← Book details Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 85

Sashe 54

Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sanadin mutuwar baban shi yasa komai na kasuwancin mahaifinsa ya dawo kansa shiyake kula da komai

komai yanayin shine batare da jin dad'i ba abubuwa masu yawa sun tunkushe masa ga matsalar danginsa da suka sashi a gaba da sai ya k'ara aure ga mutuwar mahaifinshi sannan ga babban jigo shine rashin samun magaji abun ya had'u yai masa yawa yarame kana kallonsa kasan yana cikin tashin hnkl shi sam bashi da burin k'arin Aure tunda yasan matsalan rashin haihuwan ba daga wajansu bane Allah ne kawai bai basu ba

abin duniya ya ishe hajiya zainab ga rashin mijinta ga matsalar da danginta suke son takurawa danta hakan yasa ta tarasu ta samu su kuka tace sam bata yadda ba. d'anta da matarsa basu suka hana kansu haihuwa ba Allah ne bai basu ba su kyale shi yaji da abu biyu dan uku yai masa yawa, da kyar dai ta shawo kansu dan rigimammune haka dai suka hkr suna matukar jin haushi akan sunk'i yadda da mgnr su

kwanaki suka wuce sati ya shigo ya wuce haka watanni had'e da shekaru sai da suka shafe shekara 20 sannan Adamu ya k'ara aure ya auri SAKATARIYARSA, abinda ya bawa kowa mmk, akayi sa'a bata da fad'a sai d'an karan mutunci da biyayya dan soyayyar da take nunawa hajiya Nabila da surukarta yasa kowa yake sonta ciki kuwa harda shi kanshi Adam dan yana son uwargidansa da mahaifiyarsa suna xaune lafiya xama na biyayya murja tana matuk'ar girmama su, basa kishi ko kad'an kowa yana son kowa idan ma ba amfad'a maka ba baxaka taba tunanin kishiyoyi bane kwatsam baiyi wata da auren ba uwargidansa ta sami ciki, wohoho karkaso kaga farin cikin wajan dangi biyu dangin ched'en da dangin hjy Nabila kowa son cikin yake gata na duniya hjy Nabila tasameshi surukarta hjy Zainab kamar ta had'iyeta hakama kishiyarta hajiya murja da ita akaita renon cikin har ya kai wata tara hajiya Nabila Allah ya sauketa lafiya ta haifi y'an biyu mata, yasalam hajiya zainab kamar ta had'iye yaran abinda takeso Allah ya bata shi kanshi adamu ched'en jinsa yake tamkar sabo Allah ya bashi magada nan fa dangi akaita murna ana tururuwar zuwa dan kullum acikin biki ake har ranar suna ta xagayo a ka rad'awa yaran suna Ta farko aka sa mata Zainab sunan hajiyan Adamu suke ce mata afrah,ta biyun Aysha sunan maman Nabila ita kuma suka b'oye da Hishma, akayi shagali da wadak'a da arxiki kamar baxa a dainaba dan adamu rabon motoci da bubura ya yi tun lokacin da aka samu cikin yake raba abubuwa tun ana mamakinsa har ake masa kallon murna tasa ya fara xaucewa haka ya dink'a jidar danginsa da abokanan arxiki xuwa ummara sutaya shi yiwa Allah gdy na yasamu y'ay'a,

bayan suna da sati d'aya suna xaune a falo hishma tana hannun hajiya murja Afra na hannun hajiyarmu Nabila na kusa da mijinta suna hira cike da farin ciki hajiya Nabila tace,

" hajiyanmu ki shaida na bawa murja hishma halak malak dana yayeta ta rik'eta a hannunta kafin Allah ya bata dan na d'an d'ana rashin y'a nasan hakan xai sanya ta cikin farin ciki,

ai kam tana kawowa nan hajiya murja ta fashe da kukan farin ciki cike da farin ciki Alhaji yace "Nabila na jinjina miki kinyi namijin k'ok'ari Allah yai miki albarka,

itama hajiyarmu mmk tayi kamar ta xubar da hawaye tace,

"Nabilata Allah yai miki albarka kin biyani labila kin gama min komai kin birgeni ta waiwayo kan murja data ke rungume da hishma tana kuka,

"murja ki yi hkr ki daina wannan kukan dan kin cancanci abaki hishma sbd alkairinki da mutuncinki tunda kikaxo gidan nan kike mana biyayya da girmama mu cikin yaran nan kikai ta mana hidima babu abinda yake ranki najin haushi ko akasin haka kowa ya san da wannan duniya ta sheda hakan babu abinda xamiyi mu saka miki irin haka, ubangiji Allah ya baki naki y'ay'an suka amsa da "amin

jikin murja asanyaye tace " ina kukane na farin ciki dan wllh banta b'a jin cewa bani na haifi yaran nan ba ina jin su kamar tsokata ina jin soyayyarsu fiye da yadda nake son kaina ubangiji Allah ya raya min su jikinsu asanyaye suka amsa da "amin

mutane da yawa sunyi farin ciki da wannan kyauta da hjy Nabila tai wa kishiyarta hjy murja cikin kuwa harda dangin Nabilan dan suna matukar son murja saboda tsananin kirkinta uwa uba soyayya da wahalar da jikinta datakeyi dan ta farantawa Nabila,

ranar da sukayi arba'in haka akayi ta sadaka da abubuwa na ban mmk iri iri akayi shagali sannan aka watse kowa yana addu'ar Allah ya raya yan biyu AFRAH itace (jannat) HISHMA itace (Hindu)

bayan kwana goma dayin arba'in hajiya Nabila ranar ad'akin alhaji take ta gama ba yan biyunta nono tasasu agadonsu wanda yake gefen nasu gadon da daddare suka kwanta bacci,

washe gari aka nemi yara sama ko k'asa aka rasa tun sunayi isu isu har abu ya wuce xatonsu tuni hjy murja ta yanke jiki ta fad'i asume tana kururuwar y'arta Hishma kan kace me nan da nan lbr ya karad'e ched'e estate ana dube dube lungu da sak'o na ko ina sai da akayowa ched'e estate mugun chaje ba yara babu batunsu adamu tuni xuciyarshi tafara bugawa itama hajiyarmu jiri ya fara d'ibanta ta fara layi ta yanke jiki ta fad'i sanadiyyar haka ta kamu da ciwon b'arin jiki d'aya azababban fad'a ya kaure a ched'e family nan da nan suka shiga xargin juna ana ta xargi kowa da wanda yake zargi hjy Nabila kuwa kukan ma kasa yinshi tayi sai na xuciyarta wanda sanadin shi yasa xuciyarta ta kunbura

wasa wasa sai da aka kwashe wata biyar cif duk wanda ka gani cikin su hud'un nan sai ka tausaya masa alhaji adam da mahaifiyarsa da uwar gidansa da amaryarsa sun kad'e sun rame babu mai walwala bare mgn ana haka ciki ya b'ullo jikin hajiya Nabila nan da nan aka hau rabi da rabi wato farin ciki mai had'e da bak'in ciki cikin sai da yai wata hudu basu san dashi ba sbd mummunan yanayin da suka tsinci kansu,

haka aka reni cikin cikin kulawa da ta ka tsantsan bayan wata tara ta haifi y'arta mace aka sa mata sunan maman murja khadeeja suka b'oye sunan suke kiranta da jasrah yarinyar kamarta d'aya da mahaifinta wato kamar yayyanta da suka b'ata shekara d'aya da akai neman duniya aka rasasu har masu binciken da suka fi kowa iyawa aka d'auko da ga abroad basu gane kan abinba haka dai suka hkr akaita rok'on Allah akan ya bayyanasu duk lokacin da suka kalli fuskar yarsu jasrah sai sun xubar da hawaye dan kamarta da y'anuwanta har ta b'aci babu abinda ya banbanta su cikin farin ciki da bak'in ciki aka cigaba da rainon JASRAH (sulthana)

cike da kulawa da tsaro na musamman dan har camera aka bi aka like xagayen gidan da bak'in k'ofar get d'in nashiga ched'e estate gaba d'aya wajan b'angaren Alhaji Adamu xagaye yake da sojoji masu tsaron gidan, amma dake mai son abinka ya fika dabara bayan kwana hamsin aka wayi gari da sojojin da mutanen cikin gidan da masu gadin ched'e estate har da mak'otan gidan ched'en suna wani irin axababban bacci wanda suka k'i farkawa sai da taimakon manyan likitoci aka kuma nemi Jasrah aka rasa sama ko k'asa innalillahi wa inna ilaihi raji'un abinda dangin ched'e suke kira kenan dan abin ya wuce tunaninsu koke koke da masifaffen tashin hnkl nan da nan fad'a ya kaure atsakaninsu cike da zargin kawunan su da aibata junansu,

sai dare Adamu da matarsa hajiya nabila suka farka sbd abin yafi shigarsu sosai sauran sun farka da wuri, farkawar su jin mummunan labarin b'atan jasrah hajiya Nabila komawa tayi asume dan sai da tashafe awa biyar bata farkaba shi kam Alhaji kasa komai yayi sai k'unar xuciya haka ya dinka fitar da numfashi sama sama kamar xai daina fidda shi hajiya zainab ma tuni b'arin jinkita ya xuke sbd fad'uwar da ta kuma yi sbd jin mummunan labarin hjy murja itama suman tayi,

dangi ya rikice fad'a ijunan su ijunan su har ta kai ga ana bawa hammata iska dama gasu rigimammu haka suka dinka fad'a abubuwa suka had'u su kaiwa alhaji yawa ga masifar rashin y'ay'ansa da tunanin mai yanke masa jindad'insa ga axabar fad'an danginsa tarasu yayi ya fashe da kuka yace xai bar kasar ya gaji ba xai iya ba suna cikin masifar ya kwashe iyalinsa da matansa da mahaifiyar shi ya bar musu 9ja gaba d'aya sanadiyyar tafiyarshi sanadin wargajewar dangin basu bar estate dinba amma sun xama mak'iyan juna su kansu iyalin Adamu ched'en danginsa suke zargi sanadiyyar hakan hajiyarmu take xaune akan wannan keken mahaifiyar ku kuma har yau acikin cuta take sauk'i kam sai dai daga Allah mahaifinku kam sanadiyyar barin shi 9ja kenan dan ko ya shigo ta baya iya wuce kwana biyu nema da bincike babu wanda ba a yiba har yau ba asan wanene ya aikata hakan ba cikin hikima ta Allah sai gashi ya dawo mana da ku dolene kam mu godewa Allah ta k'arasa da kuka mai ban tausayi,

gaba d'aya jikinsu sanyi yayi lokaci d'aya suka sa kuka cikin wani yanayi na jin tausayin iyayensu jannat ce tace " haryamxu ba'asan waye ya aikata hakan ba ? d'aga mata kai hajiya murja tayi,

" lallai tsugunne bata k'are ba tunda ba'asan kowa ye bane ta fashe da kuka tacigaba da cewa,

" nan da kowanne lokaci xa'a k'ara rabamu da ku kunsan irin wahalar da mukasha akan azababban sihirin dake jikinmu ?
Chapter 54 · 0% Book details