← Book details Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 55

Sashe 45

Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Gyara gurin da suka ci abincin Gwaggo ta yi ta kwanta ita ma dan ta rintsa. Shigowar Mommy ya sa ta tashi zaune tare da amsa sallamar da ta yi.
"Sannu da hutawa Gwaggo." Ta faɗa lokacin da take zama a kan carpet. Gwaggo ta ce. "Yawwa, ki ƙaraso bakin gado ki zauna mana Hajiyar birni, ai ba girmanki ba ne zaman ƙasa." Duk da ta san Magana Gwaggo ta faɗa mata sai ta yi murmurshi, cikin son ganin plan ɗinta na farko da ta tsara ya yiyu ta ce. "Kina sama ai ba na zauna ba Gwaggo, nan ɗin ma ya yi, Ina yini? Ba mu Gaisa ba ma." Gwaggo ta ce. "Lafiya ƙalau." Gyara zama Mommy ta yi ta ce. "Gwaggo wata magana na zo miki da ita, wadda nake fatan ki fahimce ni da idon basira, shi Alhaji na yi masa bayani ya ƙi ganewa." Gwaggo ta ce. "Ina jin ki." Mommy ta ce. "Yawwa, akan yarinyar nan ne dama."
"Wacce yarinya?"
Zomo baki ta yi ta ce. "Wannan ta kwancen, ban san sunanta ba ne." Gwaggo ba ta kuma magana ba sai ido da ta zuba mata alamun tana sauraren ta. Hakan ya sa ta cigaba da magana da faɗin. "Akan riƙon ta da Alhaji ya ce zai yi ne, Gwaggo zamani fa ya canza, yanzu ba da ba ne mutane babu gaskiya a zuƙatansu, kar mu je mu ɗauko abin da zai zame mana alaƙaƙai a rayuwa, TSINTACCIYAR MAGE fa BA TA MAGE, ina tsoron kar mu je garin neman gira a rasa ido, saboda ɗan hakin da ka raina shi ke tsole maka ido." Gwaggo ta ce. "Ni duk wannan karin maganar da kika jero ban gane me kike nufi ba da inda kika dosa." Karyar da murya Mommy ta yi cikin ladabi ta ce. "Abin da nake nufi ki saka Alhaji ya mayar da Yarinyar nan inda ta fito su cigaba da riƙe ta. Idan ya so in ma ɗawainiyar ta zai ɗauka sai ya dinga kai kuɗi ana kula da ita, amma nan gidan ɗin ta bar shi kawai." Gwaggo ta ce "Mene hujjarki na son a mayar da ita?" Ƙara karyar da murya Mommy ta yi ta ce. "To Gwaggo mene amfanin riƙon nata? Yarinya ba ka san daga inda take ba kawai ka ce za ka riƙe ta, ba ka san mutum ce, aljana ce, mayya ce, wacce iri ce sai Allah." Shiru Gwaggo ta yi tana kallon Mommy kamar me nazari, a ranta kuwa mamakin halin Mommy da ba za ta taɓa canzawa take, ta yi zaton ta yi hankali ashe har yanzu ana jika. Numfashi ta sauke ta ce. "Maganar ki abar dubawa ce gaske, amma shi Sa'id ɗin kin masa duk wannan bayanin?" Cikin jin daɗin ganin Gwaggon ta karɓi maganarta ta ce. "Na masa, na nusar da shi iya yina amma ya toshe kunnuwansa ya ƙi saurare na, saboda ba maganar shafaffiya da mai ba ce, saboda duk abin da ta ce masa ba ya musu yake yi."
"A'a, kar kuma ki ce haka, ke ma kin san Sa'id tsayayyen mutum ne da ƙafafunsa, ba irin mutanen da ake juya su ba ne, duk abin da kika ga ya yi shi ya saka kansa."
"Uhm Gwaggo kenan, don ba a gidan kike ba ne shi ya sa, amma ƙiri-ƙiri Alhaji yake nuna mana banbanci, yau fa kina gani girkina ne amma shi ya kai ta gurin aiki, ga ƴaƴanta ga driver duk ba za su kai ta ba sai shi? Kuma ita ma ta iya tuƙin nan, idan mota ce ga su nan burjik a gidan sai ta zaɓi wadda za ta hau." Gwaggo ta ce. "To shi ne me don ya kai ta gurin aiki ranar girkinki? Ke sau nawa yake fita da ke ranar girkinta?" Ɓata fuska Mommy ta yi ta ce. "Shikenan Gwaggo a bar maganar, mu dawo kan wadda muke yi, don Allah ki yi masa magana ya mayar da yarinyar, ke kaɗai ce za ki faɗa masa ya bi." Taɓe baki Gwaggo ta yi ta ce. "Idan ya ƙi ba sai a bar shi ba tunda gidansa ne kuma shi ya ga zai iya."
"Gidansa kuma?" Mommy ta tambaya kamar Gwaggon ta yi ƙarya. Kama haɓa Gwaggo ta yi tana girgiza kai ta ce. "Eh gidansa na ce, ko ba nasa ba ne? Daga an yi magana ki dinga gidan ɗanki gidan ɗanki. Tunda ya ɗauka ya ba shi ba shikenan ba? Kuma ban da rashin kunya don SAFWAN ya ba wa mahaifinsa gida sai ya zama abin magana? Kafin ya girma ya samu arziƙin a gidan wa ya rayu? Wa ya biya masa kuɗin da ya yi karatu har wata ƙasar ya samu aikin da ya yi kuɗin? Duk ba mahaifin nasa ba ne? Kuma kar ki manta da ƙyar Sa'id ya yarda ya dawo gidan nan da zama, sai da na saka baki na ce ba a yi wa yara haka idan sun yi gwaninta, hakan yana kashe musu gwiwa, sannan fa ya amince. A yanzu Safwan ya ce ya bar masa gidansa yana da gidaje ba ma ɗaya ba da zai zauna. Amma kin bi kin ishi mutane da gida na ɗanki ne, kullum cikin yi wa kishiya gori kina cewa albarkacinki take ci tunda tana rayuwa a gidan ɗanki, daga an yi magana ki dinga ɗaga hanci ke a dole ga uwar attajiri. Ban da shirme ma irin naki ai wannan abin alfahari ne a gare ki ɗanki yana kyautata wa mahaifinsa, amma kin mayar da hakan abin gori da izgili."
"Ni fa ban ce komai ba Gwaggo."
"Za ma ki ce ne, ai ba yau na fara sanin halinki ba." Gwaggo ta faɗa a harzuƙe. Cike da haushin maganganun Gwaggo Mommy ta tashi ta fice daga ɗakin fuuu. Gwaggo ta raka ta da harara tana faɗin. "Ka ga mace har mace, wuya da kunne da hannu sun sha zinare kamar mai hankali, amma tunanin ta na marasa lissafi ne." Ta ja tsaki tare da faɗin. "Allah ya shirya."

A fusace Mommy ta ƙarasa part ɗinta, ɗaya daga cikin masu aikinta tana mopping kawai ta ji ta ɗauke ta da mari. Dafe kuncinta ta yi cikin gigita tare da tsugunnawa ƙasa ta shiga ba ta haƙuri, duk da ba ta san lefin da ta yi ba.
"Don matsiyacin Ubanki Uwar me kika tsaya yi har yanzu ba ki gama mopping ɗin ba? Me ya sa ku matsiyata komai za ku yi sai kun nuna ƙaranta da tsiya?"
Jikin yarinyar na rawa tana hawaye ta ce. "Ki yi haƙuri don Allah Hajiy....."
"Dalla rufe mini ruɓaɓɓen bakin nan kafin na fasa shi." Mommy ta katse ta cikin tsawa tare da hamɓarin ta. Saurin ja baya ta yi tana haɗe hannayenta alamun roƙo. Ƙwafa Mommy ta yi tare da faɗin. "Ban da ƙaddara me zai haɗa ka zama guri ɗaya da talaka? Shi da duk inda yake naso yake kamar funfuna." Ta ƙarashe maganar tare da hayewa upstairs. Ajiyar zuciya mai aikin ta sauke ta cigaba da abin da take cikin sauri, jikinta har rawa yake saboda tsoron kar ta sakko ta tarar da ita ta ƙara yi mata wata sabuwar tijarar.

Mommy na tsaye a bedroom ɗinta da waya kare kunnanta, after some seconds ta ce. "Kina ji na Kaltum, na je gurin tsohuwar can na faɗa mata kamar yadda kika ce, amma matar nan ta ƙi amincewa, sai ma wasu maganganu da ta bi ni da su, kin san shegiyar tsohuwa ce mai kankanbar tsiya. Da farko fa kamar ta amince, amma ina taɓo wadda suka fi k'auna ta canza akala" Daga ɗaya ɓangaren Kaltum ta ce. "Duk ki ƙyale ƴan abu ta kazar uba Saratu, ki ba ni 1 hour gani nan zuwa gidan, wallahi shirin da zan zo da shi sai yarinyar nan ta bar gidan, kin san halina idan na ce zan yi abu sai na yi." Ajiyar zuciya Mommy ta sauke, sanin hatsabibanci da ƙwarewa a shaiɗananci na ƙanwar tata ya sa ta yi amanna da zancenta, ta saka a ranta kawai matsalarta ta kau, indai barin A'isha daga gidan ne tamkar an yi an gama. Murmushi ta saki tare da faɗin. "Sai kin zo ɗin.".........✍️
*💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖

*_Zeey Kumurya_*

*ELEGANT ONLINE WRITER'S*

*2️⃣7️⃣*
Chapter 45 · 0% Book details