Sashe 31
Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
..........Yana zuwa ya tarar da Sarki da Ado driver zaune a soron gidan Sarki suna hira, an kawowa Ado driver ruwa da abinci. Zama ya yi suka gaisa da Ado driver cikin mutunta juna. Wajen ƙarfe sha biyu Umar ya koma gidansu A'isha, lokacin an gama zuba komai nasa a cikin Mota, sun yi sallama da su Sarki, tafiya kawai za su yi. A inda ya bar A'isha a nan ya tarar da ita a zaune ta yi tagumi, Inna na zaune a gefen ta ita ma duk jikinta a sanyaye. Bayan ya yi sallama sun amsa masa sai ya rasa mai zai ce, tsawon minti biyu yana tsaye ya dai daure cikin sanyin murya ya ce. "Mama za mu wuce." Inna ta miƙe ta ce. "To Allah ya kiyaye ya kai ku lafiya, ga kayan ba ka ɗiba ba kuma." Idanunsa akan A'isha ya ce. "Idan zan fita zan tafi da su, an gode sosai Allah ya saka da Alkhairi." Inna ta ce. "Mu ne da godiya Umar, ka yi mana abun da babu wanda ya taɓa yi mana kamar shi a cikin rayuwarmu, ka taimake mu a lokacin da muke tsananin buƙatar neman taimako, Allah Ubangiji ya biya ka, ya raba ka da iyayenka da duniya da mutanen cikinta lafiya, Allah ya saka maka da gidan Aljannah ya baka mace ta gari." Ya ce. "Ameen." Tare da zaro waya keypad daga cikin aljihunsa ya miƙawa Inna ya ce. "Mama ga ƙaramar wayata nan akwai sim a ciki, insha Allahu idan mun ƙarasa zan kira ku ta cikinta." Inna ta ƙi karɓa ta ce. "A'a Umar, ka cigaba da amfani da abar ka, ya za'a yi ka bani wayarka?" Umar ya ce. "Bana wani amfani da ita sosai ne, dan Allah ki karɓa Mama kar ki ce a'a, akwai memory a ciki mai ɗauke da karatun Alqur'ani, sai ki dinga kunnawa Humairah tana saurara." Inna ta ɗan yi jim sannan ta saka hannu ta karɓa tare da yi masa godiya. Ganin yanda hankalinsa gaba-d'aya yake kan A'isha sai ta shiga ɗaki ta ba su guri. Tsugunnawa ya yi a daf da ita ya kama hannunta ya ce. "I'm sorry Humairah, ban san me zance miki da zaki fahimce ni ba, amma wallahi ba dan son raina zan tafi in bar ki ba." Ya ƙara damk'e hannunta sosai a cikin nasa ya ce. "Gida zan tafi gurin ahalina, amma duk watannin da na shafe ban gan su ba kewar ki da na fara ta saka ba na murna da d'okin ganin su, Please Humairah dan Allah kar ki saka kanki a cikin damuwa saboda tafiyata, zan dawo gare ki insha Allahu, ko dan na cika alƙawarin da na ɗaukarwa kaina na nema miki lafiya." Wani irin yanayi A'isha ta tsinci kanta a ciki wanda ba zai misaltu ba, duk saurin kukanta sai ta nemi ko d'igon hawaye ta rasa a idonta. A hankali ta kamo ɗayan hannunsa cikin magana daƙyar ta ce. "Dagaske tafiya zaka yi Yaya Umar? Ashe ba zan taɓa ganin ka ba a rayuwata? Dan Allah ka ce mun mafarki nake yi ba gaske ba ne zaka tafi ka bar ni." Kasa magana ya yi saboda yanda kalamanta suka gusar da guntun dauriyar da yake da ita. Cikin raunin murya ya ce. "Ki yi hak'uri, shine kawai abun da zan iya ce miki." Girgiza kai A'isha ta shiga yi ta fashe da wani marayan kuka mai karya zuciyar mai saurare, da sauri Inna ta fito daga ɗaki tana tambayar ba'asi. Hakan ya saka Umar zare hannunsa daga nata ya miƙe tsaye. K'afufuwansa A'isha ta rungume cikin matsanancin kuka ta ce. "Dan Allah Yaya Umar kar ka tafi ka bar ni!" Runtse idonsa ya yi cikin ƙoƙarin mayar da ƙwallar da ta tarar masa a ido, zuciyarsa na yi masa wani irin zafi da k'una. Inna ce ta zo ta janye A'isha daga jikinsa, cikin rarrashi ta ce. "Mene haka A'isha? Wannan wanne irin kuka ne? So kike ki karya masa zuciya zai tafi ya ga ahalinsa ya fasa saboda ke? Ai dama ko mun daren dad'ewa kin san zai koma tunda ba'a nan yake ba." Kamar zai fashe da kukan shi ma ya zaro kuɗi ya ajiye a ƙasa yana duban Inna ya ce. "Mama dan Allah ki kai ta asibiti da wannan kuɗin a duba a ga abun da ya samu idanun nata, in ya so duk yanda ake ciki sai ki sanar mun ta waya." Inna ta ce. "A'a Umar ba za mu yi haka ba, gaskiya ba zan karɓi wannan kuɗin ba, d'awainiyar da ka yi da mu a baya ma ta isa, Allah ya saka da Alkhairi." Dafe kansa dake sara masa ya yi ya ce. "Dan girman Allah Mama ki yi hak'uri ki karɓa, idan kika ƙi karɓa ba zan ji daɗi ba." Inna ta ce. "Amma Umar......" Ya marairaice ya ce. "Dan Allah Mama." Inna ta ce. "Shikenan." Ta shiga yi masa godiya tare da kwararo masa tarin addu'oi. Idanunsa akan A'isha dake gunjin kuka ya ce. "Humairah zo ki ji." Inna ta zare ta daga jikinta ta ƙarasa ta ɗauki kayan da ta haɗa masa ganin ba ta su yake ba kar ya manta ta nufi ƙofar gida da su. Takawa ya yi zuwa inda Aisha take ya ɗago kanta yana kallon fuskarta dake jik'e da hawaye ya ce. "Please ki bar kukan nan Humairah, da kin san yadda nake ji a cikin zuciyata da ba za ki bar d'igon hawaye ya fito daga cikin idonki a gabana ba, na faɗa miki zan dawo nan kusa Insha Allahu." Tana sheshshek'a ta ce. "Ai na san ba dawowa zaka yi ba." Ya ce. "Zan dawo mana, amma idan kin daina kukan nan, idan baki daina ba ba zan dawo ba." Duk yanda kukan ke cin ta haka ta haɗiye shi ta daina jin abun da ya faɗa. Ajiyar zuciya ya sauke ya ɗauko handkerchief ɗinsa ya shiga share mata hawaye. K'uri ta yi masa idanunta a cikin nasa saboda kafen ta da ya yi da ido, wani numfashi ya sauke mai zafi ya shafi saman idanunta ya ce. "Allah ya baki lafiya My Humairah." Ba ta ce komai ba dan tana buɗe baki kuka ne zai biyo baya. Kama hannunta ya yi suka fita waje cikin yanayin damuwa. A bakin Mota ya tsaya ya ɗan rank'wafa ya kai bakinsa dai_dai kunnenta ya ce. "SAI WATA RANA HUMAIRAH! I will miss you so much." Wani kuka A'isha ta fashe da shi ta rungume shi, so take ta yi magana amma ta kasa. Hansai dake tsaye tana lek'en su ta tafa hannuwa tare da fasa salati ta yi cikin gida cikin gudu_gudu tana cewa. "Jama'a yau na ga abun da ya ishe ni bai ishi Allah ba, karuwanci har ƙofar gida a gaban Uwa da bainan nasi, Jama'a ku fito ku ga ikon Allah." Inna dake tsaye ta yi saurin ƙarasawa ta b'anb'are A'isha daga jikin Umar daƙyar ta yi cikin gida da ita ganin har an fara taruwa a gurin kamar wani babban abun ne ya faru. Umar ya bi su da kallo wasu hawaye masu ɗumi suka zubo akan kuncinsa, saurin goge su ya yi ya buɗe front seat cikin mawuyacin hali da k'uncin zuciya ya shiga ya zauna. Ado driver dake kallon sa ya girgiza kai cikin tausayawa ya kunna Motar. Umar ya ɗago kansa daƙyar ya yiwa gidansu A'isha kallon ƙarshe, har lokacin sautin kukanta bai gushe daga cikin zuciya da kunnensa ba, kuma ya san har abada ba zai taɓa gushewa ba. Lumshe idonsa ya yi a hankali lokacin da ya ji Ado driver ya ja Motar sun fara tafiya. "I loose her." Ya faɗi hakan a cikin zuciyarsa.
Wunin yau gaba-d'aya cikin kuka A'isha ta yi shi, ba ta taɓa tsintar kanta a cikin damuwa da tashin hankalin zuci irin wannan ba a rayuwarta. Ko lokacin tafiyar su Ma'u ba ta ji abun da take ji ba yanzu a cikin zuciyarta. Ta kasa yardar wa kanta Yaya Umar ɗinta ya tafi, ta kasa yarda ba za ta gan shi anjima ba, ta kasa yarda idan ta tashi gobe da safe ba za ta gan shi ba, ta kasa yarda ya tafi ya bar ta, gani take duk k'arya ne ko kuma mafarki take yi zata farka. Inna ma duk jikinta babu daɗi haka take jin sa, ga tausayin A'isha ga kuma kewar Uwar da za su yi, dan sabo ba k'arya ba ne, ko dabba ce da kai kuka rabu sai ka ji babu daɗi na rashin ganin gilmawarta balle Mutumin ya nuna maka k'auna a lokacin da kowa yake gudun ka, ya ja ka a jiki ya nuna maka kai ma wani ne, kai ma mutum ne mai daraja kamar kowa. Ya fitar da kai daga cikin halin k'unci da matsi na rayuwa.
Wunin yau gaba-d'aya cikin kuka A'isha ta yi shi, ba ta taɓa tsintar kanta a cikin damuwa da tashin hankalin zuci irin wannan ba a rayuwarta. Ko lokacin tafiyar su Ma'u ba ta ji abun da take ji ba yanzu a cikin zuciyarta. Ta kasa yardar wa kanta Yaya Umar ɗinta ya tafi, ta kasa yarda ba za ta gan shi anjima ba, ta kasa yarda idan ta tashi gobe da safe ba za ta gan shi ba, ta kasa yarda ya tafi ya bar ta, gani take duk k'arya ne ko kuma mafarki take yi zata farka. Inna ma duk jikinta babu daɗi haka take jin sa, ga tausayin A'isha ga kuma kewar Uwar da za su yi, dan sabo ba k'arya ba ne, ko dabba ce da kai kuka rabu sai ka ji babu daɗi na rashin ganin gilmawarta balle Mutumin ya nuna maka k'auna a lokacin da kowa yake gudun ka, ya ja ka a jiki ya nuna maka kai ma wani ne, kai ma mutum ne mai daraja kamar kowa. Ya fitar da kai daga cikin halin k'unci da matsi na rayuwa.