Sashe 46
Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Har Ummi ta dawo Gwaggo ba ta daina mitar halin Mommy ba, bayan ta zauna ta dubi Gwaggo cikin mamaki tana ajiye jakarta ta ce. "Lafiya Gwaggo? Ke da wa?"
"NI da Saratu mana, wa zai taɓa ni a gidan nan ban da ita da ba ta girma."
Ummi ta sauke numfashi ba ta ce komai ba. Gwaggo ta ce. "Wai zuwa ta yi tana faɗa mini na cewa Alhaji Sa'id ya mayar da mai sunan Adda ƙauyen da take, wai kar a je watarana mun yi mata rana ta yi mana dare. Ko a kanta yarintar take oho?" Ya Maamah da ta shigo ɗakin ta tsinci zancen ta ce. "Mommy ko?" Gwaggo ta ce. "Ita fa." Girgiza kai Ya Maamah ta yi tana zama a kusa da Gwaggo ta ce. "Ban san me ya sa ba ta son wani ya raɓi gidan nan da sunan cin arziƙi ba, ita dai kullum kar talaka ya raɓe ta ya goga mata tsiya, zancen ta kenan." Tsaki Gwaggo ta yi ta ce. "Tsiya ta wuce tata? Ita ba ta duba abin faɗar da suke da shi sai na wani, tunda ubansu ya gudu ya bar su suna ƙanana wa ya ƙara jin labarin inda yake? Ya tafi ya bar uwarsu da wahala sai abincin siyarwa ta kama a bakin tasha don ta rufa musu asiri, su ma suka tashi a haka yan tuwo-tuwo, har daf da Sa'id zai aure ta ba daina fita tasha siyar da abinci ba. Amma yanzu saboda ɗanta ya yi arziƙi duk ta bi ta ishi mutane da jaraba." Ummi ta ce. "Ki yi haƙuri Gwaggo, ki bar maganar nan, kuma don Allah kar sanarwa da Abbansu ta zo miki da wannan batun, kin san shi da saurin hawa, yanzu sai ya je su yi ta rigima." Gwaggo ta ce. "Ni ban san irinki ba Zara'u, matar nan ba ta ƙaunar ki amma ke kodayaushe ba kya son ki ga ta ɓaci a idon mijinku." Ummi ta ce. "Ita ma Allah ya ganar da ita, ta gane abin da take yi ba daidai ba ne." Ya Maamah ta ce. "Hmm." Kawai.
Kaltum ba ta samu zuwa ba, ta taho a hanya ta samu accident, sai asibiti ta wuce. Hankali a tashe Mommy ta tafi asibitin da suke bayan ta kira ta sanar mata. Ta je ta tarar ba ta yi wani rauni sosai ba, a ranar aka yi mata treatment aka sallame ta.
Da daddare bayan Abba ya gama buÉ—a baki ya saka Ummi ta kawo masa A'isha part É—insa, bayan ta gaishe shi ya amsa cikin kulawa sannan ya gyara zama ya ce. "Mamana a ina kika tsaya da karatu ne?" A hankali ta ce. "J.s. 3." GyaÉ—a kai ya yi ya ce. "A haka ba kya ganin kike zuwa makarantar ko?"
"Eh." Ta ba shi amsa cikin ladabi.
"Masha Allahu, idan Allah ya kai mu bayan bakwan mahaifiyarki za mu je asibiti a duba idon naki, idan Ubangiji ya ba mu sa'a kin warke sai ki cigaba da karatunki." Duk son ta da karatu da son ta warke daga makanta sai ta ji ba ta yi wani farinciki ba da kalaman Abba, saboda ɗaci da zafin da zuciyarta take ciki na rashin Inna, wanda kullum kewar ta da zafin mutuwar ta yake ƙaruwa a cikin ranta. Tana ƙoƙarin mayar da ƙwallar da ta cika mata ido ta ce. "Na gode sosai Abba, Allah ya ƙara girma ya ji ƙan mahaifa." Cikin jin daɗin Addu'ar ta ya ce. "Amin ya ALLAH, Allah ya miki albarka ya inganta rayuwarki. Zan saka a samo malamar Addini ta dinga yi miki ƙarin Ƙur'ani da littafai, saboda Ummin taku ba ta zama tana fita aiki, da sai ta dinga miki." Godiya ta ƙara yi masa cikin raunin murya, don sosai Alkhairin Abba ya karyar mata da zuciya, taso a ce Inna tana raye su ga wannan ranar tare, ranar da wani zai nuna musu ƙauna duk ya kasance mai arziƙi da wadata. Abba ya ce. "Babu komai, ke ma 'yata ce kamar su Khalifa, ki saki jikinki ki yi rayuwa kamar kowa a gidan nan kin ji?" Gyaɗa masa kai ta yi tare da yin ƙasa da kanta. Ganin har yanzu ba ta saki da jiki da zaman gidan ba Abba ya shiga yi mata nasiha, ya san mutuwar Inna har yanzu tana dukan ta. Shi ya sa yake son ta shiga school ko hakan zai rage mata damuwa.
Bayan kwana uku aka yi sadakar bakwai ɗin Inna kamar yadda aka yi ta uku, har lokacin A'isha ba ta daina kukan mutuwar Inna ba, kulawa da ƙaunar da Ummi da Abba ke nuna mata ke rage mata damuwa, gami da ƙara saka mata nutsuwa akan zaman ta a gidan. Lokuta da dama za ta kwanta da sunan bacci, amma baccin za ta yi ba, tunanin Inna da yadda suka gudanar da rayuwarsu take cikin hawaye, hakan ya saka kullum take fama da matsanancin ciwon kai. Duk da ta samu hutu da cima mai kyau amma kullum ƙara rama take. Kwanaki bakwan nan da suka wuce jin ta take tamkar mai rayuwa cikin mafarki, ko ƙaƙa ta yi bacci ta farka sai ta ji tamkar za ta ji muryar Inna tana mata magana, ko za ta tashi su cigaba da rayuwa a gidansu. Sai dai ta tabbatar hakan ba zai taɓa faruwa ba, Inna ta riga ta tafi ba za ta dawo ba. Ta san mutuwa gaskiya ce, duk wani mai rai jiran ta yake. Da yamma tana zaune ita kaɗai a parlour tana tunanin da ta saba, Ummi na toilet tana wanka, Ya Maamah ta koma Abuja gidan mijinta, Gwaggo ma ta koma Gombe kwana biyu da suka wuce. Kasa daurewa ta yi duk da ba ta son Ummi ta gan ta tana kuka ta fashe da kuka mai tsuma zuciya. Cikin kukan take faɗin. "Allah ya ji ƙan ki Innata ya gafarta miki, rashin ki a cikin rayuwata daidai yake da na rasa farinciki na har abada. Ban taɓa tunanin ko da wasa akwai ranar da zan yi rayuwa babu ke ba." Ta ja majina tare da yin sheshshek'a ta ce. "Allah ya kai haske kabarinki." A haka Ummi ta zo ta tarar da ita tana gunjin kuka. Hankali a tashe Ummi ta ƙarasa kusa da ita ta zauna tana tambayar ta dalili kukanta, a tunaninta wani ne ya shigo ya yi mata wani abun.
"Me ya faru? Ko wani ya shigo ya miki wani abun? Shi ya sa bana son kina zama ke kaɗai a guri." Girgiza kai ta yi cikin ƙoƙarin tsayar da kukan. Ajiyar zuciya Ummi ta sauke ta ce. "To me ya faru?"
"Babu komai." Ta ba ta amsa tana goge hawayen fuskarta.
"Ko garinku kike son zuwa?"
Nan ma girgiza mata kai ta yi. Dafa kafaɗarta Ummi ta yi ta ce. "To ki yi haƙuri ki bar kukan nan haka kar ki jawo wa kanki wani ciwon, na san rashin mahaifiyarki ne yake damun ki, amma ba kuka ya kamata ki zauna kina yi ba idan kika tuno ta, addu'a za ki yi mata, Allah ya ji ƙan ta." Numfashi ta sauke tare da gyaɗa mata kai. Cikin tausayawa Ummi ta ce. "Mutuwar Uwa akwai ciwo da dukan rai, amma sai haƙuri babu yadda za mu yi. Idan zafin abun ya taso miki ki dinga kiran sunan Allah ko kina karatun Alkur'ani, za ki ji sauƙin abun insha Allahu." Cikin raunin murya ta ce. "Zan na yi insha Allah, na gode." Ummi ta ce. "Mu je ɗaki ki kwanta ki huta kafin a kira Sallah, na san kanki ba zai kasa yi miki ciwo ba."
Washegari kafin bakwai na safe sun gama shirin tafiya Asibiti. Abba ya shiga part ɗin Mommy don yi mata sallama, ya tarar da ita a kwance tana bacci. Tashin ta ya yi ta buɗe ido da ƙyar.
"Zan fita." Abba ya faɗa a taƙaice, don har yanzu bai gama hucewa daga abin da take yi ba. Miƙa ta yi gami da hamma ta tashi zaune. Cikin muryar bacci ta ce. "Ina kuma za ka je da sassafen nan na gan ka cikin shiri?"
"Za mu kai Nana asibiti ne?"
Cikin rashin fahimta ta ce. "Wace ce kuma Nana da za ta fitar da kai da sassafen nan? Ko Baby ce babu lafiya ai sai haka." Abba ya ce. "Yarinyar da na kaɗe su nake nufi, kin san tana da matsalar ido." Taɓe baki ta yi ta ce. "Ina zan sani tunda ba a wurina take ba? Sai kun dawo to."
"Yanzu ai kin sani." Ya faɗa tare da juyawa zai fice. Tsaki ta ja a ranta tana mitar akan wannan shirmen zai katse mata daddaɗan baccin da take ya ƙara mata ɓacin rai. Ya ji tsakin da ta yi, amma bai ce komai ba ya fice.