Sashe 21
Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Bayan Magriba Inna sun fito za su tafi chemist suka haɗu da Umar, yana tsaye a ƙofar gidan Sarki yana latsa wayarsa. K'ansa a ƙasa ya gaishe da Inna, ta amsa cikin fara'a. Yana kallon A'isha ta ƙasan ido ya ce. "Unguwa za ku ne Mama?" Inna ta ce. "A'a, nan chemist zan kai A'isha ba ta jin daɗi ne." Cikin tausayawa ya ce. "Subhanallahi, amma dai jikin nata da sauƙi ko?" Inna ta ce. "Alhamdulillah." Ya ce. "Allah ya ƙara sauƙi, sai kun dawo......Sannu A'isha, Allah ya ƙara sauƙi." A ƙasan mak'oshi ta amsa masa, shi ko ji ma sosai bai yi ba. Har sun yi gaba zuciyarsa ta ba shi umarnin ya bi su ba tare da shi kansa ya san dalili ba. Bayan sun je mai chemist ɗin ya duba A'isha ya ce allura zai yi mata ta kwana uku 600. Shiru Inna ta yi tana tunanin gaba-d'aya kuɗin hannunta bai fi 800 ba, amma ya za ta yi? haka ta ce a yi mata. Jin haka A'isha ta fara hawaye tare da lafewa a jikin Inna, dan ba ta k'aunar allura ko kaɗan a rayuwarta. Umar ne ya yi sallama a cikin chemist ɗin, su Inna suka amsa masa, da mamaki Inna take duban sa amma ba ta ce komai ba. Bayan Mai chemist ɗin ya gama haɗa allurar ya dubi A'isha ya ce. "Bismillah ku shigo a yi mata." Kuka A'isha ta fashe da shi ta ce. "Ni dai Inna dan Allah kar a mun allura." Inna ba ta kula ta ba ta ja ta suka shiga, daƙyar ta bari aka yi mata allurar, sai gunjin kuka take yi. Inna za ta biya kuɗin ta tsinkayi muryar Umar yana tambayar mai chemist ɗin nawa ne kuɗin, ta juyo ta dube shi ta ce. "Haba Ɗana, ka bar shi ma zan biya ai." Murmurshi ya yi bai ce komai ba ya zaro kuɗi a aljihunsa ya bayar bayan mai chemist ya faɗa masa adadin kuɗin, ko kaɗan Inna ba ta so haka ba, ba ta so ta saka shi wahala ba, godiya ta yi masa sosai sannan ta fita za ta siyo abu ta cewa A'isha ta jira ta anan ta je ta dawo. Bayan fitar Inna ya zauna a kusa da A'isha akan benci ya ce. "Kukan ya isa haka me tsoron allura." Turo baki A'isha ta yi ba ta ce komai ba ta shiga share hawaye." Murmurshi ya yi ya ce. "Ya jikin naki?" A hankali ta ce. "Da sauƙi." Ya ce. "Allah ya ƙara sauƙi, da fatan kina cin abinci dai ko?" Girgiza masa kai A'isha ta yi ta ce. "Bakina ɗaci, bana son cin komai." Ya ce. "Ba kya so ki warke kenan a daina yi miki alllura?" Ta ce. "Ina so." Ya ce. "To ki dinga cin abinci kin ji Indo?" Ta ce. "Toh." Tare da ɗan ɓata fuska na Indon da ya kira ta da shi. Dai_dai nan Inna ta dawo ta yi masa sallama suka wuce gida. Suna shiga gida suka tarar da Matan gidan da yaran gidan tsaitsaye a bakin ɓangarensu. Da mamaki Inna ta tsaya tana kallon su, Iya ta tako ta tsaya a gabanta tana mitsi_mitsi da ido ta ce. "Yanzu Asabe rayuwar da kika ɗaukarwa kanki kenan ta bin maza ke da ƴarki?" Inna ta yi shiru kawai tana kallon ta cikin mamaki. Iya ta ce. "Kya yi shiru ki tsare ni da ido mana, to wallahi ki saurara ki ji ba zai yiwu ba, baki isa ba, ba'a gidan nan ba, baza ki dinga kawo mana maza kuna iskanci har cikin gida ba." Ramatu ta karɓe zancen da faɗin. "Jiya fa ana cikin tsakiyar zuga ruwan nan amma na gan su a soro cikin duhu ita da shi da ƴar, abun kunyar ma yaro ne qarami ɗan cikinta, ɗazu kuma har cikin gida ta shigo da shi." Wata ƴar budurwa mai siffar fitsararru ta amshe zancen da faɗin. "Iya yanzu ma fa tare na gan su da shi, kuma ba ku gan shi ba kyakkyawa ɗan birni, duk yanda aka yi wani abun nasu na Mayu ta yi masa ta asirce zuciyarsa, ban da haka ya zai yi ya kula su." Jan hannun A'isha Inna ta yi suka shige ciki zuciyarta na mata k'una, abun mutanen gidan nan ya daina ba ta mamaki sai dai tsoro, wani lokacin kuma uzuri take musu, kamar dai yau da haukansu ya ba su su yi mata k'azafi. Suna shiga ɗaki A'isha da ta haɗe rai sosai ta ce. "Su ƴan gidan nan kullum masifa_masifa, su ta yi mana masifa, Inna dan Allah mu bar musu gidan mu tafi gurin ƴan'uwanmu da kika ce muna da su, Allah na gaji da zaman gidan nan." Kama hannun A'isha Inna ta yi ta ce. "Na fi ki son mu bar gidan nan A'isha, ƙaddara ce ta saka har yanzu muke zaune a cikinsa, babu yadda zamu yi ne. Na sha ki faɗa miki ki kasance mai hak'uri akodayaushe a duk halin da kika tsinci kanki a rayuwa, duk wannan abubuwan da suke faruwa watarana za su wuce su zamo labari, komai lokaci ne a rayuwa." Cikin sanyin jiki A'isha ta gyaɗa mata kai. Suna nan zaune sai ga yaro ya shigo da leda wai a bawa A'isha in ji wani. Inna ta ce gaskiya ba su ake nufi ba sai dai in yaron ɓatan kai ya yi, amma yaron ya ce su aka ce masa, kwatantawa Inna Umar ya yi, lokaci ɗaya Inna ta gane shine, godiya ta ce yaron ya yi masa sannan ta karb'i ledar cikin mamakin wannan hidimar da yake yi musu. Dafaffiyar indomie ce da k'wai sai yoghurt mai sanyi na jarka. Tunda A'isha ta shak'i ƙamshin abincin yawonta ya tsinke, ai kuwa zagewa ta yi ta ci abincinta ta kora da yoghurt ɗinta, ta ma manta da wani ɗacin baki. Washegari Sarki ya aiko aka kira masa Inna ya ba ta hak'uri akan abun da su Ɗan_juma suka yi, sannan ya tabbatar mata da hakan ba za ta kuma faruwa ba Insha Allahu, dan yanzu haka ma su Ɗan_juman an kulle su an saka musu mari, kuma ana ba su horo mai tsanani. A haka rayuwa ta cigaba da tafiya, kullum Umar sai ya haɗu da su Inna idan A'isha zata je makaranta ko kuma idan ta dawo, suna gaisawa sosai da Inna amma A'isha ba ta yi masa magana, shi ma kuma sai dai ya kalle ta kawai. Inna har ta gaji da yi mata faɗan ƙin gaishen shi da take yi.