Sashe 40
Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haɗaɗɗen Bedroom ne wanda ya tara komai na da ake buƙata ga kowane bedroom. Duk da girmansa bai hana munsharin lukutar matar dake bacci a kan luntsumemen gadon dake cikinsa cika shi ba. Da ƙarfi wata farar budurwa dake sanye da ƙananun kaya ta turo ƙofar ɗakin ta shigo ba tare da sallama ko neman izni ba.
"Mumy! Mumy!"
Shi ne abin take furtawa cikin yanayin razana, ganin ba ta ko motsa ba ta hau kan gadon tare da jijjiga ta tana cigaba da kiran sunanta. Hakan ya sa matar motsawa tare da Buɗe idonta a firgice. A tsawa ce ta ce. "Baby ba ki da hankali ne kike mini irin wannan tashin?" Shagwaɓe fuska ta yi ta ce. "Abu fa na zo na faɗa miki."
"Mene ne?" Ta faÉ—a cikin hamma.
"Abba ne na ga sun shigo da mutum shi da Ya Khalifa a lulluɓe, alamun dai gawa ce, kuma kamar accident aka yi sai zubar da jini tak..."
"What?" Ta faɗa cikin ƙaraji tare da tashi zaune.
"Ina kika ga sun yi?"
"Part É—in Abba suka shiga."
A ruɗe ta hantsilo daga kan gadon bayan ta damƙi ɗankwalinta ta fice daga ɗakin cikin sauri tamkar magen da ta hangi ɓera.
Yadda ta shiga parlour'n Abba a hargitse ya sa su ɗaga kai dukan su a tare suka kalle ta. Idanunta a kan Abba ta ce. "Alhaji! Waye ya rasu? Gawar waye wannan?" A sanyaye Abba ya ce. "Accident muka samu na kaɗe wasu mata za su tsallaka titi, a ciki ɗaya ta rasu." Ajiyar zuciya ta sauke tare da yatsina fuska ta ce. "Amma saboda Allah maimakon ka nemi ƴan'uwansu ku kai gawar can gurinsu shi ne za ka kawo ta gidan nan? Nan ɗin ma ba ɗakin mai gadi ko guest room ko BQ ba sai cikin part ɗinka a falonka? Saboda kawai ka faɗar mini da gaba ka sa hankalina ya tashi, tunda ka fi kowa sanin ɗana yana wata ƙasar kuma ya ce a cikin satin nan zai dawo, ai sai na yi tunanin ko shi ne ya taho suka yi accident a hanya. Gaskiya ba ka kyauta mini ba." Baki suka saki suna kallon ta cikin tsananin mamakin maganganunta. A tausasashe Abba ya ce. "Saratu gawa ce fa a gabanki amma kike wannan maganar mara kan gado, duk mai guntun imani a zuciyarsa idan ya ga gawa sai ya risina ko yaya ne."
"Gawar ta Uba na ce?" Ta faÉ—a kanta tsaye.
"Amma ai ta É—an'uwanki musulmi ce ko?" Abba ya faÉ—a cikin É“acin ran da yake Æ™oÆ™arin dannewa. Æata fuska ta yi sosai ta ce. "Ka tofar da yawon bakinka don ni talaka ba É—an'uwana ba ne, kar Æ™ara dangata ni da su."
"Ce miki aka yi talakawa ne? Idan ma su ne su ba mutane ba ne?"
"Sai an faɗa mini zan sani, tunda ka ce za su tsallaka titi da ƙafafunsu ai talakawa ne, tunda ba su da arziƙin hawa mota." Abba bai kuma magana ba saboda tsantsar ɓacin rai da takaicin halin matar tasa. Khalifa dake sauraren su ya miƙe ba tare da ya yi magana ba ya fice daga parlour'n, da wata muguwar harara ta raka shi sannan ta juya ita ma ta fice. Ƙwafa Abba ya yi cikin tsananin takaicin mugun halin Saratu.
Ummi tana Sallar Azhar A'isha ta farka. Da farko tunaninta guduwa ya yi ta kasa tuna komai da abin da ya faru da su, sai bayan wasu mintuna komai ya dinga dawo mata tiryan-tiryan cikin Æ™wanyarta, kamar wadda aka tsikara da allura ta tashi zaune ta fara laluben gefenta, jin hannun hagunta kamar wanda aka É—aure mata shi da wani abun ya sa ta fara kiran sunan Inna a tsorace....âœï¸
*💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖
_*Zeey Kumurya*_
*ELEGANT ONLINE WRITER'S*
*2ï¸âƒ£3ï¸âƒ£*
Da sausauri Ummi da ta yi sallama ta miƙe ta ƙarasa bakin gadon, cikin tausayawa ta ce. "Kin tashi? Sannu, bari na kira Doctor." Shiru A'isha ta yi gabanta na faɗuwa jin muryar wata ba ta Innarta ba." Cikin kuka ta ce. "Ina ne nan nake? Ina Innata?" Hannunta Ummi ta kama cikin rarrashi ta ce. "Ki kwantar da hankalin ki, asibiti ne nan, kun yi accident ne Mota ta buge ku." Ajiyar zuciya ta sauke ta ce. "Ina Inna?" Yadda ta yi maganar cikin nuna damuwa da zumuɗin son ganin Innar sai ya karyar da zuciyar Ummi, a raunane ta ce. "Tana bacci, an mata allurar bacci ne."
"Ki kai ni na gan ta."
"Ki bari na kira Doctor ya duba ki ya tabbatar babu sauran matsala sai mu je, kin ji?" Gyaɗa mata kai ta yi ba don zuciyarta ta so ba. Mayar da ita Ummi ta yi ta kwantar sannan ta fita. A hankali ta lumshe idonta tana jin yadda ƙamshin asibitin ke hautsina mata ciki, ga sarawa da kanta ke mata. Gurin da aka saka mata drip ta dinga tattaɓatawa har ta gane ƙarin ruwa ne. Ba jimawa Ummi suka dawo tare da doctor ya dudduba jikin nata tare da yi mata tambayoyi. Bayan ya fita ta juyar da kanta inda ta ji maganar Ummi, ta ce. "Zan yi fitsari." Ummi ta ce. "Ki yi haƙuri ruwan da aka saka miki ya ƙare a cire sai ki yi." Ba ta ce komai ba ta koma ta kwanta, zuciyarta cike da son ganin Inna da sanin halin da take ciki. After ten minutes aka cire mata ruwan Ummi ta raka ta toilet.
"Ga tap nan sai ki kunna ki tari ruwan tsarki." Ummi ta faɗa tana ƙoƙarin fita.
"Ai bana gani." A'isha ta faÉ—a cikin sanyin murya. Cak Ummi ta tsaya cikin faÉ—uwar gaba, da mamaki ta ce. "Kamar ya ba kya yi?"
"Makauniya ce ni."
"Subhanallahi!" Ummi ta faɗa cikin tausayawa da mamaki tare da kama hannunta, kallon idon A'isha take tana ƙara girmama ƙudura irin ta Ubangiji, saboda babu yadda za a yi ka ga fararen daradaran idanuwa kamar su ka ce ba a gani da su, ko suna tattare da wani ciwon. Jiki a sanyaye ta tara mata ruwa ta ba ta tare da tsayar da ita a inda za ta yi fitsarin, fita ta yi ta ce in ta gama ta sanar mata tana bakin ƙofa tana jiran ta.
Sosai Ummi ta kaÉ—u da jin Aisha makauniya ce, don farko ta É—auka ma dalilin accident É—in ne, kallon ta take cike da tausayawa, ta kasa É—auke idonta daga kanta, gefe guda kuma a cikin zuciyarta cike take da zullumin yadda za ta ji idan ta samu labarin rasuwar Inna. Numfashi ta sauke ta ce. "Ya sunanki?" A'isha da zuciyarta ke ta bugawa ta ce. "A'isha."
"Ayya, ashe ma Mamana ce ke, Yaya kuke da Innar taki?"
"Babata ce." GyaÉ—a kai Ummi ta yi, za ta kuma magana wayarta ta fara ringing. ÆŠauka ta yi ta duba, ganin Abba ne ya sa ta É—agawa. Magana suka yi ta sakanni ya katse kiran. After 5 minutes wata nurse ta shigo ta ba su takardar sallama da magunguna. Ajiyar zuciya A'isha ta sauke ta ce. "Gurin Innar za mu je ko?"
"Eh, tana can gidanmu an kai ta, yanzu za mu je ki gan ta." Ummi ta ba ta amsa cikin dakiya. Shiru ta yi cikin mamakin kai Innar gidansu ita kuma tana asibiti.
Abba yana bakin Motarsa a tsaye suka ƙarasa, baya Ummi ta buɗe ta shigar da A'isha ta mayar ta rufe. A nan take sanar masa A'isha makauniya ce, wadda ta rasu kuma mahaifiyarta ce. Ba ƙaramin shock ya shiga da jin hakan ba, wani irin tausayin A'isha da ƙaunar ta ya ji ya cika masa zuciya, har suka ƙarasa gida babu wanda ya yi magana a cikin Motar. Ummi na riƙe da hannunta suka shiga har part ɗin Abba inda gawar Inna take. Zaunar da ita ta yi a kan kujera sannan ta zauna ta kamo hannunta ta ce. "A'isha ke musulma ce ko?" Cikin mamakin tambayar ta ce. "Eh."
"Good" Ummi ta faɗa tare da duban Abba dake tsaye yana kallon su. Numfashi ya sauke bai ce komai ba. A'isha da ita dai burinta ta ji muryar Innarta ko ta ji ta a kusa da ita ta ce. "Su waye ku? Ina innar tawa?" Abba ya ce. "Ni ne na buge ku da Mota, Innarki kuma yanzu za ki ji Inda take." Abba ya ƙarashe maganar tare da zama a kujerar dake fuskantar wadda suke. So yake ya faɗa mata Inna ta rasu amma ya rasa ta inda zai fara, don sosai A'isha take ba shi tausayi. Ƙarfin hali ya yi ya fara da yi mata nasiha akan yarda da ƙaddara mai ratsa jiki, hakan ya sanyaya wa A'isha jiki sosai, ta nutsu tana sauraren shi. Ganin nasihar ta shiga jikinta yadda yake so sai ya miƙe ya kama hannunta da kansa ya kai ta gaban gawar Inna ya zaunar. A raunane cikin sigar rarrashi ya ce. "Na san kin san dukkan mai rai mamaci ne, duk wanda yake rayuwa a doron duniya akwai ranar da dole sai ya koma ga mahaliccinsa. Ina mai ba ki haƙurin sanar miki cewar a hatsarin da muka yi Ubangiji ya karɓi ran Mahaifiyarki." Wani abu A'isha ta ji ya daki zuciyarta, tamkar an saka adda an datsa ta gida biyu, numfashinta ya ɗauke na wucen gadi, ta daina fahimtar komai, lokaci ɗaya kanta ya yi wani irin juya mata, daga zaunen da take ta yi baya luuu za ta faɗi. Da sauri Ummi ta yi kanta ta riƙe ta tana ambatar "innalillahi... Abbansu dauko ruwan sanyi a shafa mata, kamar fa ta suma."
"Subhanallahi." Abba ya faɗa tare da miƙewa ya ɗauko ruwan a fridge ya miƙa wa Ummi. Da rawar jiki ta karɓa ta shafa mata a fuska. Gwauron numfashi ta sauke tare da zabura tana faɗin. "Inna! Inna! Kina ina? Wani mummunan mafarki na yi yanzu, wai mun je Kano an kaɗe mu kin mutu, na san ba gaskiya ba ne, ba za ki mutu ki bar ni ba, don Allah Inna ki yi magana na ji muryarki."