← Book details Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 55

Sashe 6

Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

..........Baki buɗe Inna ta shiga bin Hajiya Kareema da wani irin kallo mai kama da na baki da hankali, kafin ta daure zuciyarta ta ce. "Ban gane ba Hajiya? Ƴar tawa guda ɗaya tal zan baki ki tafi ita da Saudiyya? Ban san ki ba ban taɓa ganin ki ba, ban kuma san daga inda kike ba." Hajiya Kareema ta yi murmushi ta ce. "Ai ba haka sakaka zaki bani ita na tafi da ita ba, komai a rubuce za'a yi shi da shaidu da saka hannun hukuma, kuma ƴaƴana suna cikin garin nan da zama zan kai ki har inda suke ki gani, balle ki ce zan gudar miki da ƴa ne." Inna ta ɓata fuska ta ce. "To ita A'isha ƴar ƙanƙanuwa da ita neman kuɗin me zata iya yi?" Hajiya Kareema ta ce. "Sana'a mana, ga sana'o'i nan kala_kala a ƙasar Saudiyya na samun kuɗi." Murmurshin takaici Inna ta yi ta ce. "Amma a sana'ar ne na ji kin yi maganar ko dan kyan A'isha za'a amfana da ita, wacce irin sana'a ce da take da haɗi da kyau ko wani yanayin halittar jikin Mutum?" Hajiya Kareema ta ɗan taɓe baki ta ce. "Aa, ai a komai na duniya an fi son abu mai kyau Ko? Ko abu take saidawa sai a siyi nata ai kafin a siyi na munana, ni haka nake nufi ba wani abun ba." Murmurshin takaici Inna ta ƙara yi ta ce. "Haba Hajiya, ba fa Yarinyar goye ba ce ni ko kuma wadda aka haifa yau da ban san takan duniya ba, karki ganni haka a ƙauye ki yi tunanin ban san me nake yi ba, na san sarai me kuke yi a Saudiyyan idan kun je." Hajiya Kareema ta ɓata fuska ta ce. "A'a Tsohuwa karki yi mun wata fassarar daban, samuwa ce fa kawai na zo miki da ita." Inna ta haɗe rai sosai ta ce. "To na gode, amma ba zan iya ba, ƴar tawa guda ɗaya tal a duniya zan tura ta yawon aikatau wata ƙasar? To bazan iya ba gaskiya." Hajiya Kareema tana yi mata wani shegen kallo ta ce. "Taimakon ki na zo yi fa ba wani abu ba, in kuma fitar dake daga wannan k'angin talaucin da kike ciki." Inna ta ce. "Allah ne zai fitar da ni, kuma Ni ban ce ina neman taimakon kowa ba bayan na Ubangiji na." Hajiya Kareema ta miƙe ta saɓi Jakarta ta ce. "Ai dama an ce kare bai gaji arzik'i ba, sai da aka mun bayanin halinki amma na dage sai na zo, ni uwar son gwaninta." Inna ba ta kuma yi mata magana ba. Ta zira takalminta sannan ta ɗauko wani ɗan kati daga cikin Jakarta ta ajiye a gaban Inna ta ce. "Gashi nan, idan kin yi shawara daga baya in kin ga kina da interest akan abun da na zo miki da shi sai ki neme ni, ga Numbern wayana nan a jikin katin, kya kira ni." Daga haka ta juya ta fice daga zagayen. Bin ta da kallo kawai Inna ta yi, ita abun ma mamaki ya bata ba kaɗan ba, ta dinga tambayar kanta me yasa duk mutuncin da suke yi da Ramatun bata kai ƴaƴanta ba sai ta_ta ƴar? Ko da yake bata sani ba ko har da su zata tafi. Miƙewa ta yi ba tare da ta bi ta kan katin da matar ta ajiye ba ta shiga ɗaki, gurin A'isha ta je ta taɓa goshinta dan jin yanayin jikin nata, har lokacin A'isha baccinta take sha. A fili Inna ta ce. "Ƴar wannan Yarinyar da ba ta fi shekara goma sha biyu ba ita ake tunanin akai Saudiyya aikatau?" Ta ja ɗan ƙaramin tsaki a ranta tana jinjina wannan haukan, dan ita rashin hankali kawai ta ɗauki batun.

Wunin yau gaba-d'aya A'isha a kwance ta yi shi cikin ciwo, gashi ta ƙi cin komai, Innar Ma'u har ɗan wake ta yi mata ta kawo sanin da ta yi tana k'aunar ɗan_waken amma ta kasa ci. Inna ta siyo mata paracetamol da Panadol, su dai an samu ta sha daƙyar bayan Inna ta yi yaƙi da ita. Hankalin Inna fa ya tashi ganin yanayin jikin A'isha, gashi bata da kuɗi balle ta kai ta chemist a yi mata allura. Wasa_wasa sai da A'isha ta yi kwana Uku a kwance amma jikin sai godiyar Allah kawai, dan Jiya I yau yake. Mutanen gida sai lok'owa suke suna yadawa Inna Habaici, wai sun kama ƴar wani ne abun ya dawo kansu, Inna dai ba ta tanka musu, ko kallon inda suke ma bata yi.

Yau Lahadi, da Hantsi Inna suna zaune a tsakar gida ta shimfid'e A'isha akan tabarma tana goga mata ruwa da tsumma a jikinta saboda yanda jikin nata ya yi zafi sosai. Innar Ma'u ce ta shigo zagayen nasu bakinta ɗauke da sallama. Inna ta amsa mata tare da faɗin. "Maraba lale, sannunki da zuwa." Innar Ma'u ta amsa da "Yawwa." Tare da zama a gefen tabarmar da Ma'u take kai. Cikin alhini tana kallon yadda A'isha ta rame da ce. "Sannu A'isha, ya jikin naki?" Inna ta ce. "Da sauƙi Alhamdulillah, amma jiya ba mu yi bacci ba tana ta complain ɗin kanta na yi mata ciwo sosai." Innar Ma'u ta ce. "Allah ya ƙara sauƙi, amma da kin kai ta chemist ɗin Isma'il anjima ya duba ta, wataƙila zazzaɓin cizon sauro ne fa ya kamata." Inna ta ce. "Bana jin shine Ladidi, kin ga ai garin nan ba mu da sauro." Innar Ma'u ta ce. "Haka ne, amma duk da haka ki kai ta ya duba ta." Inna ta ce. "Da cewa na yi gobe zan yi asubanci in je in tsinko mata gayye in yi mata sirace ko Allah zai saka a dace." Innar Ma'u ta ce. "To ki gwada yi mata, Allah ya bada lafiya." Inna ta ce. "Amin ya Allah." Washegari kuwa Inna kamar yadda ta faɗa ta ce ta karb'o gayyayyaki ta zo ta yiwa A'isha surace. Ba wai son kai ta chemist a duba ta ne ba ta son yi ba, kuɗin da zata biya ne ba ta da shi. Dan tunda A'isha ta fara ciwo a wurin Innar Ma'u take rantar ɗan kuɗin da suke kashewa, da yake ita Innar Ma'u tana siyar da kayayyaki, kuma ƙaninta dake zaune a cikin Kano yana da hali, yana yawan yi mata aiken kuɗi akai_akai. Duk da Inna ta yiwa A'isha surace amma jikin dai jiya i yau still. Dole Inna ta ranci 500 ba don ta so ba takai A'ishan chemist aka yi mata allura ta kwana biyu, da wannan ta samu jikin nata ya fara yin ɗan dama_dama har take iya magana, saɓanin daa da sai dai kallo da ido.

Ranar Juma'a wanda ya kama kwanan A'isha goma a kwance. Da yamma daf da Magriba Ma'u ta shigo zagayen nasu, bayan sun gaisa da Inna ta shiga ɗaki gurin A'isha. "Sannu Indo." Ta faɗi haka tana zama a kusa da A'ishan, gyaɗa mata kai kawai A'isha ta yi, dan wani irin azababben ciwo kanta yake mata. Ma'u ta ce. "Yanzu muka haɗu da mutuminki Ɗan_juma ya ce mun kina ina? Kwana biyu ba ya ganin ki." Duk da halin ciwo da A'isha take ciki sai da ta yi tsaki. Ma'u ta yi murmushi ta ce. "Na ce masa baki da lafiya ne, ya ce in miki sannu, bai sani ba ai da ya zo ya duba ki." A'isha tana numfarfashi cikin muryar marasa lafiya ta ce. "Dan Allah Ma'u ki daina yi mun zancen wani Ɗan_juma, wallahi ƙara mun ciwo kike." Ma'u ta ce. "To na daina, Allah ya baki lafiya." Bayan Ma'u ta tafi ciwon kan A'isha ya tsananta, tana kwance ita kaɗai a ɗaki sai jujjuya kan take yi. Inna ta yi alwalar Magriba ta shigo ɗakin yin Sallah ta tarar da A'isha a wannan halin. Da sauri ta ƙarasa inda take tana faɗin. "Subhanallahi, Lafiya A'isha? Ko jikin ne?" Muryar A'isha ko fita ba ta yi sosai ta ce. "Inna, kaina zai tsage gida biyu, Inna ki kaini asibiti a cire mun shi dan Allah?" Cikin ɗimuwa Inna ta ce. "Subhanallahi, kai kuma A'isha? Ko yunwa ce tunda ba kya iya cin abinci? Bari na yi Sallah mu san abun yi." A daddafe Inna ta yi Sallar, tana idarwa ta fice zuwa zagayen Innar Ma'u don aron kuɗi, duk da kuɗin da take bin ta ya kai 2500 amma haka zata ƙara karɓar wani, dan yanda A'isha take juyi tare da riƙe kanta ya ɗaga mata hankali ba kaɗan ba, gwara kawai ta kai ta asibiti a duba mata ita sosai. Ciwo ya ƙi ci ya ƙi ƙarewa daga wannan sai wannan, har tana murna da aka yi mata alluran nan jikin ya fara kyau, ashe da sauran rina a kaba.
Chapter 6 · 0% Book details