalar da ta sha kafin ya yarda ya aure ta?" Rukky ta ce. "Har aka yi auran fa baya son ta, yanzu ma soyayyar duk ta asiri ce." Taɓe baki Fadeela ta yi ta ce. "Zai karye ne watarana, mu ga ƙarshen jijjigi da kai da ɗagawar auren mai kuɗi, kyakkywa da ake mana."

*5 days later*

Yau ta kama ranar komawa asibiti karɓar sakamakon gwajin da aka yi wa A'isha. Sai a cikin kwanakin nan da suka wuce Mommy ta san A'isha makauniya ce, ranar da ta ji labarin ba ƙaramin bala'i ta yi ba, ta ce sai dai Abba ya zaɓa ko ita ko A'ishan. Don ba za ta iya zama da ita a gida ɗaya ba, ga talauci ga rashin asali sannan kuma ga makanta. Da farko Abba bai kula ta ba, sai da ta ishe shi ya ga idan bai tsawatar mata ba, ba za ta bar shi ya yi sukuni ba sannan ya ce mata ya zaɓi A'isha, ta je ta yi duk abin da za ta yi. Ƙaramin hauka ta yi da jin furucin nasa saboda ba ta taɓa zaton zai iya kallon cikin idonta ya faɗa mata haka ba. Ko Ummi bai taɓa cewa ya zaɓa a kanta ba sai wata TSINTACCIYA mara asali? Ranar kasa rintsawa ta yi saboda baƙin ciki. Tsanar A'isha mai tsanani ta ƙara cika mata zuciya.
Chapter 51 · 0% Book details