← Book details Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 55

Sashe 7

Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Idar da Sallar Innar Ma'u kenan Inna ta shiga gurinsu. Tun daga yanayin Sallamar Inna, Innar Ma'u ta san ba ƙalau ba. Bayan ta bata gurin zama ta zauna, ta ce. "Innar A'isha lafiya kuwa?" Inna ta sauke numfashi murya a sanyaye ta ce. "Jikin A'isha ne ya tashi wallahi Ladidi, dama kwana biyu tana mun k'orafin kanta na damun ta da ciwo sosai." Innar Ma'u ta ce. "Subhanallahi, ciwon kai kuma? Na sha ai jikin nata ya yi sauƙi yanzu." Inna ta ce. "Jikin ya yi sauƙi, ciwon kan ne dai." Innar Ma'u ta ce. "Gaskiya asabe ya kamata ki kai yarinyar nan asibiti a duba jikin nan nata, ko kuma ki kai ta gurin masu magani namu na gargajiya." Inna ta ce. "Shine abun da ya kawo ni dama, Na yanke shawarar gobe kawai zan kai ta asibitin Rano ne da safe." Innar Ma'u ta ce. "Ya kamata dai, amma wannan ciwo ya ƙi tafiya, yarinya tafi sati a kwance." Inna ta ce. "Ban san me yasa hankalina ya ƙi kwanciya da wannan ciwon na A'isha ba, duk da ba wani dad'ewa ta yi sosai a kwance ba, amma gabana sai fad'uwa yake yi." Cikin son kwantar mata da hankali Innar Ma'u ta ce. "Haba_haba, babu komai fa Asabe, insha Allahu zata samu lafiya, zazzaɓi ne dai kawai irin wanda ake yi." Inna ta sauke numfashi ta ce. "Allah yasa, amma dan Allah Innar Ma'u karki gaji da ni, aron kuɗi dai zaki kuma bani idan kina da shi, in Allah ya bata lafiya sai na nemi abun yi na biya ki." Cikin tausayawa Innar Ma'u ta ce. "Babu komai, ai na san baki da shine Asabe, Jiya Muntari ya turo mun da kuɗi, bari Ma'u ta dawo daga kasuwa sai ta je a ciro kuɗin na baki ki kai ta asibitin, Allah yasa kuɗin ya isa dan dubu Uku ne ya turowa Ma'u ta siyi takalmin kwalliya." Inna ta ce. "Na karɓewa Asma'u kuɗi kuwa?" Innar Ma'u ta ce. "To mene ne? Ai cuta ce, magani ai yana gaba da takalmi tunda ba rasa na sakawa ta yi ba, in ma baki samu kuɗin ba idan an yi mun biyan bashi sai na siya mata." Inna ta ce. "Toh shikenan, Na gode Na gode sosai Asabe, Allah ya saka da Alkhairi ya ji ƙan Mahaifa ya raya zuri'a, babu abun da zance miki akan irin taimakon da kike mun, sai dai Ubangiji Allah ya biya ki kawai." Innar Ma'u ta ce. "Ameen, amma mene abun godiya, ai duk yiwa kai ne." Inna zata kuma magana ta jiyo muryar A'isha daga ɓangarensu tana ƙwala mata kira. Da sauri ta miƙe ta koma zagayen nasu, Innar Ma'u ta mara mata baya. A tsakar gida suka tarar da A'isha tana laluban bango, Inna ta riƙe ta da sauri tare da faɗin. "Gani A'isha, mene ne?" Aisha ta ce. "Inna fitsari nake ji, kuma na fito zan je bayi amma bana ganin komai." Inna ta ce. "Kamar ya ba kya ganin komai?" A'isha ta ce. "Wallahi Inna duhu sosai kawai nake gani, ko idona a rufe yake ne?" A rikice Inna ta ce. "Duhu kuma A'isha? wanne iri? ga hasken farin wata nan ana iya ganin komai, kuma idanunki a buɗe suke tar." Lalubar hannun Inna Aisha ta yi ta kai saitin idonta ta ce. "To Ni dai Inna bana ganin komai sai duhu, ke ma fa bana ganinki kwata_kwata."...........✍️

_*Not Edited*_

*By*
*Zeey Kumurya*
*💖 KOMAI NISAN DARE.....! 💖*

_By_
_Zeey Kumurya_

*ELEGANT ONLINE WRITER'S*

0️⃣5️⃣

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 08066268951

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
Chapter 7 · 0% Book details