Sashe 33
Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ba ta ce komai ba ta samu guri ta zauna, zuciyarta cike da damuwar rashin jin Umar da masifar gidansu da ba ta ƙarewa. A sanyaye ta ce. "Ina wayar nan Inna? Bai kira ba ko?" Girgiza kai Inna ta yi cikin tausayawa ta ce. "Bai kira ba, ki yi haƙuri ki cire damuwar hakan daga ranki, addu'a ya kamata ki yi masa Allah ya sa yana lafiya."
"Insha Allahu, ya ce akwai karatun Alkur'ani a cikin wayar, ki É—auko ki kunna mini."
"Ai ban san ta yadda zan kamo ba, amma bari anjima idan zan je shago siyayya, sai mu biya gurin mai chaji ya kunna miki."
Kwana Uku A'isha ta yi tana jinin sannan ya ɗauke, kamar yadda Inna ta sanar mata alamar da za ta ji ta san ya ɗauke, tana ji ta sanar da ita, duk da an koya musu yadda ake wankan tsarki amma sai da Inna ta ƙara yi mata bita domin ta yi shi yadda ya kamata. A ranar Inna ta ƙirga kuɗaɗen da Umar ya ba ta ranar da zai tafi, dubu ɗari da goma ne, ta zazzari wasu sun yi amfani da su saura dubu ɗari da biyu. Cikin farinciki ta haɗa musu kayansu don tafiya asibitin Kano gobe a duba A'isha, dama jira take ta samu tsarki sai su tafi.
"Wai Haulatu ba za ki bar kukan nan ba? Na ce ki kwantar da hankalinki in dai Umar ne zai zo da ƙafafun shi har inda muke, ina nan ina shiri akan hakan."
Haulatu dake gunjin kuka ta ce. "Yaushe zai zo to? Tunda ya tafi kike ce mini haka, kuma yau an fi sati da tafiyar tasa bai dawo ba." Cikin lallami Uwa ta ce. "Gaggawar me kike ne? Ki bi komai a sannu ze zo ne ai." Zunɓura baki ta yi ta ce. "Gaskiya ni dai na gaji da jira, so nake kawai na gan shi ko na ji muyar shi, ki je gurin Sarki ki karɓo mana lambarsa, na san ba zai rasa ba." Shiru Uwa ta yi cikin nazari sannan ta ce. "A baya na je na karɓo lambar Mahaifiyarsa, yanzu kuma na koma na karɓo tasa? Ba zai yiwu ba gaskiya, kin san Sarki da saurin gane abu, dole zai fuskanci akwai abin da muke ƙullawa, sai dai mu je gurin su waccar makauniyar yarinyar, na san ba za su rasa ba."
"Kina ganin za su ba mu kuma Uwa?"
"Na san me zan ce musu da dole za su ba mu, tashi ki ɗauko mini gelena mu je yanzu-yanzu, da zafi-zafi ake dukan ƙarfe."
Cikin farinciki Haulatu ta share hawayen fuskarta tare da miƙewa.
A'isha tana zaune a tsakar gida ta yi tagumi tana tunanin Umar su Haulatu suka kwaÉ—a sallama. A sanyaye ta amsa musu. Haulatu dake bin ta da Kallon tsana ta ce. "Asaben ba ta nan ne?" Cikin jin haushin yadda Haulatu ta gatsa mata sunan Inna A'isha ta ce. "Me ya faru?" Kafin Haulatu ta kuma magana Inna ta fito daga bayan gidan da ta zaga, da fara'a take duban Uwa.
"Ku ne a tafe? Sannun ku da zuwa, ku zauna mana, kwa tsaya a tsaye." Ta yi maganar tana ware musu tabarmar da A'isha take zauna. Bayan sun zauna ta kawo musu ruwa Uwa ta dube ta, ta ce. "Asabe lambar waya muka zo karɓa a gurin ku." Cikin mamaki Inna ta ce. "Lambar wayar wa?"
"Ta Umar baƙon yaron da ya zauna a gidanmu, don mun san ba za ku rasa ba."
Dam! Gaban A'isha ya yanke ya faÉ—i, da sauri ta É—ago kanta amma ba ta ce komai ba.
"Ayya, ai kuwa ba mu da lambar shi, don kwana uku mun je gurin mai chaji akan ya duba mana cikin wayar da ya bar mana ko akwai lambar waya amma ya ce ma babu, daga ta kamfanin layi sai ta layin da yake cikin waya....."
"Sai dai in ba za ku ba mu ba ne kawai, amma mun san kuna da ita." Haulatu ta katse Inna cikin rashin É—a'a."
Inna ba ta ce komai ba sai kallon yarinyar da take cikin mamaki. Æata fuska Uwa ta yi ta ce. "To ai shi ya ce mu zo mu karÉ“a a gurin ku, saboda yana so su dinga waya da Haulatu, da zai tafi kuma ya manta yana sauri bai ba ta ba, abin da ya sa ma muka zo saboda kar ya gaji da jiran kiran mu, ga rashin jin muryata da ba ya yi zai iya jefa shi cikin wani hali, kin san ba Æ™aramin Æ™aunar ta yake ba."
"To sai ku jira idan ya gaji da rashin jin murya tata ya dawo garin ya ba ku lambar da kansa, ina ganin hakan zai fi kyau ko?" Inna ta faÉ—i haka cikin haÉ—e rai.
"Ko ba ki faɗa ba ma zai dawo, tunda ya gani yana so, ƴan baƙin ciki sai dai su mutu, yarinya ƴar dangi da asali zai aura ba baƙin haure ba."
ÆŠan murmushi kawai Inna ta yi ba ta ce komai ba. Zuciya babu daÉ—i su Uwa suka zira takalmansu suka fice.
A'isha da ta yi mutuwar zaune cikin bugawar zuciya tun lokacin da Uwa ta ambaci soyayya tsakanin Umar da Haulatu ta ji wasu hawaye masu É—umi sun shiga rige-rigen zuba akan kuncinta, ba tare da ta san dalili ba. Ita tana nan tana zaman jiran kiran shi ashe ba ta ita yake ba, ko tantanma ba ta yi wannan dalilin ne ya hana shi kiran ta.
"Kada ki bari wannan zancen ƙanzon kuregen ya yi tasiri a zuciyarki, na san yanzu ƙaramin tunanin ki ya ba ki abin da ba shi ba ne." Inna ta faɗi haka cikin tausasa harshe.
Ajiyar zuciya ta sauke ba don kalaman Inna sun gamsar ita ba, duk da ƙarancin shekarun ta amma kalaman Uwa ba ƙaramin dukan zuciyarta suka yi ba, ba ta san mene ne so ba balle kuma kishi, abin da ta sani kawai ta damu da Umar, a halin yanzu babu abin da take buƙata sama da ta ƙara jin muryarsa, ta ji shi a kusa da ita yana yi mata hira, ta ji daddaɗan ƙamshinsa gami da dariyarsa mai sa ta ji sanyi a cikin ranta. Gocewa ta yi ta kwanta a gurin saboda jin kanta ya fara juya mata. Wani irin haushin Haulatu ta ji ya cika mata zuciya, tsaki ta ja a fili ba tare da ta san ta yi hakan ba. Inna dake lura da yanayin da take ciki ta miƙe don cigaba da haɗa musu kayansu, don gobe asubanci za su yi zuwa Kano.
Kamar a mafarki wayar da Umar ya bar musu ta fara ringing, wata irin zabura A'isha ta yi ta fara laluben wayar dake gefen ta, jikinta har rawa yake saboda tsabar zaÆ™uwa da zumuÉ—in jin muryarsa da take........âœï¸
*💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖
_By_
_Zeey Kumurya_
*ELEGANT ONLINE WRITER'S*
*1ï¸âƒ£8ï¸âƒ£*
Ta yi nasarar lalubo wayar ta riƙe a hannunta, ajiyar zuciya ta saki mai ƙarfi tare da faɗin. "Inna ana kira ki zo ki ɗaga kar ta katse." Karɓar wayar Inna ta yi da niyyar ɗagawa, kafin ta ɗaga wayar ta saka Battery shutdown ta ɗauke.
"Yawwa, ba ni in kin É—aga."
A'isha ta faÉ—i haka tana yawo da hannunta a cikin iska tamkar za ta cafki babu.
A sanyaye Inna ta ce. "Ban kai ga ɗagawa ba ta mutu, ina ji chaji ne ya ƙare." A gigice A'isha ta ce. "Innalillahi! kunna dai mu gani ko batir ɗin ne ya goce." Inna ba ta yi musu ba ta kunna wayar, ƙara mutuwa wayar ta yi alamun dai babu chajin. Cikin damuwa na ganin samu da rashi A'isha ta miƙe tana faɗin. "Bari na kai ta wurin chaji."
"Idan kina ganin hanya ba, mene haka ne wai A'isha kike yi? Duk kin bi kin gigice saboda an kira waya, shi ne ma ko ba shi ba ne wanda kike ta ƙulafucin kiran nasa oho? Kin ga A'isha ki raba kan ki da abin da ya fi ƙarfin ki, ki cire damuwar yaron nan daga ranki."
Komawa ta yi ta zauna tare da saka kuka, cikin raunin murya ta ce. "Inna shi kaɗai ne fa wanda ya so mu a cikin garin nan bayan Innar Ma'u, shi ne abokin hirata, tunda ya tafi na koma halin zaman kaɗaici, idan na damu da kiran shi laifi ne? Idan kuma laifi ne ki yi haƙuri na daina." Wani irin sanyi jikin Inna ya yi, tausayin A'isha ya cika mata zuciya. Tabbas idan kana cikin hali na ƙunci da kaɗaici ka samu mai ɗebe maka kewa, lokaci ɗaya kuma ya tafi dole ka damu. Cikin kwantar da murya ta ce. "Ko kaɗan abin da kika yi ba laifi ba ne, kawai dai ina so ki rage damuwar da kika saka a ranki ne, kawo wayar yanzu na kai ta gurin caji, kar a kuma kira a ji a kashe." Share hawayen fuskarta ta yi ta miƙa mata wayar.
Sai bayan isha'i Inna ta je karɓo wayar, ta cewa mai cajin ya kunna ya duba gurin kira ya kira mata lambar da aka kira. Bayan ya duba ya ce. "Babu lamba ko ɗaya a gurin kira fa." Da mamaki Inna ta ce. "An kira fa tana ta ringing, kafin a ɗaga ta mutu babu chaji."
"Shi ya sa ba za a ga kiran ba, ai indai aka kira ba a É—aga ba har waya ta mutu a haka to kiran ba zai nuna ba."
"Yanzu kenan ba za a ga lambar da aka kira ba?"
"Eh." Ya ba ta amsa a tak'aice.
Zuciyar Inna babu daɗi ta karɓi wayar bayan ta biya shi kuɗin cajin ta koma gida.
Ihu ne kawai A'isha ba ta yi ba da Inna ta sanar mata ba a ga lambar da aka kira ba, amma ta sha kuka mara sauti. Washegari tun asubar fari suka shirya don tafiya, sai dai a karo na biyu Inna ta nemi kuɗi sama da ƙasa ta rasa, ga shi ba ta ko ficika da ya yi saura, gabaɗaya kuɗaɗen hannunta ta haɗe guri ɗaya ta ajiye a tare.