← Book details Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 55

Sashe 18

Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tunda bayan da Inna ta kai A'isha makaranta ta wuce Sabon gari kamar yadda ta ce, tana zuwa ta tarar lokacin za'a fara aikin k'uli_k'ulin, zama ta yi aka fara aikin da ita. Ba su gama aikin da wuri ba, dalilin da ya saka kenan ba ta koma makarantar su A'isha ba, yin aikin kawai take yi amma hankalinta gaba-d'aya yana gurin A'isha. Lokacin da suka gama aikin haɗarin nan ya haɗo sosai, amma haka Inna ta taho gida saboda hankalinta gaba-d'aya yana kan A'isha, har fad'uwa ta ji gabanta yana yi ba tare da ta san dalili ba. Sai dai tun kafin ta ƙarasa gida aka fara ruwan, duk da haka ta so zuwa ta ɗauko A'isha a ruwan, amma saboda yanda ruwan ya yi ƙarfi yasa dole ta hak'ura ta wuce gida ba dan ta so ba. Tunda ta koma gidan sai ta kasa tsaye ta kasa zaune, haka kawai ta ji zuciyarta ta kasa nutsuwa, ga gabanta da yake ta fad'uwa. Addu'a ta dinga yi akan Ubangiji yasa a ɗauke ruwan ta je ta gano halin da ƴarta take ciki. Ana fara tsagaita ruwan kuwa ta ɗauki buhu ta lullub'a a kanta ta nufi makarantar su A'isha, tana zuwa ta tarar babu kowa makarantar ma a kulle take. Hankalinta a matuƙar tashe ta dawo gida zuciyarta cike da tarin tambayoyi akan inda A'isha take. Tana shiga soron gidan su ma su A'isha suna shiga. Juyowa ta yi jin takun tafiya a bayanta, da sauri ta dawo baya cikin zak'uwa ta ce. "A'isha!" Jin muryar Inna yasa A'isha ta fara kuka tare da janye hannunta daga cikin na Matashin. Inna ta rungume ta tare da sakin ajiyar zuciya. Cikin kuka A'isha ta ce. "Inna ina kika tafi ba ki zo kin ɗauke ni ba?" Inna ta ce. "Ban dawo da wuri ba ne A'isha, da fatan babu abun da ya same ki? Ruwa bai dake ki ba ko? Na ji jikinki da lema, ina takalmanki?" A'isha ba ta iya bawa Inna amsa ba sai kuka kawai take yi. A rud'e Inna ta ce. "Me ya faru dake ne A'isha? Me aka yi miki kike wannan kukan?" Ta ƙarashe maganar tare da ɗago ta daga jikinta. Matashin dai kawai kallon su yake yi cikin tausayawa, yanda A'isha take ƙanƙame Inna yasa ya gane har lokacin a cikin firgici take. A hankali ya ɗan risina ya cewa Inna "Ina Yini?" Inna da ta manta ma A'isha tare suke da wani ta ɗago ta dube shi ta ce. "Lafiya ƙalau." Kallon shi Inna ta dinga yi ko kiftawa babu gabanta na fad'uwa, ƙasa ya yi da kansa ya miƙawa Inna jakar A'isha. Inna da duk zaton ta sabon Malami ne shi aka kawo a makarantarsu A'isha dan ko kusa bai yi kala da ƴan garin ba ta sauke ajiyar zuciya, cikin sanyin murya ta ce. "Mun gode sosai Bawan Allah, Allah ya saka da Alkhairi." Shafa kansa ya yi ya ce. "Babu komai Mama, bari na wuce na ji an shiga Sallah, akwai maganar da nake son mu yi dake idan babu damuwa sai na dawo gobe da safe mu yi in Allah ya kai mu." Inna ta da kasa ɗauke idonta daga kansa ta ce. "Babu damuwa ɗan nan, Allah ya kai mu goben lafiya." Ya amsa da Ameen, sannan ya yi mata sallama ya tafi, har ya fice daga soron Inna ta kasa ɗauke idonta daga kansa, kallon sa take yi cikin wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa. Kama hannun A'isha ta yi wadda ke kuka har lokacin suka shige cikin gida, abun mamaki suna shiga Inna ta ga Ramatu ta bar bakin zauren da sauri ta shige cikin ɓangarensu har tana tuntub'e, ko tantanma Inna ba ta yi leken su take yi ta ga me suke yi a zauren jin muryar Namiji. Girgiza kai kawai Inna ta yi ta wuce. Tambayar duniya Inna ta yiwa A'isha akan me ya faru bayan sun zauna amma A'ishan ta ƙi faɗa mata, sai kuka kawai take yi. Gajiya ta yi ta kama yi mata faɗa, cikin takaici ta ce. "Wanne irin iskanci ne wannan A'isha? ina miki magana kin mayar da ni wata gantalalliya, sai kukan banza da kika sani a gaba kina yi, ki faɗa mun me ya samu fuskarki na ga kamar shatin hannu? Ina takalmanki kuma suke?" A'isha ta share hawayen fuskarta ta bawa Inna labarin duk abun da ya faru. Cikin tsananin tashin hankali Inna ta ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, su waye waɗan nan azzaluman?" A'isha ta ce. "Ban san su ba nima." Inna ta fara hawaye ta ce. "Hasbunallu'wa ni'imalwakil, Allah ka shiga tsakanin mu da waɗan nan azzaluman da ba mu san ko su waye ba, Allah ka saka mana, Ubangiji karka ba su ikon cutar da wannan baiwa taka ko nan gaba. Allah na gode maka da ka kub'utar da ita. Wannan wanne irin abu ne, daga wannan sai wannan." A'isha ta ce. "Inna waye ya kawo ni gida? Ni ban gane muryarsa ba." Inna ta ce. "Ni ma ban san shi ba A'isha, da alama baƙo ne a cikin garin nan." A'isha ta shinshina jikinta ta ce. "Ɗan gayu ne ko Inna? Na ji yana ta ƙamshi mai daɗi, ni ma kin ji kayana suna yin ƙamshin ya shafa mun." Inna ta bi ta da kallo tana jinjina sha'anin k'uruciya, ban da haka ita da aka so yi mata fyaɗe har ta soma manta abun cikin ƴan mintuna ta fara sakin ranta. Kwanciya ta yi a jikin Inna cikin raunin murya ta ce. "Kaina ciwo, duk jikina ma haka musamman ƙafata da suka tattaka mun." Inna ta ce. "Allah ya saka miki, bari na ɗora miki ruwan zafi ki yi wanka sai ki ji daɗin jikinki, idan kika ci abinci kuma sai ki sha magani ki kwanta."

A ɓangaren Matashin nan, yana fita cikin sauri ya nufi gidan Sarki dan yin alwala, a zaure ya tarar da su Ɗan_juma wanda suka iya tashi daƙyar suka fito. Wani mugun kallo ya watsa musu ya shige ɗakinsa. Hamza ya sauke numfashi ya dubi Ɗan_juma wanda ya bi bayan Matashin da wata muguwar harara ya ce. "Wai waye wannan ɗin ne Ɗan_juma da ya bazar da mu?" Harara Ɗan_juma ya banka masa ya ce. "Ban sani ba, ragwayen banza kawai, kuna gani yana auna mun naushi amma kuka kasa yi masa komai kuna kuku biyu sai ma ƙoƙarin guduwa kuka yi." Hamza ya ce. "Mu fa ba ragwanta ce ta saka muka yi yunk'urin guduwa ba, tsoron muke kar asirinmu ya tonu ya je ya faɗawa Sarki a hukunta mu." Ɗayan ya ce. "Ai har yanzu ma a cikin tsoron muke, tunda ba mu sani ba ko zai faɗa ɗin." Tsaki Ɗan_juma ya yi ya ce. "Wannan kuma ku ta shafa, dan ni ko a jikina, amma wallahi Wannan garan bai daki banza ba, sai na ɗauki fansar abun da ya mun." K'wafa ya yi ya fice daga zauren fuuuu kamar zai tashi sama, su Hamza suka mara masa baya. Daren yau gaba-d'aya Matashin nan da tunanin su A'isha ya yi shi manne a cikin zuciyarsa, ya rasa tausayi ne ko mene ne ya mamaye masa zuciya akan A'isha a gani ɗaya tak da ya taɓa yi mata yau a cikin rayuwarsa, hakan ya yi matuƙar ɗaure masa kai da ba shi mamaki ba kaɗan ba.....✍️

*By*
*Zeey Kumurya*
*💖 KOMAI NISAN DARE.....! 💖*

_By_
_Zeey Kumurya_

*ELEGANT ONLINE WRITER'S*

*1️⃣0️⃣*

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 08066268951

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
Chapter 18 · 0% Book details