Sashe 41
Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kallon Abba Ummi ta yi idanunta cike da ƙwalla ta ce. "Ina ganin mu bari yarinyar nan ta dawo cikin hayyacinta sai mu sanar mata yadda hankalinta zai ɗauka."
"Mutuwa ba a shirya mata Dr, a duk lokacin da za mu faɗa mata sabuwa take a gurin ta, kuma dole sai ta sani, don haka babu amfanin ɓoye-ɓoye."
"Hakane." Ummi ta faɗa tana gyara wa A'isha zamanta, wadda ke zaune tamkar mutum mutumi." Cikin sanyin murya ta fara magana. "Ba mafarki kike ba Mamana, Allah ya yi wa mahaifiyarki rasuwa, ga gawar ta nan a gabanki." Ummi ta ƙarashe maganar tare da ɗora hannun A'isha a kan gawar Inna. Kuka ta fashe da shi don zuwa yanzu ta tabbatar ba mafarki take ba, amma kuma zuciyarta ta kasa yarda Innarta ta rasu, Innalillahiwa'inna'ilaihirra'ji'un kawai take maimaitawa cikin sarƙewar harshe, numfashinta na fita a rarrabe tamkar zai bar gangar jikinta. Jikinta na kyarma ta buɗe bakinta cikin rawar murya ta ce. "Ya Ubangiji ka yi gaggawar farkar da ni daga wannan mummunan mafarkin da nake, na san ba gaskiya ba ne, na san Inna ba za ta taɓa mutuwa ta bar ni ba saboda ta san ba ni da kowa sai ita, don Allah su waye ku? Ku tashe ni daga wannan mummunan mafarkin da nake." Ta ƙarashe maganar tana laluben hannu Ummi. Rungume ta Ummi ta yi tana rarrashinta da ba ta baki, amma ba ta fahimta, babu abin da take ganewa. Da ƙyar ta iya amsa tambayar da Abba yake nanata mata ta daga ina suke? Ya buƙaci ta faɗa masa sunan gidansu dan a sanar da ahalinsu halin da ake ciki, sai ta ce masa ba su da kowa. Daga nan ba ta ƙara magana ba. Duk yadda Abba ya so ya samu wani information ɗin amma bai samu ba, har yamma ta yi ba akai Inna makwancinta ba. Alhaji Abubakar abokin Abba da ya dawo gidan a lokacin ya ce. "Ina ganin Alhaji Sa'id a tara jama'a kawai a yi wa matar nan Sallah akaita makwancinta, dare yana yi kuma mun san ba a son jinkirta kai mamaci." Numfashi Abba ya sauke ya ce. "Haka ne, amma da na fi so mu sanar da ƴan'uwanta su zo su ga gawar akai ta tare da su."
"To Alhaji Sa'id ina muka san inda suke? Ita yarinyar da suke tare amsa É—aya take ba mu ba su da kowa, mu kai ta kawai daga baya idan yarinyar ta dawo cikin nutsuwar ta sai mu je a sanar musu, amma idan ba haka ba gawar nan sai ta kwana." Cikin gamsuwa Abba ya ce. "Shikenan, bari na saka a sanar a masallaci, sai a nemo mai wankan gawa ta mata, Allah ya gafarta mata."
"Amin."
Kasancewar Abba babban mutum ne ana sanarwa a masallaci mutane suka fara taruwa a ƙofar gidan, maƙwabta mata kuma suka shiga cikin gida. A'isha dai tana zaune tamkar mutum-mutumi, ba ta fahimtar komai da yake faruwa, magana ma in an yi ba ta ji saboda komai nata ya tsaya cak, wani irin numfashi take fitarwa da sauri da sauri. Ummi na kusa ita tana tofa mata addu'a. An yi wa Inna wanka an haɗa ta an saka a cikin makara, jiki a sanyaye Ummi ta kamo A'isha ta tsugunnar a gaban gawar ta ce. "Ki yi mata addu'a, za a kai ta gidanta na gaskiya." Cikin fitar hayyaci A'isha ta ce. "Me zan ce? Ya ake addu'ar? Don Allah kar ku raba ni da Innata, ku bar mini ita a haka ina son ta, zan rayu da ita ko ta mutun." Sai kuma ta kama girgiza kai tana faɗin. "Innata ba ta mutu ba, don Allah Inna ki tashi ki ce musu ba ki mutu ba, na san ba za ki tafi ki bar ni, ni kaɗai ba." Ta ƙarashe maganar tare da ɗora kanta a kan gawar ta ƙanƙame ta. Da ƙyar aka ɗaga ta daga kan gawar, don tamkar mai iskokai haka ta koma, maganar wata tsohuwa da ta shigo tana cewa. "Shikenan fa rayuwar, yanzu ita ta tafi saura mu, Allah ya ji ƙan ta ya kyauta namu zuwan." Ya sa A'isha sumewa a jikin Ummi da ta riƙe ta.
Safa da marwa kawai take yi a cikin makeken parlour'nta wanda ya ƙawatu da kayan alatu. Shigowar Baby ya sa ta dakatawa tana mayar da numfashi. Da mamaki Baby take bin ta da kallo.
"Mommy lafiya kuwa na gan ki a hargitse?"
"Ina fa lafiya Baby? Ba ki ga abin da mahaifinku ya yi ba ne?"
"Me ya yi Mommy?"
Taune leɓe ta yi alamun abun ya daki zuciyarta ba kaɗan ba ta ce. "Anan gidan fa aka yi wa matsiyaciyar matar da ya kaɗe sutura aka yi mata Sallah, maimakon ya kai ta can danginta su yi mata, ko kuma cewa aka yi dan ka kaɗe mutum ka yi masa sutura a gidanka?" Cikin rashin damuwa Baby ta ce. "To mene abin damuwa Mom? Daga an kai ta ba shikenan ba." A tsawace Mommy ta ce. "Akwai abin damuwa babba ma kuwa, a yi wa gawar talaka sutura a cikin gidan da nake ki ce mene abin damuwa? Talaka fa! Kin san yadda na tsani talauci da talakawa kuwa? Yadda nake jin tsanar talaka a cikin raina wallahi da ina da hali ƙasar da nake ciki a zaune ma ba zai zauna ba!" Ta ƙarashe maganar cikin ɗaga murya.
Yadda A'isha ta faÉ—i babu numfashi a jikinta ya taÉ—a hankalin su Ummi, Family Doctor É—insu ta kira ya zo ya ba ta taimakon gaggawa. Har bayan isha'i A'isha ba ta farka daga allurar baccin da aka mata ba, sai wajen É—aya na dare ta farka da wani irin ciwon kai da nauyin Æ™irji, har lokacin ba ta gama dawowa cikin hayyacinta ba.......âœï¸
_*Alhamdulillah, uzurin da ya riƙe ni yake hana ni posting akan lokaci na kammala shi, insha Allahu yanzu za kuna ji na kodayaushe, na gode.*_
*💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖
*_Zeey Kumurya_*
*ELEGANT ONLINE WRITER'S*
*2ï¸âƒ£4ï¸âƒ£*
Da ruwan ɗumi Ummi ta gogge mata jikinta tare da sauya mata kaya zuwa wata doguwar riga mara nauyi ta yarta MUNEEFAH dake boarding school. Ta haɗo mata tea mai kauri amma ta kasa sha, duk yadda Ummi ta yi da ita akan ta sha amma ta ƙi, sai haƙura ta yi ta ƙyale ta. Tun wannan farkawar ba ta kuma komawa bacci ba har garin Allah ya waye. Har yanzu zuciyarta ta kasa aminta Inna ta rasu, ta kasa yarda ta tafi ta bar duniya, ta kasa yarda ba za ta kuma ganin ta ba har abada a cikin zuciyarta. Damuwa da tashin hankali mara misaltuwa suka cika zuciyarta, so take ko ɗison hawaye ne ya zubo mata dan ta ji sauƙin abin da take ji a cikin zuciyarta, amma kukan ya ƙi zuwa. Sai a wannan lokacin ta gane ashe kuka ma Rahama ne. Ta yi addu'ar Ubangiji ya ɗauki ranta a wannan daren ita ma babu adadi, saboda ba ta san ina za ta saka kanta ba, ba ta san ta yaya za ta fara rayuwa ita kaɗai babu Inna ba, ba ta san ta yaya za ta kula da rayuwarta ba alhalin tana makauniya. Ina za ta ga danginta? Wa zai sada ta da su tunda babu Inna? Tunanikan da ta kwana tana yi kenan, hakan ya ƙara rurucewar ciwon jikinta, zazzaɓi mai zafin gaske ya rufe ta haɗe da zazzafan ciwon kai. Yadda ciwon ya galabaitar da ita ko ɗanyatsa ba ta iya motsawa. Hankalin Ummi ya ƙara tashi ganin yadda take rawar ɗari, numfashinta na fita da sauri da sauri. Addu'a suka haɗu suka ita da Abba suna tofa mata cikin ɗimauta da yanda jikin nata ya yi tsanani. Ana yin Sallar Asuba suka ɗauke ta zuwa asibiti. Suna zuwa aka karɓe ta tare da ba ta taimakon gaggawa. Ganin ta samu bacci Abba ya koma gida ya bar Ummi tare da ita. A main parlour ya ci karo da Khalifa. Cikin girmama ga gaishe shi, amsawa Abba ya yi cikin kulawa.
"Ya jikin yarinyar?"
"Da sauƙi Khalifa, na baro ta ma tana bacci."
"Allah ya ƙara sauƙi, Yanzu Ya Maamah ta kira ni wai za ta biyo jirgin 8 ta zo, ta ce na maka jaje kafin ta ƙaraso, ta kira wayarka kai da Ummi ba ku ɗauka ba." Abba ya ce. "Allah ya sauke su lafiya sai sun ƙaraso."
"Amin." Khalifa ya faɗa tare shigewa ɗakinsa. Abba yana shiga part ɗinsa ya tarar da Mommy Hakimce a kan kujera, yana ganin yadda fuskarta take murtuk ya san ba ƙalau ba, haɗe tasa ya yi shi ma don ya san neman fitina ne kawai ya kawo ta kamar kodayaushe.
"Sannu Sa'id."
Ta faɗa cikin rashin ladabi. Abba dake ƙoƙarin shiga ɗakinsa ya dakata ba tare da juyo ba. Ba ta damu ba ta ci gaba da magana cikin ɓacin rai. "Wai me kake nufi da barin yarinyar can a cikin gidan nan?"
"Gidanki ko nawa?" Ya yi maganar a tsawace tare da juyowa.
"Na É—ana ne." Ta ba shi amsa kai tsaye.
"To idan kin isa ki saka ɗan naki ya zo ya fitar da ita daga gidan. Saratu ki kiyaye ni fa da wannan haukan banzan naki, kar ki kai ni bango na faɗa miki!" Ya ƙarashe maganar cikin ɗaga murya mai haɗe da tsawa. Ba ta ce komai ba ganin yadda ya ɗauki zafi, ƙwafa ya yi ya shige ɗaki cikin ransa yana mamakin wacce irin zuciya ce da Saratu, ana girma ana hankali da tunanin lahira amma ita ƙara haukacewa take da son duniya. Da harara Mommy ta raka shi, tsanar Ummi na ƙara cika mata zuciya, don ta san duk wannan abun ita take kitsa shi. Ƙwafa ta yi ta miƙe tana ƙissima matakin da za ta ɗauka a cikin ranta.