Sashe 37
Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yau Juma'a ranar da su Yawale suka saka ta ɗaurin Auren A'isha da tsoho makaho. Tun cikin dare A'isha take kuka har gari ya waye ba ta yi shiru ba. Inna da gabanta ke ta faɗuwa ta dube ta, ta ce. "Don Allah ki bar kukan nan haka, sai kanki ya yi ciwo ko kin janyo wa kanki wata cutar, dama ba ki gama farfaɗowa ba." Cikin sheshshek'a ta ce. "Ni ba na son Auren nan, don Allah Inna mu gudu mu bar garin nan." Hawaye Inna ta matse ta ce. "Tabbas in har Yawale bai janye maganar auren nan ba to kuwa lokaci ya yi da zan bar garin nan dole." Ajiyar zuciya A'isha ta sauke mai ƙarfi ta ce. "Mu tashi mu tafi Inna, kin san ma ba janyewa zai yi ba ma, kamar yadda ya faɗa ana saukowa daga masallaci za su ɗaur......"
"Wacce irin sabgar tsiya da bayar da kai ce wannan Asabe kike yi haka?"
Muryar Malam da ya shigo kamar an hankaɗo shi yana baza babbar riga ta karaɗe zagayen cikin amsa amo. Da mamaki Inna take duban shi cikin alamun tambaya. Cigaba da ya yi da magana cikin ɗaga murya. "Wanne irin abu ne wannan? Yau kusan sati da cewa a je a yi jere amma kin ƙi siyo kaya ki bayar har yau ranar ɗaurin Aure? Ko a ƙasa kike son su ci amarcin ne? Wannan ai halin matsiyata ne da nuna tsiya." Miƙewa Inna ta yi ba ta ce komai ba, don ba ta da lokacin ɓaɓatu da mutumin da take masa uzurin ciwon hauka, ko ƙara kallon inda yake ba ta yi ba ta shige ɗaki.
"Wato ga mahaukaci ina magana kin mini shiru kin shige ɗaki ko? To wallahi ko me za ki yi sai an ɗaura auren nan yau, sai dai baƙin ciki ya kashe ki." Ya ƙarashe maganar tare da wurga wa A'isha wani mugun kallo. Hamɓarin ta ya yi da ƙafa ya juya ya fita. Yana tafe yana cigaba da banbanmin faɗa shi kaɗai, gidan tsoho Makaho zai je ya ba shi haƙuri akan rashin zuwa jeren, ya kuma tabbatar masa zai tursasa Asabe dole ta bayar a siyo ko da katifa ne, don tsohon ya ce masa ba zai angonce a dandaryar ƙasa ba. Jiniyar da ya ji ya sa shi tsayawa a ƙofar gida yana kallon Motar police dake tahowa.
Officer gashi nan ma."
Faisal dake fitowa daga cikin Motar ya faÉ—a tare da nuna Yawale. Zaro ido ya yi cikin tsoro ya ce. "Kai É—an samari me na yi kake nuna ni?"
"Idan muka je office za ka ji, shiga Mota mu ƙarasa."
Cewar wani police cikin haÉ—e rai.
Yawale zai kuma magana aka daka masa tsawa, dole ya shiga Motar ƙirjinsa na dukan uku-uku, sai rantse-rantse yake akan bai aikata laifin komai ba, Auren ƴa ma zai yi yau. Bayan tafiyar su ba jimawa labari ya karaɗe unguwa da gidansu A'isha ƴan doka sun zo sun tafi da Yawale a Mota.
Bayan sun ƙarasa station wani ɗansanda ya dubi Yawale tare da nuna Faisal da hannu ya ce. "Wannan Malamin su wata yarinya ne A'isha dake gidanku, ya kawo ƙarar ka akan kana shirin yi mata Auren dole saboda mahaifinta ya rasu, haka ne ko ba haka ba ne?" Gumi ne ya shiga tsatstsafo wa Yawale, cikin rarraba idanu ya ce. "Ranka ya daɗe ba Auren dole ba ne, tana so yarinyar, ita ta kawo mijin ma da kanta." Wani mugun kallo Faisal ya wurga masa bai ce komai ba.
"Mahaifiyar yarinyar da bakinta ta shaida wa Faisal ba sa son Auren, sanadin maganar auren har ciwo yarinyar ta kwanta, amma tunda ka ce haka mu je gidan mu zanta da su mu ji gaskiyar al'amari, wallahi idan suka tabbatar mana Auren dole ne sai ka yi kwanan cell, saboda wahalar da shari'a da ka yi."
"A yi haƙuri ranka ya daɗe zan faɗi gaskiya, wallahi ba sa so, amma ka mini rai kar ka kulle ni."
Yawale ya faÉ—a cikin tashin hankali.
"Shikenan ka wanke kanka, yanzu za mu je mu taho da uwar yarinyar a yi yarjejeniya akan ba za ka ƙara shiga cikin rayuwarsu ba, sannan kuma maganar Auren nan an rushe ta."
"FaÉ—a taka cikawa tawa, duk abin da ka ce haka za a yi ranka ya daÉ—e."
Inna tana cikin haɗa kaya wata mace ta je ta tafi da su, cike da zullumi da fargaba suka je, amma da suka ji dalilin kiran sai farin ciki ya lulluɓe su. Bayan ƙara tattaunawa aka yi musu iyaka da Yawale, kowa ya yi signing aka ce su tafi. Yawale kamar zai zura da gudu saboda saurin da yake zubawa don ya yi ya bar gurin, sakamakon kaɗawar da cikinsa ya yi yana buƙatar zagayawa masai. Tsabar farinciki Inna har da ƙwalla, ji take tamkar an yaye mata dukkan damuwarta. A'isha kuwa tamkar ta taka rawa haka take ji don murna.
"Na gode, na gode sosai ɗana da wannan taimakon naka, Allah ya biya ka ya fi mu yabawa." Murmushi ya yi idanunsa a kan A'isha ya ce. "Ba komai Mama, Allah ya kiyaye gaba." Kan A'isha a ƙasa ta ce. "Mun gode sosai Sir." Still yana murmushi ya ce. "Babu komai A'i." Ya rasa me ya sa tun ranar farko da ya fara ganin ta tausayin ta ya cika masa zuciya, ko don makauniya ce ita? Babur ya samu suka hau ya biya kuɗin aka mayar da su gida.
Labarin fasa auren A'isha da tsoho ranar shi ya yi ta yawo a cikin garin, kowa na tofa albarkacin bakinsa. Iya da sauran mutanen gidan kuwa baƙinciki da takaici kamar su kashe su, suka dinga cewa kamar yadda Inna ta lashe kurwar Umar haka ta lashe ta Faisal, shi ya sa ya tsaya musu har aka fasa Auren. Bangaren Tsoho da Yawale kuwa faɗa ne ya kaure, tsoho ya ce sai ya biya shi duk kuɗaɗen da ya dinga ba shi akan auren, Yawale kuma ya ce ya cinye ba zai biya ba, ai ba shi ya ce ba shi ba. Rigima har gaban wazirin Sarki, da ƙyar aka yiwa tufkar hanci da cewa Yawale ya biya rabin kuɗin da Tsoho ya ba shi, sun raba asara kenan.
A ranar Iya ta zo ta É—auke kayan lefen da aka kawo, wanda ya yi ta walagigi a tsakar gida, don tun ranar da aka kawo Inna ba ta É—auke su daga gurin da aka ajiye su ba. Da yamma ganin Inna ba ta da niyyar ta ce su tafi ya sa cikin karaya A'isha ta ce masa. "Inna ba za mu tafin ba ne? Kar dare ya yi fa."
"Tunda an fasa auren maganar barin mu garin nan ta rushe ita ma."
"Amma Inna...."
Ɗaga mata hannu ta yi tare da faɗin. "Ki bi abin da na ce kawai, tunda kika ga na ƙi barin garin nan akwai dalili, amma na san watarana dole mu bar shi, lokaci kawai nake jira." A'isha ba ta kuma magana ba, amma cikin ranta ba ta so hakan ba, don zaman garin gabaɗaya ya fice mata aka, duk da a nan ta buɗi ido ta gan ta.
Washegari kamar daga sama sai ga Innar Ma'u ta sauka a garin da safe. Tsabar murna rasa inda Inna za ta saka ta, ta yi. Bayan sun gaisa Inna ta kawo mata ruwa da abinci ta ce. "A'isha haka kika ƙara girma? Yanzu ai kin fi Ma'u komai da komai." Cikin murmushi Inna ta ce. "Ni ma har mamakin girman da take nake yi, lokaci ɗaya kuma ta yi wannan girman, don ma ta yi ciwo kwana biyu ta yi rama, kafin ta yi ciwon ai ta fi haka." Innar Ma'u ta ce. "Masha Allahu, haka ake so. Ya fuska? Har yanzu idon dai bai buɗe ba?" A raunane Inna ta ce. "Muna nan muna ta addu'a dai."
"To Allah ya amsa, ya ba ta lafiya."
"Amin."
A'isha ta ce "Inna me ya sa ba ki zo da Ma'u ba?"
"Tana tahfiz ne, amma ita ma ta so mu zo tare, makarantar ce suna da tsauri ba sa son fashi, amma idan suka yi hutu ko ita kaÉ—ai ce zan sako ta a Mota ta zo ta kwanar muku biyu."
"Allah ya kai mu."
Bayan sun taɓa hira Innar Ma'u ta tashi ta shiga cikin gidan don su gaggaisa da sauran matan gidan, saboda a ranar za ta koma Kano. Kafin ta tafi take sanar da Inna ta zo ta haɗa ta da wani mutum da suke turo masa da kaya yake sayarwa anan wani ƙauye Luran dake gaba da su, kayan za su dinga sauka a gurin Inna, shi kuma zai dinga zuwa yana ɗauka, idan ya sayar ya kawo mata kuɗin, a ciki ita ma sai ta dinga ɗaukar nata percentage ɗin. Da da wani mutumi suke haka, yanzu kuma ya rasu, shi ne Innar Ma'u ta cewa ƙaninta kawai su dinga ba wa Inna, ta san za ta riƙe musu amana, kuma hakan zai taimaka mata matuƙa da samun ɗan na kashewa. Ba ƙaramin farinciki Inna ta yi da jin wannan labarin ba, ta ƙara tabbatarwa idan aka ce mutum masoyinka ne mai son cigaban ka har abada hakan take, ta dinga yi wa Innar Ma'u godiya har da hawayen farinciki. Bayan kwana biyu da zuwan Innar Ma'u aka turo kayan.
*One Year later*