← Book details Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 85

Sashe 81

Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"zan tafi anjima xan dawo ki kular min da ..."

rufe masa baki tayi tana nuna masa su jannat dariya yayi yaja hannunta suka fice daga falon

sulthana ta kalli jannat

"oh anty jannat ?"

xare mata ido tayi jannat d'in

"anty jannat me ? ke wace irin futsara ce bakuyi agabana ba ? naga har janbakin ki kibawa haisam sbd k'auna "

suka k'arasa da dariya

"to ai naga leb'ensa ne"

sulthana ta fad'a tana turo baki girgixa kai jannat tayi tana dariya

"waya ce dama naki ne ?ko mai ma naki nasa ne"

shigowar rubayyace ta katse musu hira suka kalleta ta d'an canxa ba kamar d'axu ba dan gyalenta a hannu ma yake ganin haka yasa sulthana tayi dariya sosai ganewa Rubayya tayi itama tai dariyar tana girgixa kai hira sosai suka hau yi muryar wacce suka jini yasa su kallon juna cike da mmk jidda ce ta shigo da ita da wani da mmk suke kallonsu cike da murna suka rungume junansu suna kallon wanda suka shigo tare ya xauna yana danne dannen IPhaat cike da mmk jiddan take kallonsu ganin suna masa kallon kamar basu sanshi ba

muryarsa asanyaye suka gaisa yana dariya k'asa k'asa

"wai kuna nufin baku sanshi bane?" jidda ta fad'a tana harararsu

xuba mata ido sukayi

"toh mijina ne d'anjuma"

da mugun mmk suke kallon sa ya mik'e yana kallonsu hannunsa kan sajen fuskarsa yana shafawa

"nayi fushi da ku tunda kun kasa gane ni"

ya fice da sauri jidda tabi bayansa suma bin bayansu sukayi cike da mmk wai danjuma ne yaxama had'ad'd'an d'an gayu sai wani ji da kansa yake dan yasan yana da kyau yayi kib'a ya k'ara xama fari tass gashin kansa ya kwanta irin na fulani kai bakace d'anjuman da suka sani ba ne gab da shi jidda ta tsaya tana mariraicewa hango su jannat yayi yai dariya

suka k'araso kusa dasu suka gaisa cikin farin ciki ya amsa yana magana kmar wani bature jefi jefi har sun juya xasu tafi yace

"anty jannat ga jiddaty na xan bar miki amanar ta ki kulamin da duk wani motsinta,

kafin na dawo karki bari sulthana ta bibbige min ita"

xaro ido sulthana tayi cike da mmk kafin tayi magana

ya shafo fuskar jidda

"plx jiddaty ki kula fa sosai ki san ba ke kad'ai bace kike da kanki ban so ki wahala"

hannunshi cikin nata mmk ya hanasu magana da kyar jannat tace

"bakomai danju....khaleel xan kula da ita"

suka wuce cikin falon suna zama sulthana tace

"kan bala'i amma fa nayi mmk wannan abu wai d'anjuma ne yaxama wani big guy irin haka ya xama kamar wani d'an sarki lallai na yadda mace na gyara mijinta"

rubayya tace

"hmmm yanxu fa yafi jiddan ma wayewa"

suna cikin mgrn ta shigo a hargitse hannunta rik'e da d'ankwalinta fuskar ta cike da frin ciki tana dariya.

nan ta xauna suka hau hirar yaushe rabo basu dad'e ba zahra ta shigo tana dariya da mmk suka rungume junansu dake basu koma ba tun xuwan da sukayi

jannat take tmbyr ta

"ina ya mukarram d'in ?"

"da kyar muka rabu yanxun nan wai ba xai shigo ba sai anjima

wai wanne biki akeyi yau ? nayi nayi ya mukarram ya fad'a min yak'i"

suma xaro ido sukayi jannat tace

"biki kuma gsku ban sani ba "

suma d'in basu sani ba sulthana tace

"mu xuba musu ido magani"

nan suka cigaba da hirarsu akan irin soyayyar da mazajensu suke musu su kam sunfi mmkin

danjuma dan wayewar sa ta shammace su yanda suka kula jidda kam nacikin jin dad'i da soyayya mai k'arfi

shigowar hindu da mahboob daya kawo ta ne ya katsesu cikin farin ciki suka rungume juna mahboob ficewa yayi wai ana jiransa xai dawo anjima hira suka cigaba dayi jidda tana baxu lbrn xamanta da mijinta

"maza basu da kunya akan matayensu kunga yanda Ibrahim yake min agaban innarsa da kishiyata? soyayya kamar me haka innarsa ma na sona bakuga yanda suke kulawa dani ba, matarsa ma yarinya ce irin auren k'auyen nan anty take cemin tunda na girme ta,

da ita ake had'uwa ake nuna min soyayya tana da hkr bata damuwa ko kad'an,

dai dai gwargwado yana kwatanta adalci ni kam sai gdy ga Allah dan yanxu baxan iya rayuwa babu Ibrahim ba sbd ya shagwab'a ni da yawa"

dariya sukayi sulthana tace

"munga alama kam ni har mmkin haisam d'ina nake baya iya nesa dani ko ina xani k'afarsa k'afata kulawa ta ban mmk ko cikin gida,

dai dai da toilet sai ya bini shekaranjiya da mukaje gidan momy tana son muyi sirri ya kafa ya tsare yak'i tafiya yana kusa dani kamar xai shige cikina ko kunya sai da momy ta gaji tace muje ciki sulthana kai kuma ka xauna anan ya biyo mufa har d'aki momy tace futa ka bamu gu sirri xamuyi dady ne ya rarrashe sa yace kayi hkr xo mu fita kasan mata da sirri da kyar ya fice momy tace oh yaran nan ! bamu gama sirrin ba ya dawo wai mutafi gida .."

dariya sukeyi dukansu jannat tace

"yanxuma da kyar ya fice bayan kun kwashe 1 hour awaje daga rakiya"

Rubayya tace

"maxan yanxu kam abarsu nifa hajiyarsa ce min tayi Rubayya kiyi ta hkr dan Allah ya had'aki da naci kullum yana gida baya iya kyakkyawan motsi sai kina kusa dashi k'annansa har wasa suke min wai ina mannau d'inki alhmdllh danginsa na sona nayi dacen suruka da k'annan miji bani da wata matsala sai Hamdala"

zahra ta girgixa kai cikin dariya tace

"ni matsala ta missing d'in ku amma kunsan larabawa da kula tari wannan innayi ammi da Abbu kamar suyi me,

sun dink'a cemin sannu sannu

haka dangin sa cikin kulawa dani suke, shi kansa ya mukarram Ammi sai ta koreshi da fad'a

office kafin yaje sai ankusa k'aramin yak'i kusan kullum sai ya makara sai da Abbu yace tare xasu d'ink'a tafiya mu kam mun dace Allah ya datar da y'anmata masu burin yin aure"

hindu kamar xatayi hawaye tace

"amin ni kuma banyi dace ba ranar da aka kaini dayaxo mukayi hira ya fice yabar min gidan ban kuma ganinsa ba sai bayan kwana 3 shida matarsa tace min

hindu kada ki b'ata rayuwar ki da b'acin rai kibar min mijina nawa ne ni kad'ai kiyi hkr kije ki sami wani take tasa ya sakeni saki ma har uku !"

tak'arsa da xubar hawaye tausayinta ya kamasu jannat tace

"ki gdw Allah dan hakan shi ya fi miki alkairi Allah yabaki wanda ya fishi "

suka amsa da

"amin"

suka tashi gaba d'aya suka shiga kitcean suna k'ok'arin shirya lunch

bayan sungama sunyi sallah sun ci abinci suna hira har akai kiran sallar la'asar suka katse hirar sukaje sukayi sallah suka cigaba da tattauna lbrn hjy murja jidda tace

"shiyasa nake xaune lfy da tawa kishiyar ina gudun hak'k'in wani akaina Allah ya kare mu da xaluntar wani"

suka amsa da

"amin"

ya khaleel ne yai sallama ya shigo sulthana cikin tsokana

"oyoyo ga majnun "

d'an garamin murmushi yayi dan sulthana sam bata tsoranshi

"oh ! ashe fa tsoranka nakeji" ta kama baki sauran su ka gaishe shi ya amsa ba yabo ba falla gab da xai shiga d'aki yace

"ya xanyi dake sulthana tunda kin mai da ni k'aramin kakan ki"

dariya suka yi dukansu ya kira jannat ya bata wasu kayan na daban yace ta canza wani shegen yadi ne mai kyau sosai kamar material maroon colour an masa landing da fari sai head fari da farin sark'an gold nan da nan da shek'a kwalliya dasu tana mmkin me xa'ayi shima ya shek'a nashi adon da farin yadi shigen na ta amma shi mai kauri ne suka fito fess da su kamar ranar dinner wayam taga falon ba su sulthana hannunta ya rik'e suka fito harabar gidan taga ank'awata shi da decoration maroon da white su sulthana ta hango kowanne yana kusa da mijinsa ta kalleshi da mmk

"ya khaleel wai me akeyi ?"

janyota jikinsa yayi a hnkl ya rad'a mata a kunne

"birthday d'ina "

xaro ido tayi tana kallonshi ta b'ata rai

"shine baka fad'amin ba?"

"ina son baki mmk ne dan ke zan taya murna khaleel d'inki ya k'ara shekaru"

murmushi tayi rik'e da hannunta suka k'arasa wajen.

wajan xamansu na musamman suka xauna basuyi wani gayyata ba family memmbers d'insu ne kawai sai masu pix da vedio danjuma Ibrahim ne yai jawabi dan shi yagabatar da komai cike da birgewa ya birge kowa da barkwanci akayi nishad'i sannan suka mik'e xasu yanka cake waje ya rud'e ana wak'ar birthday

"happy birthday to u !

happy birthday to u !

happy birthday ya khaleel ! happy birthday to u ! "

ya yanko cake ya bata ta amsa tana k'ok'arin yankowa sukaji muryoyin da ya basu mmk hajiyarmu ce da hajja da momy da ammy da hjy Nabila suka taho suna tasu wak'ar birthday d'in

dariya sukayi dukansu da mmk haisam yake kallon hajja

"hajja harda ke ?"

ya mutsa fuska tayi

"eh harda ni kun maidamu tsoffi baku gayya ce mu ba toh mun kawo kanmu"

mukarram ya harari yusuf daya ke b'uya cikin gyalen hajiyar mu

"nasan wancen parrot d'in ne ya fad'a musu"

ya nuna yusuf

hajiyarmu tace

"koma waye munxo mu yanka cake"

dariya sukayi cike da nishad'i suka yanka cake akayi wasa da dariya masu photuna nayi shike da nishad'i suke hira dukansu kamar baxasu rabu ba.

*Ummee Garkuwa*

[3:16PM, 1/14/2017] Fatima Garba:
'<Øûß
'<Øûß
'<ØûßJENNIFER

'<Øûß
'<Øûß
'<Øûß

*na sadaukar da wannan page d'in ga y'an group d'ina Jennifer novel group da Hausa and English novel group da kuma y'an group d'in basma y'ar lele da kuma Ummu khamal novel group and all readers da writers ngd sosai Allah yabar xumunci*

123&124

*Ummee Garkuwa*

basu bar wajen ba sai bayan magrub suna cike da nishad'i sannan suka koma gidajensu

4 days ago

da safe Abba ya kira wayan ya khaleel yace suxo gida shida jannat a firgice suka je tunanin su ko wani abun ya faru
Chapter 81 · 0% Book details