← Book details Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 85

Sashe 35

Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wllh anty jannat Allah yana fishi da matar da take juyawa mijinta baya,

hindu tana dariya tace yauwa sulthana tunasar da ita,

waiwayowa jannat tayi ta hararesu jarababbu yau kam duk jarabarku baxan tanka muku cikin daren nan ba in kun gaji da neman fdan sai ku kwanta, ta juya musu baya

sulthana tace sorry anty jannat plx tashi ki bani shawarar na matsu naji kin san fa ina son ya haisam,

hindu ta katseta,

wai je bakya jin kunya ?? ki budi baki kice kina son wani ?

dan Allah ki dinka abu da tsari,

hararta sulthana tayi akufule tace idan ana mgnr kunya hindu kina da bakin da xaki ce kina da ita ?

ai babu me sauki a cikinmu irin jenny, ta kama baki sbd hararar da jannat tai mata sorry na manta jannat zance, cikin daure fuska tace ki kiyaye gaba plx bana son wannan sunan

hindu tace rashin kunyar da kikeyi sulthana bazan taba yin irintaba

tsaki sulthanan tayi tanawa hindu kallan sama da kasa ke abinda kikeyi waxai iya shi ? ko mazan ma da sukeyi ba kowanne namiji ne xai iya ba balle ke mace,

cikin fada hindu tace zan wanka miki mari fitsararriya,

farr sulthana tayi da ido ta ya b'una fuska ke kuma fandararriya

jannah ce ta katsesu haba dan Allah gsky ku kyaleni ko kowacce ta tafi dakinta kullum sai kun biyoni sannan baxa a xauna lafiya ba,

hindu tace sai dai ke kifita ba inda zani,

sulthana tace shareta anty jidda bani shawarar yanda zan shawo hnklinsa kin san ita ba abinda ta iya sai rike bindiga da baraxana da ita,

dariya hindu tayi sbd rashin kunyar ki yasa keda kika iya soyayyar kina so ba'a sonki

shiru sulthanan tayi hmm anty hindu kenan baki san ni bane na wahalar da samari banta ba son kowa araina inba haisam ba karkiso kiga tulin samarin dana ke dasu larabawa yayan sarakai da na attajirai

soyayya daban take bata daukar matsayi ko mulki na yadda haduwar jini ce kawai,

anty jannat ina jinki,

ajiyar xuciya jannat tayi idan xaki kiyaye ki jure,

tsaki tayi kinga anty jannat ke shari'ah ce da xaki dinka kafamin sharadi ?? kawai ki bani shawara dan ma kin ga ina lallabaki?

girgixa kai tayi zan bk ne sbd ke macece ciwon ya mace na ya mace ne ba dan halinki ba,

soyayya ba hauka bane dan kina son mutun ba hauka xaki tayi kina babatu har raini ya shiga tsakaninku, muddin kina shishshigewa namiji da nuna masa mahaukaciyar soyayya dole ya tsaneki ko da kuwa yana sonki burin namiji yasamu mace me aji, aji bawai wulakanci ba sbd yanmata basa tantance aji da wulakanci, wulakanta mutun bashi da kyau duk kaskancin sa, koyaya ansan mace da kunya idan baki da ita kina da kawaici ko baki iya kauda kai ba dole ki koya kibawa kanki kima da daraja ki canza wannan dabi,un da kike nuna masa agabansa ki shareshi, ba gaba ba, sama yake dake gaisuwa kawai xata dinka hadaku itama bawai ki saki fuska kina kwasar dariya ba, a a ba yabo ba fallasa daga gaisuwa kada ki yadda wata mgn ta hadaku dashi, jim sulthana tayi tana jinta,

sai ki janyo hnklin shi ta abinda yakeso bawai yadda xai gane ba cikin rashin sanin baki son yana so ba, da sauri ta kalleta anty jannat ta yaya ban gane ba ?

kinga ya haisam yana da son kwalliya da nutsuwa sannan yana da son cin abinci kusan duk mazan yanxu suna da son wayan nan abubuwan,

misali kiyi girki ki xubawa kowa shi kuma ki tura masa plate din kice ya xuba kinga yasan ke kikayi idan yana waje yi kokari ki kama kanki koda xakiyi surutun kiyi shi me ma'ana xaki ga shi kanshi ya fara shayinki,

jikinta asanyaye tace idan kuma baya sona fa ?

dariya jannat tayi kin san wani abu ? duk wanda kikejin soyayyarsa aranki shima yana ji xaiyi wuya kisamu wanda bayajin hakan ko yaya idan kika ga ya kyaleki kin nuna xakewa shine xaisa yaji ya tsaneki, kada ki kuskura ki nunawa namiji xakewa da rashin nuna kimarki ki nuna kina da kima da daraja kada ki nuna masa soyayyarki afili kija ra'ayinsa ta hanya mai kyau wacce xata kara miki kima awajansa, yasan lallai ke ta mutunci ce, ba namijin daya keson ballagaza, ki kyale ya haisam kiyi kamar ba sulthanan da cen ba dariya tayi cikin jin dadi ngd sosai anty jannah

*********************

washe gari bayan ta idar da sallar asubah gari nayin shaa ta koma bacci bata tashi ba sai 11:00 tayi mmkin baccin datayi ta shi tayi ta shiga toilet tai wanka hade dayin brush ta fito kenan taji karar test murmushi tayi dan tasan mr coffee ne dauko wayar tayi ta duba ....nashigo daxu kina bacci munta fi abuja da dady yau ko gobe xamu da wo

ki kula da kanki....

jim tayi xuciyarta ba dadi asanyaye tace Allah ya dawo da ku lfy ta shirya cikin riga da siket na less mara nauyi kalan brown da kwalliyar golden yellow ajikinshi falo tayi breakfast ta sakko babban falo ta same su dukansu ta xauna kusa da hindu tana gaishe da momy cikin kulawa da fara'a momy ta amsa, karar motoci sukaji, wasu mata suka shigo tare da jidda datake kuka, ganinsu yasa gaban jannat ya fadi tana kallon matan tagane dayar kanwar dady ce wacce ta xageta lokacin sa ranar jidda, da fara'a momy tace sannunku da xuwa,

dayarce tace dakata hajiya fiddausi " ba gaisuwa ce ta kawo mu ba, jidda na kwance jikin ummanta tana kuka lallai bashir ya nunamin ban isa da yayanshi ba tunda har xa a daura auren danshi yakasa sanardani sbd munafunci irin naki, dayar matar da jannat bata santa ba cikin fada tace hjy fiddausi burinki ya cika kin mallake mana dan'uwa sai abinda kikace sai abinda kikeso shi akeyi ke ishashshiya a daura auren waccen arniyar ta nuna sulthana atunaninta itace jannat da ibraheem bamu sani ba sbd tsabar munafunci irin naki, a kufule sulthana tace wllh ni ba arniya bace kije cen kinemi arniya inda take to wai ma suwaye ku da xaku xo kuna yi mana haushi cikin gida ?? da sauri momy ta toshe bakin sulthana idan na isa dake sulthana kar na kuma jin bakinki, sakin baki sukayi hade da yiwa sulthanan wulakantaccen kallo, da kyau dangin agumi yar masu sai da garar garau akan titi, sulthana ta zaburo momy ta riketa na miki mgn ba ruwanki dani sukeyi kiyi shiru,

hjy amina kiyi hkr ba a kyauta ba amma dadynsu da shi khaleel din sunta fi gidanki ta nuna daya matar cen abuja su fada miki yadda abun yake da niyyar in xasu dawo xasu biya wajan hjy hadiza, hjy hadizan ce momyn jidda cikin tsawa ta katseta rufemin baki munafuka, ran momy abace tace ku sani kufa kannan mijine ba yayyansa ba ba kowacce mgn ya dace ko yabamin ita ba, sulthana ta fashe da kukan takaici momy me yasa kika hanani mgn ? ki kyaleni na nuna musu jarabar sabon jini rikota momy tayi a a sulthana,

haka suka kare musu tas xagi nacin mutunci sannan suka tafi zigum kowa yayi a falon sulthana ce kawai take mitar jarabar an hanata kwatawa momy yanci jikin jannat asanyaye ta hau sama hawaye sosai takeyi tana kukan bakin cikin cin mutuncin da kannan dady sukaiwa momy duk a dalilinta gsky momy da dady mutane ne nagari baxata gushe ba har abada xata cigaba da yi musu addu'a har karshen rayuwar ta ranar kam gidan kwanan bacin rai kowa yayi

*****************

washegari da safe tana tashi test din ya khaleel ta gani na suna hanya sun kusa isowa hindu ta shigo fuskarta ba walwala jannat ta kira sunanta,ina son xuwa gidana nida sulthana zamu kwaso kayanmu masu amfani kin san tunda muka baro cen bamu koma ba,

da murna jannat tace nima zan biku ina son naje naga mamana da su david,

xaro ido hindu tayi waya ce miki yanxu irin da kike ? shari'a bata yadda ki fita ko nan da nan sai da ixinin mijinki,

a sanyaye tace yaushe xaku tafi ?

hindu tace sai yamma,

da murna tace yauwa time din ya dawo sai na nemi ixininsa,

********************

kitchen ta shiga ta shirya masa abinci kala kala wanda tasan yana so karfe biyu da rabi na rana ya dawo ya bar dady acan shi sai gobe xai dawo sbd yana da mittin,

tana shiga dakinsa ta tadda ya fito daga wanka ya xauna kusa da ita hade da kunna tv yana kallon tashar world sinima ta janyo flask xata fara xuba masa coffee dan tasan shiyake fara sha kafin yaci komai,

dakatar da ita yayi kinga " tashi ki cire wannan hijab din na jikinki a shagwabe ta kalleshi ya kau da kai yana kallon tv ganin ba wasa afuskarsa yasa ta cire ta ajjiye akan kujerar kusa dashi, ta dauko cup ta xuba masa coffee ta mika masa ya waiwayo xai amsa ya kalli kayan jikinta sun mata kyau sosai kamshin turarenta mai dadi ya cika dakin shi ya amsa yana sha kadan kadan ta xuba masa abincin ta ajjiye ta mike xata fita,

ina xaki tafi ? tayi shiru dawo ki xauna anan sai nagama cin abincin ya nuna mata kusa da shi a darare ta xauna tana jin kunya sosai ya kalleta yaga tayi nesa dashi daure fuska yayi ya nuna kusa dashi sosai, nan nace ki xauna, turo baki tayi ya yi murmushi sbd turo bakin yai mata kyau ta dawo kusa dashi ta xauna tana bata rai itama girgixa kai yayi yace yarinta ko meye na bata ran ?
Chapter 35 · 0% Book details