← Book details Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 85

Sashe 55

Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

awajan Kristen na tashi su suka reneni kan addininsu basu cutar dani ba illah gata da suka bani da kyar Allah ya taimakeni na amshi musulunci da taimakon mijina da iyayensa ga hindu cen tana fama da damfara da kwace kud'in mutane tana abu kamar namiji wannan ganin nakuma sai da ta damfare babban yaronka Abba wannan sulthana ce ba uban da tabari kowa rashin kunya ta ke masa, wahalarmu bata k'are ba tunda har yanxu ba'asan mai aikata hakan ba a tsorace dukansu suke kallonta cike da gamsuwa da bayaninta dukkansu maganganinta sun tsorata su sunkuma basu mmk da mugun takaici na rashin sanin tak'amai mai wake xaluntarsu shin yanxu kenan wani aiki sabone agabansu ? lallai kam dawowarsu xaisa mai aikata musu wannan muguntar yafara sabon shiri na yadda xai k'ara rabasu wai shin tayaya xasu gane waye mai ha'intarsu me sukai masa yake son jefa rayuwarsu cikin masifa yake gaba da farin cikinsu innalillahi wa innalaihi rajiun TSUGUNNE BATA K'ARE BA !

by

*Ummee Garkuwa*

[5:44PM, 12/18/2016] Fatima Garba:
'<Øûß
'<Øûß
'<ØûßJENNIFER
'<Øûß
'<Øûß
'<Øûß

85&86

Wani irin yanayi Na firgici da tashin hnkl lokaci d'aya suka shigesu gaba d'aya wajan tsit yayi kowa da irin abinda yake sak'awa aransa wai shin tayaya xasu gane wannan makirin ? Yanxu ta wacce fuska xai xo musu bayan wannan wahalar ta shekara da tashekaru nan gaba wacce iriyar wahalarwa xai musu ?

innalillahi wa inna ilaihi rajiunn kalmomin da dukansu suke maimaitawa kenan! cikin kuka sulthana tace,

" hakane Anty jannat maganar ki gaskiya ce shekara goma sha Tara ana abu d'aya kuma ba agane waye yake aikatawa ba ?

muna cikin had'ari, hawaye suka sauko mata da gudu tayi shiru tana goge hawayen,

Hindu ajiyar xuciya tayi cike da tausayin Kansu,

" shikenan nan gaba ma ina ga kashe mu xaiyi ni dai koma waye kada ka k'ara jefa rayuwa ta cikin masifa kwara ka kasheni Na huta Dan nika dai nasan irin rayuwar dana yi duk da Alhamdulillah ban ta b'a kisa bare aikata mummunan xunibi asalima ina da gata illah itace kawai kwace da damfara Na xama kamar wata annoba bana jin dad'in in dai ban kwace kud'in mutane ba yanxu ne nasamu sauki Allah ya yayemin,

ashe akwai sauran wata masifar innalillahi wa inna ilaihi raji'un

hajiyarmu ce tayi salati da k'arfi wani masifaffan bak'in ciki Na ratsa jijiyoyin jikinta cikin muryar kuka da takaici tace,

" baxaiyiyu ba

Allah baxai kuma bawa mak'iya nasara akanmu ba muma baxa mu xauna haka ba yasalam ! wannan wacce iriyar masiface ?

tsayawa jannat tayi da kukanta,

"nikam ko ayanxu aka kara watsani duniya ngd wa Allah Dan naga fuskokin iyayena naji farin cikin da akeji idan an kalli iyaye naji ni kwance jikin su,nasan mutanen nan bak'aramin hatsabibai bane kun manta abinda sukayi lokacin da xa a sace muku jasra ? wannan ya isa yasa Ku gane komai xasu iya kun manta sihirin dake jikinmu Wanda dakyar aka samu ya karye ? kun manta k'iyayyaan junanmu da aka had'amu da ita ? ta girgixa kai cike da yadda da xancenta wannan kad'ai ya isa yasa Ku gane ko ma suwaye sun riga sun shiga gabanmu,

da sauri hajiya murja ta dakatar da jannat,

" afrah plx ! ki daina karya mana xuciya bamu manta da hakan ba haka bamu manta da Allah ba kiyi tunani tayaya kuka dawo garemu ? daga Allah ko ? toh mun barwa Allah komai,

sarkine yai gyaran murya asanyaye yace,

" hakane murja kin gama mgn mun barwa Allah kowaye yake mana wannan ta'asar mun barshi da Allah ubangiji xai mana maganin komai kada Ku damu kada xuciyoyinku su karaya Ku had'asu da Allah Dan shi yasansu a duk inda suke kuma xai kareku daga sharrinsu yai mana maganinsu tunda sunfi karfin idonmu addau'a kuma yanxu akafara ubangiji Allah ya tona asirinsu,idon sarki yakai kan Alhaji adamu yaganshi cikin wani yanayi ya rik'e kirjinshi da hannu idonshi aruntse, sarki yace

" subhanallah Adamu ?

ahankl Adam ya dago kai cikin mayuwancin hali muryarshi adashe yace,

" Allah yana tare damu bi'ixnillah babu Wanda xai k'ara rabani da tsokar jikina Na samu yayana har abada babu mai rabamu,

abban A.k ya dafa kafad'ar shi muryarshi asanyaye yace,

" kada kadamu dawowarsu ya isheka samun kwarin gwiwa Na Allah ya karya k'arfin abokan gaba duk inda suke sukaji lbrn dawo warsu lokaci d'aya dole suji tsoro su gane Allah da kanshi ya karya musu lago mu cigaba da addu'a Na Allah ya bayyanasu ya kuma k'ara tsaremu,

nan sarki yai addu'a sbd dare ya fara yi dan har ankira magruba gab da xasu tashi dady yace,

jama'a Ku gafarceni agurguje tunda ankira sallah zan fad'a muku jannat fa tana auren d'ana gashi cen babban yarona ne khaleel nan ya kwashe lbrn dalilin auren ya fad'a musu,

sarki yai murmushin kasaita yace,

" haba bashir kaima fa y'ay'anka ne ko duka ka aurar dasu ai bakayi laifi ba in banda kai mutumin karkine kasan basu da asali har kabari d'anka ya aureta AI in wani ne sai dai in karta karb'i addinin,

rabon Alhaji Adam da dariya har ya manta sai yanxu ya D'an dara kad'an yace,

" AI babu wata mgnr agafarce ka ni Na haifi yaran nan kai ka wahala dasu ayanxu haka ba y'ay'ana ba ka isa dani kaina da duk wani abu dayake mallakina khaleel AI d'ana ne shi kanshi khaleel d'in ya isa dani kaina da duk wani abu Wanda yake mallakata kowa yaji dadin maganarsa haka sarki yace,

" matan su Shiga cikin gida suyi sallah da sun idar xasuje cen main house d'in su Na ched'e family su gansu Dan basu da lbrn dawowarsu,

suka shige cikin gidan sarki matan, maxan suka tafi masallaci Dan sauke farali

bayan sun idar da sallah suka tafi can main house dinsu Na ched'e family dake bashi da nisa da gidan sarki nan da nan suka isa, bayan sun isa ya tara dan gin nasu gaba d'aya ya fada musu y'ay'ansa sun dawo gareshi ya nuna musu su, cikin murna da farin ciki suke kiran tabbas ko makaho ya shafa yasan ya shafo fuskar y'ay'an adamu Dan kama har ta b'aci murna suka dink'ayi wasu ma kuka suka saka haka suka dink'a shafar jikinsu cikin so da kauna suna jin tmkr su hadiyesu,

jannat ta kallesu taga yawansu hawaye ya sauko mata aranta tana tunanin " ashe su yan dangine ake kiran su marasa asali ? tayi hamdala had'e da gdy ga Allah.

haka dangin ched'e sukai ta murna da farin ciki

bayan sun idar da sallar isha'i dady yace xasu koma gidanshi Na nan kusa dasu lameedo crescent xuwa gobe xasu dawo sunyi farin ciki da jin haka sun kuma bashi gwarin gwiwa Dan suma sunyi taradda din xaman shi cikinsu Dan sam basu yadda da junansu ba Dan cike suke da xargin kawu nan su

haka dai suka bar gidan nasu abinda bai tab'a faruwa ba,

direct gidan shi na kusa da main house dinsu ya koma shida dukansu bayan sun xaune aka sake sabuwar gaisuwa,

dady yana son yace wa iyalinsa sutafi yana jin babu dad'i aransa Na rabuwa da su jannat Dan sunyi mugun sabo sukansu iyalan dady tunanin rabuwa dasu suke,

jikin dady asanyaye yace,

"toh mu dai Alhaji adamu xamu tafi sai xuwa gobe Dan dare yayi, tuni jannat da Hindu suka mik'e sulthana ma mik'ewar tayi tace,

"gsky dady kwara muje Dan dare yayi,

jikin adamu ched'e da iyalansa asanyaye suke kallonsu Dan sun so ace yau sun kwana waje d'aya da yaransu kodan shekaru goma sha tara da suka kwashe cikin rad'ad'in rashinsu,

jikin momy asanyaye tace,

" a 'ah banda Ku anan xamu barku Ku kwana da iyayenku,

xaro ido sukayi dukansu,

jannat tace,

" wllh momy ba inda xaki ki barni,

turo baki sulthana tayi,

" momy k'afarki k'afata,

Hindu tace,

"tab momy tayaya ma xamu xauna anan dady muje dare yayi ina jin bacci,

Alhaji kasa mgn yayi sai binsu yake da ido cike da birgewa Dan ya fuskanci sun shak'u sosai dasu Dan ko suma iyayen karfin hali sukeyi,

dady yace

"kuyi hakuri yau kawai ! haba jannat, kukan shagwaba sufa Sam basu yadda da wannan tsarin ba,

murmushi dady yayi yace " kufa wani sa'in kunfi D'an shekara biyu rigima in kuka botsare sai Allah tunda kun dage Firdausi yau ki kwana anan dasu xuwa gobe ararrashe su ni da su khaleel xamu koma gida, xaro ido khaleel yayi cike da rashin yadda da mgnr dadynsu, cikin in Ina yana Sosa sajensa yace "a'ah yace dady inaga... dama.. ka ... barni ...a nan tunda jannat ta.....

momy ta katseshi da salati,

" khaleel oh ni Firdausi !

Alhaji adamu da iyalansa sukayi dariya

Alhaji yace,

" to nima nayi mgn abar min d'ana tunda matarshi tana nan, cikin jin kunya jannat ta rufe fuskarta,

dady yayi dariya yace bakomai,

suka tafi shida haisam da mahboob kawai, aka bar su rubayya da zahra da kuma khaleel alhaji ya rakasu har bakin get bayan yayi waya d ministern tsaro akan abashi Wanda xasu bashi tsaro har dady ma sai yasa aka tsare gidansa,

nan suka xauna a falo suna hira gwanin ban sha'awah lokaci d'aya sukayi sabo da junansu duk yawancin hirar akan su jannat ne,

Alhaji ya dawo daga rakiya ya taddasu suna hira xama shima yayi suka cigaba da hirar bai dad'e ba ya tashi ya barsu ya koma b'angarenshi bai dad'e ba ya dawo, ya kira khaleel ya nuna masa b'angarensa cen ya koma yai wanka yai shafa'i da wutr yana tunanin yadda xaiyi yaga jannat dan yau jinsa yake cikin wani yanayi na rashin hkr haka yaita juye juye akan gadon baya jin dad'in komai babu abinda yake son gani irin jannat d'insa gaba d'aya yaji wajan yayi mugun gundirarsa,

tana kwance jikin hajiyarmu tana jin dad'i mara fisaltuwa tana kallon fuskarshi lokacin da Alhaji ya kirasa wani irin kallo ya jefeta dashi wanda ta tabbatar da yana son ganinta ita kanta a wannan yanayin datake jin kanta na farin ciki xata so ta ganta kwance jikin faffaden k'irjinsa,

hajiya murja ce tace,

"Afrah maxa tashi kije wajan mijinki,

banxa tayi da ita kamar bata jiba,
Chapter 55 · 0% Book details