Sashe 48
Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Tun kafin ya huta sulthana da Hindu suketa tambayarshi jannat ce kawai batayi mgn ba itama yasan kunya ce ta hanata ya basu hkr su bari yai sallah, ya idar da sallah ya ya tarasu duka a babban falo da nasiha ya fara sai da ya tabbatar jikinsu yai sanyi sannan ya fada musu avinda ya faru ga mmkin sa sai yaga sunyi tawakkali basu tada hnklinsu ba, ya khaleel ya kalli dady,
Dady uwargidan ched'e tana da alaka mai girma tsakaninta da masarautar garin nan dan kakanta yai mulki yanxu haka sarki yayanta ne Dan kakan ninsu d'aya mai xai hana aje wajan sarkin ai mishi bayanin komai tunda nasan ba xa a samu matsala da ga b'angreshi ba, murmushi dady yayi nan da nan ya nemi bacin ransa ya rasa, sbd shawarar da khaleel ya kawo shi Sam bai son da haka ba, hakane khaleel Allah yai mk albarka,
Amin dady xanyi wa prince A,K Garkuwa mgn yai mk jagora wajan sarkin tunda shima suna da babbar alaka duk dangin sune, dady ya saki fuska, mashaa Allah in shaa Allah kuwa gobe nakeso naga sarkin mutattauna dan nafison yaran nan suga iyayensu su huta da wannan bakin cikin,
In shaa Allah dady xankira A.K Garkuwan anjima kadan basu bar wajan ba sai da dady yai addu'a akan Allah ya basu nasara sannan suka tashi suna jin dadin wannan shawarar da ya khaleel ya bada,
Washegari dady tun 2:00 na rana yaje gidan sarki dan tun safe ya khaleel yake kiran A.K Garkuwa wayarshi akashe rabonshi da shi tun jiya da sukayi waya da daddare ya fad'a masa yace badamuwa kai tsaye ba'n garensu A.K Garkuwa sukaje suka tadda shi shida mahaifinsa bayan sun gaisa suka fadawa mahaifin A.k, kabeeru Garkuwa na suna son ai musu iso wajan sarki,
Alhaji kabeer Garkuwa yace, yasalam anyi sab'ani sarki ya jiya jiyan nan ya tafi umara sai yayi kwana 12 xai dawo sai dai kuyi hkr Ku jirashi nan da kwana 12 jikinsu asanyaye suka dawo nan ma lallashinsu yayi yace kwana 12 kamar gobene in Allah yasa muna da tsawon rai, jikinsu yai sanyi Dan gani suke kamar baxa suga iyayensu ba, dady ya kwantar musu da hnkl da nasihohi,
Bayan kwana 9
Saura kwana 4 d'aurin auren ya khaleel da jidda, kullum cikin fita unguwa suke dan tunda sukaxo itada ummanta basu koma ba sauran ne suka koma suma jiya suka dawo aka fara shirye shiryen biki, kullum kafin dady ya fita sai yai musu nasihan kada su biyewa k'annansa Dan yasan mafad'a tane kullum sai sun yadda musu da mgn, babu mai kulasu sulthana ce mara hkr dalilin dayasa momy tace ta dawo b'angarenta duk inda ta xauna sulthana na kusa da ita sbd gudin rigima,
Jannat na kwance adakinta xuciyarta cunkushe tarasa me ke damunta tun safe ta kasa fita jikinta duk yayi sanyi, turo k'ofa akayi tayi tunanin ko su Hindu ne shiyasa bata waiwaya ba, fusgo hijab din jikinta taji anyi da sauri ta waiwayo had'e da mikewa ta kallesu hantar cikinta ta kad'a sbd tsoro ta bisu da wani irin kallo cike da firgici,
Jidda ce zahra da umman jiddan, suna mata wani matsiyacin kallo,
Umman Jidda tai guda ta dingure mata kai, to Yar tsintuwa jikar bola kin mike agado kamar na ubanki, kin kwaso tarkacen bola irinki y'an'uwanki kin kawo gida sbd kuna son maidamin Yaya irinku to shi Dan asaline kowa yasan kakan nin kakaninsa, Jidda tace hmm, ummana ni kadai nasan bakin cikin dana keji inna kalli wannan a matsayin kishiyata Mara galihu wacce bata da asali gayyar tsiya, wllh momy sam yarinyar nan bata dace da ya khaleel ba da su danjuma ta dace talaka irinta,
Zahra ta katseta, ina bakin cikin ace wannan itace matar ya khaleel dole na yadda asiri sukai masa, ummanmu plx ki karya sihirin nan ya rabu da shegiya mu huta nifa na fison ace yayana ya auri Yar wani k'usa a garin nan ko Anty Jidda amma ya b'ige a Mara galihu mtsww,
Umman tace barni da shegu ni ce maganinsu sai na karya bakin asirinsu, Jidda ta karasa da sai ako mawa danjuma dan tun farko shi naso ki aura, suka fice bayan sun gama mata cin mutunci,
Tagumi tayi tana xubar da hawaye masu xafi da kuna, kuka mai daci ya kufce mata taitayin shi har sai da kanta ya fara sarawa ta dauki kur'ani tana karantawa a hnkl a hnkl tafara jin saukin radadin da xuciyarta takeyi, ta Dade tana addu'a akan Allah ya kawo mata sauki cikin al'amuran rayuwarsu, karar wayar ta taji ta kalli screen din wayar ta ga ya khaleel ne haushi ya kamata taga duk danshi ake mata wannan cin kashin ta kyale taki dagawa har wayan ta yanke, ta tsurawa wayan ido tana tunanin any'a kuwa ta kyauta ? Tasan ba shi yai mataba, tayi ajiyar xuciya tana ganin tayi babban kuskure na k'in d'aga wayarshi da tayi motsin bude kofa taji anyi da sauri ta kalli kofar atsorace, ya shigo, yana kallon fuskarta da tasha kuka, tayi jaja jaja ya karaso inda take ta sunkuyar da kanta ya xauna kusa da ita, ya janyota jikinshi ta saki ajiyar xuciya, cikin muryar lallashi, me ya sameki ? Tayi shiru tana tunanin amsar bashi, kuka ya kufce mata da ta tuno bakaken magangun da su jidda sukai mata, lalashinta yayi yana tunanin ko damuwar rashin iyayenta ne, shi kanshi yana cikin damuwa ta rashin ganin iyayen nasu daurewa kawai yakeyi, nasiha ya cigaba da yi mata, har sai da jikinta yai sanyi ta daina kukan ya xamota daga jikinsa ya shafa cikinta, kinci abinci kuwa ? Kai ta daga masa, anya kuwa beautyna cikin nan naki baiyi kama da Wanda ya ci abinci ba, ya mike yana kallonta, ina jin yunwa ki kawomin abinci hade da coffee ina jiranki ya fita, ta mike jikinta asanyaye ta tashi ta tafi kitchen,
Jidda ce take ta safa da marwa daga sama xuwa dining ganin momy da sulthana sun hau sama yin sallah sai Hindu kad'ai suka bari a falo yasa ta faki idonta ta d'ebe abinci a flask cikin sauri ta fita waje da shi ta d'auko d'aurin maganinta ta barbarda tai b'angaren ya khaleel kai tsaye ta shige dakin cikin bacin rai ya kalleta, meke damunki Jidda ? Meyasa vaki iya sallama ba in xaki shigowa mutane daki ? Da sauri ta juya aranta tana fadin xaka gane kuranka na kusa rama wulakancin da kk min in dai kaci abincin nan sallama tayi ya amsa kamar bayaso ta shigo ta ajjiye abincin yana tsaye kusa da kofar toilet dinshi, ta kalleshi ya khaleel abinci naka wo maka,
Ok ajjiye wanka zan shiga kije ngd,
Tayi narai narai, ya khaleel na dawo to anjima?
Kan sa ya daga mata ya shige toilet bata so ba ta fice daga dakin tana murnan yau xata sami kan ya khaleel da murna ta hau sama dan tabawa ummanta da sauran yan'uwanta lbrn ta xuba maganin
Bayan ta xuba masa abincin ta wuce kitchen ta hada masa coffee ta nufo bangarensa tayi sallama ya amsa hade da xubawa k'ofar ido ta shigo dai dai lokacin daya ke xuba abincin da Jidda ta kawo masa a plate ganinta yasa ya ajjiye, ta kalli abincin tasan Jidda ce ta kawoshi ta b'ata rai had'e da turo baki, dad'i ya kamashi ganin tayi kishinsa sosai, sorry beautyna ina jin yunwa ne sosai, bata ce masa komai ba ta xuba mishi nata avincin ta mika masa ya amsa ta xuba masa coffee sai da ya fara shan shi sannan yaci abincin suna hira jefi jefi, kwatsam kamar an jehota ta shigo ta gallawa jannat harara ganin yana cin abincin dake duk iri d'ayane yasa ta lumshe ido tana jin dadi, tsawa ya khaleel yai mata, baki da hnkl ? Ki dink'a shigowa d'akin mutane ba sallama, murmushin samun nasara tayi ta fice batace masa komai ba,
Bayan yagama cin abincin jannat ta d'auki flask din da plate da cups din da tashigo dasu ta fita tabar abincin Jidda anan, murmushi yayi ya bita da kallo dan tunda ta shigo taga abincin jiddan take bata rai daukar abincin yai ya fito harabar gidan dashi ya ci karo da danjuma dayake wanke kayansa,
"Danjuma Dan Allah ga wannan abincin kabawa almajirai,
Jikin danjuma na rawa ya amsa Dan dama yunwa yakeji ya ajjiye wankin a ransa yana fadin gani kuma wanne almajiri xan nema, sbd gaggawar yaci abincin ko bissmillah baiyi ba ya fara cinshi da sauri da sauri kamar wnda xa'a kwace mishi ya cinye abincin tass dai dai da kashin naman sai da ya taune da kyar ya xubar da dusar k'ashin yasha ruwa yai hamdala ya shige d'akinsa ya kunna redio yana sauraro wani nannauyan bacci yai awan gaba dashi