← Book details Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 55

Sashe 14

Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

..........Washegari tun sassafe suka shirya, A'isha tana zaune tana karyawa, Inna kuma tana duban kuɗin da za su yi amfani da shi a inda ta ajiye jiya da daddare amma kuɗi ya ce ɗauke ni inda kika ajiye. A cikin wata jaka dama ta ajiye su, ta duba jakar ya fi sau goma ta zazzage ta amma ba ta ga kuɗin ba. Wasu guraren ta shiga dubawa ko ta manta ta canza musu guri ne, sai da ta birkice duka ɗakin amma ba ta gan su ba. A'isha da take sauraren b'uruntun da Inna take ta yi ta ce. "Inna wai me kike dubawa tun ɗazu?" Cikin damuwa Inna ta ce. "Kuɗin da zan kai ki asibitin A'isha, ban gan su ba." A'isha ta ce. "Ko dai kin manta inda kika ajiye ne?" Inna ta ce. "Amma ko mantawar na yi yanda na birkice ɗakin nan ya ci ace na gan su, sai dai in ba ya cikin ɗakin." A'isha ta ce. "Allah yasa dai ki gan su Inna." Inna ta ce. "Amin." Dai-dai nan innar Ma'u ta shigo zagayen nasu, bayan ta yi sallama sun amsa mata ta ɗaga labulen ɗakin tana faɗin. "Har yanzu ba ku tafi ba? Idan takwas ta wuce fa ba za ku samu ganin likita ba." Inna dake maimaita kalmar innalillahi a cikin zuciyarta ta dubi Innar Ma'u cikin sanyin murya ta ce. "Ladidi kuɗaɗen na nema na rasa." Innar Ma'u ta ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, kamar ya kin neme su kin rasa? A ina kika ajiye?" Inna ta ɗauko jakar da ta ajiye kuɗin ta ce. "A cikin jakar nan na saka, kuma ko kafin na yi bacci na duba na ga suna ciki, Jakar kuma a gabana ta kwana a k'ark'ashin shimfid'ata." Innar Ma'u ta ce. "Bari dai na shigo mu ƙara duba ɗakin sosai, ko wani gurin kika cilla su kika manta." Inna ba ta ce komai ba har Innar Ma'u ta ƙaraso cikin ɗakin ta fara dubawa. A'isha dake ta murna yau za'a kai ta asibiti a yi mata magani sai murnar ta koma ciki, kana kallon fuskarta ka san tana cikin damuwa. Sai da innar Ma'u ta ƙara duba ko'ina a cikin ɗakin amma babu kuɗin babu alamar su. Hankalin Inna fa ya yi matuƙar tashi, baiwar Allah har gumi ya fara tsatstsafowa a jikinta na rud'ani. Duban Innar Ma'u ta yi wadda ita ma take cike da tararrabin abun ta ce. "Kuɗin nan fa ba ya cikin ɗakin nan." Innar Ma'u ta ce. "An shigo an ɗauke su kenan?" Inna ta ce. "Amma da na yi matuƙar mamaki, saboda babu yanda za'a yi a ɗaga shimfid'ar da nake kwance har a zare jakar nan ban ji na farka ba." Innar Ma'u ta ce. "Hmmm, Asabe bar mutum kawai, maso abun ka ya fi ka dabara, amma ko tantanma bana yi in dai shigowa aka yi aka ɗauki kuɗin nan to da sandar nan da suke amfani da ita suka zo, wadda idan aka ajiye ko idonka biyu baza ka iya motsawa ba har sai sun gama ɗaukar abun da za su ɗauka sun ɗauke ta." Inna ta sauke numfashi tare da zama dab'as a ƙasa cikin raunin murya ta ce. "Allah kai ka san me kake nufi da wannan al'amari, kuma kai ka bani wannan kuɗin Allah ka ƙara bani wasu." Cikin tausayawa Innar Ma'u ta ce. "Amin ya Allah, insha Allahu Asabe kuɗin ki sai ya fito, Allah ya dawo miki da su, ya toni asirin duk wanda ya ɗauka." Kamar A'isha zata yi kuka ta ce. "Inna shikenan yanzu baza mu je asibitin ba an sace kuɗin?" Inna ta ce. "Ki yi hak'uri A'isha, haka Allah ya Ƙaddaro mana, babu yanda zamu yi." Tsugunnawa Innar Ma'u ta yi ta dafa kafadun A'isha cikin son kwantar mata da hankali ta ce. "Insha Allahu A'isha Ubangiji zai kawo hanyar da za'a kai ki asibiti, ki kwantar da hankalinki insha Allahu zaki warke." Gyaɗa mata kai kawai A'isha ta yi. miƙewa Innar Ma'u ta yi ta fice bayan ta ce musu tana zuwa. Hawaye ne yake ƙoƙarin zubowa daga idon Inna amma ta ƙi ba su damar hakan, wani irin zafi take ji a cikin zuciyarta, kuɗin da ta hana kanta ci, ta hana kanta sha, da goma da ishirin ta tara su kusan watanni goma amma wani mara imanin ya raba ta da su a dare ɗaya, ita yanzu ina ta ga hanyar da zata kuma samun wasu kuɗaɗen? Hawaye A'isha ta fara ta ce. "Yanzu shikenan Inna ni ban zan kuma gani ba tunda an sace kuɗin da zaki kai ni asibitin? Allah ya isanmu wallahi, ba mu yafe ba, Allah ya kumbura cikin duk wanda ya ɗaukar mana kuɗinmu." Inna ta ce. "In Allah ya yarda A'isha zaki warke." A'isha ta ce. "To Inna wa zai ƙara baki wani kuɗin ki kai Ni?" Inna ta ce. "Allah, shi ya bamu wannan ɗin kuma shi zai ƙara bamu wasu."

Wunin yau gaba-d'aya cikin damuwa da rashin walwala A'isha da Inna suka yi su, dan Inna ko abinci kasa ci ta yi. Abun da yake bata mamaki game da ɗaukar kuɗin da aka yi, ita dai a iya saninta babu wanda ya san da batun kuɗin kaf cikin gidan balle kuma a waje, daga ita sai Innar Ma'u suka sani, kuma ta san Innar Ma'u baza ta yiwa kowa zancen kuɗin ba, tunda ba wani shiga sabgar matan gidan take yi sosai ba. Amma babu komai ta bar wa Allah, shi kaɗai ya san me yake nufi da hakan ta faru, fatanta Allah ya musanya musu da mafi Alkhairi. Innar Ma'u ta yi iyarka ƙoƙarinta wajen ganin ta samu kuɗi ta bawa Inna ta je asibiti a cikin satin amma hakan bai samu ba saboda halin rayuwa. Haka A'isha ta cigaba da rayuwa cikin makanta, ga tsangwama da tsanar da suke fuskanta daga mutanen garin, babu abun da ya ragu sai ma ƙaruwa da ya yi.
Chapter 14 · 0% Book details