← Book details Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 85

Sashe 76

Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"jannah ! wannan rigar ina son na ganki da ita a kyakkyawan jikinki kada ki sakata dan banso ki wahala" yasaka mata ita.

wulli tayi da rigar tana nunata da hannu

"harda had'in bakinki ? kada ki cuceni khaleel na sonki ajikina !" ........

runtse idonta tayi tasa rigar ta fito daga toilet d'in ta dawo falo ta xauna ta kalli sallayar dayake sallah ta kalli jama'ar falon

"momy ku dawo min da khaleel ! kunga sallayar sa ! idan na kalleta ina jin kamar zan ganshi ..."

kuka hindu tasa ita da hjy murja

"jannat kiyi hkr dan Allah kina jefa mu cikin axabar bak'in ciki" ta mik'a mata carbi "karb'i kiyi ta salati xuciyar ki ta sanyaya"

karb'ar carbin tayi

ta kece da kuka

"ya khaleel ne ya bani carbin nan da hannunsa yace na dinka xikiri gashi kin mik'omin shi sbd rashinsa,

ku tai makamin ku nemo minshi wllh idan ban ganshi ba sai na kashe kaina ! ..... wayyo ! innalillahi Allah kadawo min da khaleel ! mama meyasa xasu rabani da shi ? ki basu hkr kice nace su kyaleshi ni su kashe ni ! nasan sbd dani xasu axabtar min dashi .... momy ki dawo min da khaleel rubayya kinsan me nakeji ? ki daina kuka ki dawo min da khaleel zahra ! kin san gobarar xuciya ? xuciyat tayi gofara idan ba khaleel bani da sauran numfashi mutuwa xanyi ! hindu ki d'auko bindigar ki ki kashe ni! idan baku kashe ni ba zan haukace baxan iya yin shiru ba bansan hakana ke ba ! ku daina kuka ! kashe ni kawai xakuyi shine gatan da xakuyi min wayyyyo innalillahi wa inna ilaihi raji'unnn haka axabar xuciya yake wllh baxa ku gane me nakeji ba !""......

kuka dukansu sukeyi mai had'e da gunji

ta girgixa kai axababben hawaye na sauka

"sulthana ina muka b'oye bindigar hindu ? d'auko ta plx ! "....

cikin kuka sulthana tace

"anty jannat surutun nan naki yana axabtar da xuciyar mu kiyi hkr ki bari surutun ki yana mana illah axuciya ki bari bansan inda take ba !" ta k'arasa da wani irin kuka..

da kukan axaba jannat tace

"k'arya kike sulthana kin san inda bindigar hindu take mu muka b'oye ta,

momy bindigar tana gida a d'auko ta na harbi kaina ....."

ta shi tayi tsaye da sauri hjy murja ta rik'eta tayi wani mummunan murmushi

"mama kada ki rik'eni ki bari na fita na nemo ya khaleel idan ba haka ba zan mutu da axaban rashin ganinsa,

na tsani kaina bani da amfani "...... kanta na juyawa bibbiyu take kallon kowa

"sbd jin dad'i kun koma bibbiyu kowa ya xama iri biyu amma sbd bakwa son farin cikina sai kuka mai dashi d'aya ni ko shi d'ayan ne kubani shi ahaka mu rayu ...."""" kuka me cusa axaba takeyi tana k'ok'arin kwace kanta daga hannun hjy murja bayan ta fincike tayi luuuu ta k'ume da center table ta gangara wajan kujera kanta ya k'ara k'umuwa.

gaba d'aynsu suka sa kuka sukayo kanta tana k'ok'arin tashi ta sume a hannun hjy murja jini na fita akanta wulli hajiyarmu tayi da sandar ta tararu mosu ita da hjy murjan tana wani irin kuka

"jannat na shiga uku ni zainab naga axabar rayuwa ! "

suna k'ok'arin fita da ita suna rusa kuka mahboob ya shigo arikice yana mgn yana fidda uban haki

" ga khaleel can an yasar mana dashi a k'ofar gida ko ina na jikinsa sarane ! "

da gudu suka fice suna wani irin kuka sam ! sun manta sun tab'a rayuwar farin ciki.

a sume khaleel d'in yake su dady suna k'ok'arin sa shi amota suka hango matan sun nufu so suna kuka jannat rumgume jikin hjy murja kamar matacciya da kuka suka basu lbrn abinda ya faru suka sata amota suka nufi asibiti

asibitin su wanda suke xuwa sama da shekara 20 suka tafi babban likitan daya ke dubasu ya fito da sauri ya nufi inda aka kai khaleel emergency d'akin k'asa ita kuma jannat tana sama b'angaren mata

hjy murja ta biyo bayan Dr fahat tana kuka tana fad'in

"Dr fahat kai sauri muna buk'atar khaleel ka ceto mana rayuwarsa"...

"kiyi hkr madan xamuyi iya k'ok'arin mu"

ya shiga d'akin ya umarci kowa ya fita

suna fita ya xuge labule bayan ya rufe k'ofa ya d'auko kwalbar allurai guda biyu d'aya mai murfi ja d'aya kuma fara ya dad'e yana naxari ya ajjiye me farin murfi ya bud'e mai jan murfin yasa allura ya xuk'ota ya kalli khaleel dayake asume ya tsikara masa allurar ya mayar da ita aljihunsa yai ajiyar xuciya ya bud'e k'ofar d'akin ya fito ya samesu sunyi jigum jigum cikin kasalalliyar murya me cike da tausayi yace

"nan da 20 mints xaku iya shiga amma bai farfad'o daga suman ba" ya wuce office d'insa

bayan 15 mints suka shiga d'akin yana kwance babu alamun motsi dady yana kallonshi gabansa ya fad'i ya kara kunnansa yaji babu alamun numfshi ya d'aga hannunsa asake gumi me d'umi ya karyo masa yace

"innalillahi wa inna ilaihi raji'unnn khaleel ai yarasu ! "

salati me k'arfi suka saki da gudu hjy murja tai office d'in Dr fahat tana sambatu baya office d'in giftawar shi ta hango a sama d'akin da jannat take ta haw saman tana ihu

jannat ta farfad'o idonta akan dr tana k'ok'arin mgn hjy murja ta shigo tana sambatu

" Dr fahat khaleel ya rasu ! "

da sauri matan suka mik'e arikice cikin mugun yanayi kafin su ankara jannat tayi kukan kura ta bangaje su ta fice a guje suka dafa mata baya sam bata ganin komai ta gangaro daga benan tundaga na farko har na k'arshe tuni ta sume jini mai yawa ya b'alle yana fita ta gabanta cikin mugun yanayi suka kinkimeta dr yace su kaita d'akin da khaleel yake kuka sosai mahboob da haisam suke shi kanshi Abba kukan yake yana surutan baxai yadda ba sai ya d'au mataki su ka kwantar da ita kusa da gadon khaleel Dr fahat yace su fita xai dubata

suna fita ya ciro allurar da yaiwa khaleel itama ya tsira mata ya maida aljihu ya bud'e d'akin ya fito ya samesu duk sun rud'e suna kuka me tsuma xuciya babu me rarrashin wani dr Fahat ya goge gumin fuskarsa ya girgixa kai bakin shi na rawa yace

"kuyi hkr itama ta rasu !"

kuka suka kece dashi kowa na sambatu sulthana muryarta tafi ta kowa d'agawa

"ya xakuyi mana haka anty jannat muna sonku ! nima kashe kaina xanyi wayyyyo ! jannat ki tashi ku rayu "........!!!!!!!!!

salati me k'arfi hajiyar mu tayi suna waiwayo wa murja asheme ta sume da gudu hjy Nabila ta nufi office d'in Dr Fahat tana surutai irin na xautuwa

"Dr kaxo itama xata mutu murja dukansu sun mutu wllh nima bazan rayuwa ba mutuwa xanyi".......!!!!!!

arikice yace jeki gani nan xuwa da gudu ta fita har tana tuntub'e

murmushin mugunta yayi da muryar azzalumai yace

"saura ke murja dan kece nest target d'ina dole ki mutu!!!!!""""".....

*Ummee Garkuwa*

i dedicated dis page to u Rukayya abubakar yola (rakiya =ØÞ=ØÞ)

saura ki [truncated by WhatsApp]

[6:58PM, 1/9/2017] Fatima Garba:
'<Øûß
'<Øûß
'<ØûßJENNIFER
'<Øûß
'<Øûß
'<Øûß

115&116

*Ummee Garkuwa*

*warwara*

kai tsaye dr fahat d'akin da aka kwantar da hjy murja ya nufa ya taddasu akanta suna rusa kuka kowanne da kalan surutun da ya keyi da tausayi ya kallesu yace su fice xai dubata kamar baxa su fita ba hk suka fita suna jimamin abinda xai biyo baya.

suna fita ya rufe k'ofar yana hangensu ta window suka tsaya cen babban harabar asibitin dai dai d'akin da khaleel da jannah suke.

murmushi dr fahat yayi ya rufe window ya xuge labule.

gaf da hjy murja yaje ya tsaya ya shafa fuskarta yana murmushin mugunta cikin muryar mmk yace

"shegiya talatu wai dan Allah ya akayi kika iya suman k'arya ?"

bud'e idonta tayi ta mik'e had'e da sakin dariya

"d'an iska sarkin tambaya manta ni kayi ?

kasan wannan kad'an ne daga cikin shed'anci na"

kusa da ita ya xauna yana k'are mata kallo

"talatu ba Allah aranki kina birgeni sbd makirci"

wani kallo ta jefeshi dashi

"kai d'an iska ba na hana ka cemin talatu ba ?"

dariya yayi ya tab'e baki

"kunjini da shegiya waya ce miki ana canzawa tuwo suna ?kina nan a yanda na sanki TALATU MASIFA,

amma yanxu kin koma talatu makira"

yak'arasa da kai mata d'an k'aramin duka a fuska .

far tayi da ido ta ya mutsa fuska

"kasan dai murja iyayena suka rad'amin ko ?"

tsaki yayi

"ke kam bakya canzawa kullum muka had'u sai mun raba hali shekara 30 kenan ba'a canzawa sunanki murja kuma talatu duk iyayenki ne suka rad'a miki bawani shege ba"

mik'ewa tayi tsaye tana kallon gefen gadon dayake

"fahat kaci wannan tuffan dana baka d'axu lokacin da muka kawo shegen yaron cen khaleel?"

dariya yayi mai sauti ya kalleta data tsura masa ido

"naci murja ! meyasa kika damu da sai na ci ?"

ajiyar xuciya tayi sannan ta saki dariya me kyau

"bakomai fahat ina son naji ka cine "

d'age kafad'a yayi

"shikenan talatu ya cikon kud'ina ? kin san ni akan kud'i koda ubana zan iya b'atawa"

watsa masa harara tayi ta juya baki tana masa kallon raini

"mtssw banza mayen kud'i d'an iska jarababbe wllh duk nacinka bazan k'ara mk ko sisi ba "

"dama kin saba y'ar talakawa amma wannan karan shine na k'arshe talatu kin sanni nasanki wllh sai naci ubanki akan kud'in nan"

"fahat kasan kuwa kaine nest target d'ina ? duk duniya kafi uban kowa sanin sirrina babban had'arine xama da kai araye dan nafara shakku akanka kafiya mistakes a ayyukanka"

"talatu kenan nasan wannan yunk'urin naki nasan ina cikin way'anda xaki bada list d'insu akashe, kafin na mutu ki bani cikon kud'ina shekara 30 kenan ina wahala dake akan wannan wllh zan b'ata miki ayki dan tuna miki asiri zanyi

dariya tayi harda kyakyatawa ta nuna shi da yatsa cikin dariya

"kamanta ni fahat kamanta ni shed'aniya ce kai shedan ma yasan nafishi shed'an ci me xaka fad'a musu ?
Chapter 76 · 0% Book details