Sashe 4
Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaciðŸ™ðŸ»_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
.........Bayan Sun ɗan yi nesa da gidan Mai_gari Ma'u ta dubi A'isha wadda ke ta huci ta ce. "Kin ga A'isha ki daina yiwa Ɗan_Juma tsiwa, ni ina tsoron kar wataran ya yi miki shegen duka, kin san halinsa fa." Tsaki A'isha ta yi ta ce. "Tab'dijan, sai ka ce wata ƴarsa zan zauna ya dake Ni, wallahi ya yi kaɗan." Ma'u bata kuma magana ba har suka ƙarasa makarantar. Kamar yadda Ma'u ta faɗa babu wanda ya zo sai mai_gadi wanda shine yake buɗe Makarantar, su ne na farkon zuwa. Bayan sun shiga ajinsu suka ajiye jakunku nansu suka shiga sharar ajin, dama kullum su suke yin sharar. Sai da ƙarfe tara ta wuce sannan sauran yara suka fa zuzzuwa da Malaman Makarantar. A'isha suna zaune akan desk ita da Ma'u wata yarinya wadda baza ta wuce sa'ar su ba ta zo ta tsaya a gaban A'isha, cikin tsiwa da neman faɗa ta ce. "Matsa zan wuce in zauna." A'isha ta kalli Ma'u dake jikin bango sannan ta kalli yarinyar ta ce. "Ina kuma zaki shige Kandala? Bayan ga guri a nan?" Ta ƙarashe zancen tana nuna mata gefenta inda babu kowa. Kandala ta ce. "Inda kike zaki matsa mun in zauna mana." Kallon sama da ƙasa A'isha ta yi mata ta ce. "Sannu Inna." Daga haka ta ɗauke kanta bata kuma magana ba, dan ba ta san su yi faɗa, saboda kullum kafin ta fito daga gida sai Inna ta gargad'e ta akan ko an tsokane ta kar ta biyewa kowa balle su yi faɗa. Kandala da dama neman tsokana ne ya kawo ta, ta ce. "Kar ki matsa ɗin, banza kawai, shegiya Mayya." Da sauri Ma'u ta dube ta, ta ce. "Haba Kandala mene ne haka?" Hararar Ma'u Kandala ta yi ta ce. "Malama ban saka baki da ke ba, ke dama ai sun riga sun gama cinye kurwarku ke da Innarki, shi yasa komai ta yi ba kya ganin lefin ta." Miƙewa tsaye A'isha ta yi ta ce. "Kar ki ƙara ce mun Mayya ke Kandala." Cikin ɗaga murya Kandala ta ce. "An faɗa ɗin Mayya ce ke mara Uba, Shegiya sai me?" Sauran ƴan aji suka tattaso suka ƙaraso gurin dan bawa idonsu abinci, Kandala ta dube su ta ce a bugawa A'isha gangar Shegiya Mayya. Nan fa yara suka fara buga desk da jarkokin ruwansu suna yiwa A'isha ihun Mayya da SHEGIYA cikin waƙa. Komawa A'isha ta yi ta zauna tare da toshe kunnuwanta da hannayenta saboda yanda ihun da suke yi yake shigar mata har cikin kai. Wasu Hawaye masu zafi suka fara zuba akan kuncinta, kusan kullum idan ta zo makarantar sai an yi mata wannan ihun aka, duk da yanda ko an tsokane ta bata kula mutum saboda gudun hakan, amma ba sa ƙyale ta Yaran. Cikin tausayawa Ma'u ta rungumo ta jikinta tana bata haquri. Shigowar wani Malami ce tasa yaran suka yi tsit bayan ya daka musu tsawa tare da buga ƙofa. A fusace ya ce. "Kowa ya nemi guri ya zauna." Bayan sun zauna ya dube su ya ce. "Ihun Uban me kuke mana a aji? Duk kun cika mana makaranta da hayaniyarku." Ma'u ce ta ce. "Malam Kandala ce ta ce su yiwa A'isha ihun Mayya da SHEGIYA." Sai a lokacin Malam Buba ya dubi A'isha wadda ke kuka sosai ya ce. "Ina Kandalar take? Ta miƙe tsaye." Kandala ta miƙe tana cuccuna baki gaba kamar bakin tulu, Malam ya ce ta fito gaban allo ta yi kneel down ta rufe ido, sauran Yaran ma ya saka su yin haka amma su kowa a inda yake zaune, ban da A'isha da Ma'u. Sannan ya rarrashi A'isha ya bata baki ta yi shiru ta bar kukan da take yi. Gaban allo ya koma ya ce. "Dama abun da ya kawo ni na zo ne in sanar muku za'a ɗauki mutum uku masu ƙoƙari a cikin ajin nan wanda za su zana common entrance tare da ƴan aji Shida." Kasancewar su A'isha a Primary 5 suke. Nan fa yara suka fara murna kowa yana fatan a ɗauke shi. Malam Buba ya karanto sunan Yara Ukun ciki har da A'isha. Wannan abun ya yayewa A'isha damuwar ihun da ƴan ajin suka yi mata, sai su gata suna ta tsalle da murna ita da Ma'u.
Bayan an tashi daga makaranta sun koma gida A'isha ta tarar Inna bata nan, ko uniform bata cire ba ta fara duban abinci ko Inna ta girka ta ajiye mata amma bata ga komai ba. Zama ta yi a tsakar gida tana jiran dawowar Inna, sai dai har Ma'u ta biyo mata zuwa gidan Malama karatu Inna bata dawo ba, haka ta tashi ta shiga ɗaki ta canza kaya suka tafi karatun yunwa na ƙwaƙular hanjin cikinta. Sai Yamma suka dawo, zuwa lokacin yunwa ta fara galabaitar da A'isha. Inna tana wankin kayan sakawarsu A'isha ta shigo da sallama can ƙasan mak'oshi. Inna ta amsa mata tare da bin ta da kallo. A'isha ta turo baki ta ce. "Inna Ina kika je? Na dawo na tarar ba kya nan." Inna ta ce. "Sabon Gari na je." Ba ta jira cewar A'ishan ba ta tsame hannunta daga cikin ruwan wankin ta shiga ɗaki ta ɗaukowa A'isha k'uli_k'uli mai gishiri da awara ta bata. Da murna A'isha ta karɓa ta ce. "Inna yau yunwa ta kusa kashe ni fa." Inna ta ce. "Tunda bata kashe kin ba sai ki yiwa Allah godiya." Bayan A'isha ta gama cin awarar da k'uli_k'ulin ta sha ruwa ta dubi Inna ta ce. "Inna Ina son in tambaye ki wani abu." Inna ta ce. "Ina jin ki." A'isha ta ce. "Dan Allah Inna da gaske Baba Malam ba shine Babana ba? Kuma ba mu da asali?" Haɗe rai Inna ta yi ta ce. "Ba na ce kar ki ƙara mun wannan tambayar ba A'isha?" Cikin raunin murya A'isha ta ce. "Inna ki yi haquri kin faɗa mun, amma Inna ke baki da qani ne ko Yaya ko k'anwa kamar Innar Ma'u? Kin ga ita suna zuwa Kano gurin ƙaninta, kuma suna zuwa Sanda gidan Inna larai k'anwarta, amma mu ba ma zuwa gidan kowa." A'isha ta ƙarasa Maganar cikin raunin murya. Shiru Inna ta yi gabanta na fad'uwa, a ranta tana faɗin. Tun yanzu A'isha ta fara tambayar ta wani nasu? ina ga ta ƙara girma da wayo ta san me duniya take ciki? Tabbas dole ta yiwa tufkar hanci tun yanzu, ta kuma san me zata faɗawa A'isha wanda zai kwantar mata da hankali. Ganin Inna ta yi shiru cikin raunin murya A'isha ta kuma cewa. "Dan Allah Inna mu ma muna zuwa gurin ƴan'uwanmu a daina ce mana marasa asali." Sosai tausayin A'isha ya cika zuciyar Inna, ta san dole abun ya dame ta duk da kasancewarta yarinya, ko dan yanda mutanen gari suke muzanta_ta akodayaushe. Tasowa Inna ta yi ta dawo gaban A'isha cikin sanyin murya ta ce. "A'isha! INSHA ALLAHU watarana zamu je gurin ƴan'uwanmu mu ma kamar kowa, kin ji?" Hawaye A'isha ta fara ta ce. "Yaushe Inna? Mu je gobe mana." Inna ta girgiza kanta ta ce. "Inda suke ne da nisa A'isha, sai na tara mana kuɗin Mota, Nima ina son mu je ɗin, amma mun kusa zuwa insha Allahu." Gyaɗa mata kai kawai A'isha ta yi. Inna ta ce. "Jiya da kika je ɗiban ruwa me aka yi miki kika dawo da kuka?" A'isha ta ce. "Ce mun aka yi MAYYA SHEGIYA a gurin, yau ma a makaranta an mun ihun haka a aji." Kama hannunta Inna ta yi cikin lallami ta ce. "Ki yi haquri A'isha, duk abun nan da ake yi miki ni na jawo miki, amma insha Allahu komai zai wuce, duk wannan abubuwan da ake yi mana sai sun zamo tarihi, watarana komai zai wuce da yardar Allah, KOMAI NISAN DARE gari zai waye A'isha, ki ƙara hakuri." A'isha ta ce. "Shikenan Innata." Inna ta ce. "Yawwa A'ishana, share hawayen naki ki tashi ki dauraye mana kwanikan can kafin a kira Sallah." A'isha ta miƙe ta ce. "Toh." Inna ta bi ta da kallon tausayi kafin ta miƙe ita ma.