Sashe 54
Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tunda Ihsan ta saka ta a mota ta sunkuyar da kanta ba ta ɗago ba, shi kuwa dama ko kallon inda take bai yi ba, driving ɗinsa kawai yake. Lokaci zuwa lokaci yana duba wayarsa da kira ke shigowa ba ƙaƙƙautawa.
Tsaki Salma ta ja karo na babu adadi ta dubi Baby da za su fita tare ta ce. "Wai ina Mine ya shiga ne? Ina ta kiran shi ya Æ™i É—auka, kuma ya san zai kai ni unguwa yanzu, na faÉ—a masa fa." Baby ta ce. "May be driving yake shi ya sa bai É—aga ba." A fusace ta ce. "Amma ai ko parking sai ya yi ya É—aga kira na, idan mun gama wayar ya cigaba." Kallon mamaki Baby ta mata, a ranta tana faÉ—in. "Sannu Mommy." Amma a fili ba ta yi magana ba, sanin halin masifar Salman sai ta huce a kanta. Ganin har biyar ta wuce bai dawo ba bai kuma É—aga kiran ta ba ya sa ta miÆ™ewa a Æ™ufule ta nufi parking space da nufin ta tafi kawai a motarta, ta gaji da jira, kuma ta san zuwa yanzu an kusa gama birthday É—in da za ta. Amma fa ranta ba Æ™aramin É“aci ya yi ba, saboda ta gama cin burin Safwan ne zai kai ta, ya buÉ—e mata mota a gaban Æ™awayenta, ta nuna musu yanzu a tafin hannunta yake. Tana Æ™arasawa parking space É—in motarsa na shigowa, ko bari ya gama parking ba ta yi ba ta nufi inda suke a fusace tare da saka hannu ta kama murfin motar na front seat.........âœï¸
*💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖
*_Zeey Kumurya_*
*ELEGANT ONLINE WRITER'S*
*3ï¸âƒ£2ï¸âƒ£*
"Aunty Salma." Baby dake bin ta a baya ta kira sunanta.
Tsayawa ta yi tare da juyawa ba tare da ta buÉ—e motar ba.
"Mene ne?" Ta faÉ—a a zafafe.
Baby ta ce. "Stain na ga kin yi, kuma na san ba ki sani ba." Cikin takaici ta ce. "What?" Tare da fara dudduba jikinta. Tsaki ta ja ganin yadda jikinta ya ɓaci da jini ta gurin zama. Kamar za ta fashe da kuka ta juya ta koma ciki, bin bayanta Baby ta yi don ita ta yanke ta ma fasa fitar.
Ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ya sauke wadda ta sa A'isha ɗagowa da sauri ta kalli saitin da yake kamar mai ganin shi. Ƙura mata ido ya yi na wasu sakanni sannan ya sauke numfashi, lokaci ɗaya kuma ya haɗe rai. Jan motar ya yi ya ƙarasa har kusa da part ɗin su Ummi. Ba tare ya yi magana ya fita ya buɗe ɓarin da take. Duk da bai yi magana ba amma motsin buɗe ƙofar ya sa ta yunƙurawa ta fito tana laluben hanya da hannunta. Mayar da ƙofar ya yi ya rufe. A hankali ta ce. "Na gode." Ko kallon ta bai yi ba ya koma cikin motar ya bar ta da zullumin yadda za ta iya shiga ciki. Daidai lokacin Lubna ƴar Hajiya Zainab ta fito daga ciki. Da mamaki ta ce. "Nana dana ina na gan ki ke kaɗai?" Cikin jin daɗi ta ce. "Ba ni kaɗai ba ce, yanzu aka sauke ni." Kallon motar Lubna ta yi ta ƙaraso ta kama hannunta suka shiga ciki. Da mamaki Ummi ke Kallon su har suka zauna. Tana duban A'isha ta ce "Wa ya dawo da ke? Yanzu nake ƙoƙarin kiran Khalifa na ce masa ya biya ya ɗauko ki." A'isha ta ce. "Wanda ya kai mu ne." Cikin ɗaurewar kai Ummi ta ce. "Safwan?" Gyaɗa mata kai ta yi.
Ummi ta ce. "Ikon Allah, to an gode masa."
Tana saka wani kayan ya shiga ɗakin. Murya ƙasa-ƙasa ya yi sallama. Wani kallo ta wurga masa mai haɗe da harara, ba tare da ta amsa masa sallamar ba ta ce. "Ina ka je?" Cikin danne tsoron da yake ransa ya ce. "Abba ne ya aike ni, kafin na ƙarasa inda zan je muka samu accident na buge wasu." Ɗauke idonta ta yi daga kansa ta ce. "Daga nan kuma sai yaya?"
"Hospital na kai su aka yi musu duk abin da ya dace, lokacin da kikkira wayar tana mota na bar ta a ciki." Cikin gamsuwa ta ce. "Amma da ka kai su Hospital É—inka yaranka sun kula da su ai, tunda ka san you keep me waiting."
"I'm sorry." Ya faÉ—a cikin sauke ajiyar zuciya tare da hugging É—inta.
Da daddare Ummi ta kama hannun A'isha zuwa part ɗin Abba. Yana zaune shi kaɗai a parlonsa yana karatun Alkur'ani suka shiga. Bayan ya kai aya ya amsa musu sallamar da suka yi. Ummi ta ce. "Barka da dare Abba." Ya ce. "Yawwa DR." Cikin ladabi ita ma A'isha ta gaishe shi, ya amsa cikin kulawa da fara'a. Bayan Ummi ta faɗa masa yadda suka yi a asibiti ya ce. "Masha Allahu, Ubangiji ya sa a yi aikin a sa'a, gobe idan Allah ya kai mu sai mu je a biya kuɗin." Ummi ta ce. "Allah ya nufa ya saka da Alkhairi." Abba ya amsa da "Amin." A'isha da ta rasa kalmomin da za ta yi amfani da su ta gode wa waɗannan mutanen masu karamci, mutunci da tausayi ta ce. "Na gode sosai Abba, Allah ya ji ƙan mahaifa ya saka da gidan Aljanna." Cikin murmushi ya ce. "Amin amin daughter, Allah ya yi miki albarka ya ba ki lafiya." Suka amsa da Amin gabaɗaya. Gyara zama Ummi ta yi ta ce. "Ɗazu principle ɗin su Muneefah ta kira ni wai ba ta da lafiya a je ɗauko ta." Abba ya ce. "Subhanallahi, Allah ya kai mu gobe sai Khalifa ya je ya ɗauko ta, Allah ya sa jikin ba tsanani ya yi ba sosai." Ummi ta ce. "Muneefah ce fa, za ta iya kwanciya ciwon ƙarya ma, ka san ta tsani makarantar nan kamar mutuwarta." Abba ya ce. "A'a fa, autata ba za ta yi haka ba." Ummi ta ce. "Toh shikenan Allah ya kai mu goben ka gani." Kafin Abba ya ƙara magana Safwan da Salma sun shigo, wadda ke tafiya cikin taƙama tamkar basarakiya. Kan dole ba don son ranta ba ta zauna a ƙasa. Ba yabo ba fallasa ta gaishe da Abba, Ummi kuwa kamar an mata dole.
Abba yana duban Safwan ya ce. "Gobe za ka je Gomben ko?" GyaÉ—a masa kai ya yi. Ummi ta yi murmurshi ta ce. "Za a je gaishe da Gwaggo kenan?" Ya ce. "Eh, tunda ta ce sai dai ni na je ita ba za ta zo ta mini sannu da zuwa ba." Ummi ta ce. "Gwaggo kenan, idan ka je ka gaishe ta da kyau." Ya ce "Za ta ji in sha Allah."
Tunda Salma ta zauna idanunta na kan A'isha, ita ta manta da Yarinyar ma gabaɗaya sai yau da ta gan ta. Bayan sun fita ta biya part ɗin Mommy take tambayar ta wacece A'isha a gidan? Mommy ta ce. "Au Khaltum ba ta faɗa miki ba? Na ɗauka da kika je ai ta miki bayani." Salma ta ce. "ko ɗaya, ai ba mu taɓa zancen yarinyar da ita ba." Taɓe baki Mommy ta yi ta ce. "Wai daga Alhaji ya kaɗe su ita da uwarta uwar ta mutu shikenan ya ce zai riƙe ta saboda rashin sanin ciwon kai, mutum ce aljana ce mayya ce sai Allah." Salma ta ce. "Ban gane ba, wai yana nufin shikenan a gidan za ta cigaba da rayuwa?" Mommy ta ce. "Eh mana, na nusar da shi illar hakan amma ya ƙi ganewa, wai shi Sarkin taimako." Cikin haƙiƙancewa Salma ta ce. "Idan taimakon ta zai yi ya kai ta orphanage mana ko police station a yi cikiyar iyayenta idan ba ta san inda suke ba, ni fa farko da na gan ta I thought ƴar'uwar waccan matar ce, ashe ma tsinto aka yi daga sama a titi. To gaskiya ba zai yiyu ba, babu yadda za a yi mu yi rayuwa da wata bare a gida ɗaya, dole a san abin yi yarinyar nan ta bar gidan nan." Mommy ta ce. "Ƙoƙarin da nake ta yi kenan." Salma ta ce. "Better, don ba zan yarda Mijina yana ganin wata mace ba bayan siblings ɗinsa ba." Mommy ta bi ta da kallo kawai ba ta ce komai ba.
Washegari da safe A'isha na zaune ita kaɗai a parlour tana karyawa Khalifa ya shigo. Bayan ya yi sallama ya zauna a kusa da ita. Cikin sanyinta ta ce. "Ina kwana?" Ya ce. "Lafiya ƙalau, 2 days ba mu haɗu ba ko cikiya ta ba kya yi ko?" Ta ce. "Na tambayi Ummi ta ce kana gurin aiki." Cikin murmushi ya ce. "Dagaske?" Ta gyaɗa masa kai. Ya ce. "Ya jikin naki? I hope dai yanzu kin warware?" Ta ce. "Eh Alhamdulillah." Ya ce. "Ina Ummi?" Ta ce. "Tana kitchen." Miƙewa ya yi ya shiga kitchen ɗin. Bayan sun gaisa Ummi ta ce. "Abba ya faɗa maka za ka je ka ɗauko Muneefah ko?" Ya ce. "Eh, amma sai na je office na yi abu daga nan zan wuce." Ummi ta ce. "Toh shikenan Allah ya kiyaye." Ya amsa da Amin sannan ya dawo parlour'n. Ummi ta biyo shi da breakfast ɗinsa. Bayan ya gama ci ya dubi A'isha ya ce. "Zan fita, me kike son na taho miki da shi?" Shiru ta yi kamar mai nazari. Ya ce "Yau fa sai kin faɗa mini duk zamiyar ki." Murmushi ta yi ta ce. "Komai ma, amma abin zaƙi." Ya ce. "Shikenan shazumama, sai na dawo."
"Allah ya tsare." Ta faÉ—a idonta a kan direction É—in inda take jiyo muryarsa.