← Book details Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 85

Sashe 80

Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

haka y'anuwansa suka dink'a fad'a ranar kam sun dad'e suna mitting suna rok'ar junan su yafiya sbd xargin da sukaiwa kawunan su masu gaba da juna suka daina take yanke basu bar wajan ba sai da akayi kiran sallah hindu ce ta kira hafiz mijinta na da tace yaxo ya d'auki hjy murja dan kowa ya fita sabgarta babu mai kulata ga ciwon cikin dake bigeta kamar farfad'iya uwa uba jinin datake xubarwa me k'arni aikin poisind d'in data sha bata fad'a masa komai ba sai da yaxo Abba ya bashi lbr dan jininsu ya had'u da yaron kuka sosai hafix yayi yana jinjina rashin imani da yayarsa haka ya kinki meta ya kaita asibiti

sukace baxasu iya ba dan poising d'in yaratsa ta yayi awa goma acikinta dole ya dawo da ita gidan k'annansa ya ajjiye yai tafiyarsa yana Allah wadai da bak'in halinta.

bayan hankalinsu ya kwanta suka kuma yin gagarumin meeting akan wannan matsalar data wuce suka tattauna Abba ya tara sojojin da y'ansan dan da aka xuba a unguwarsu da gidajensu ya sallamesu da kud'ad'e masu yawa shi kam b'anagre d'aya na xuciyar shi yana jin dad'in wahalarsa taxo k'arshe gefe d'aya na takaicin wai ashe murja ce take ha'intarsa ?"

jannat tana kwance gefen jikin ya khaleel awajan taron ko kad'an bata son nesa dashi jikinta xaxxab'ine da jiri ke damunta na rashin cin abinci da bata yi kwanaki ba hjy Nabila na kula da ita ana gama meeting d'in ta rungumota jikinta tana tab'a ta

"jikin nan naki akwai xaxxab'i jannah ! gida xamu koma tare in kin warware kya koma gidanki !"

xaro ido khaleel yai ganin haka yasa momy tace

"gaskiya kam dan jikinta baiyi kwari ba nan da sati uku ta koma"

kasa jurewa khaleel yayi ya marairaice

" momy plx ina laifin kwana d'aya ? xamuje a dubata anjima a hospital "

hjy Nabila tai murmushi

"shikenan mai jannah ! kada ka damu goben ta koma tunda ka dawo dama ai cuta ta warke"

ta k'arasa tana kallon jannat

da saur ta rufe idonta cikin jin kunya dan bawani sabo sukayi da mahaifiyar su ba sunfi sabawa da hajiya murja sosai

bayadda yaso haka ya kyale su dake magrub ta kusa k'in barin gidan yayi sbd shima anan ya kwana

washegari hajiya xainab da Abbu da ya mukarram da zahra suka diro 9jaa sbd sunji lbrn b'atan khaleel da dawowarsa sai bayan sun xo sukaji lbrn abinda hjy murja tayi sunda d'e suna mamaki sosai sun jimanta dan zahra da hjy zainab har kuka sukayi abinka ga mata da raunin xuciya haka suka xauna suna hira sosai suna ta ujjibi da mmk akan abinda ya faru kowanne xuciyar shi ta kai k'arshe a mmk hjy Nabila tace

"ni kaina Zainab har gobe ina tambayar xuciya ta meyasa murja tai min haka duk irin yadda da amanar da na bata y'ay'ana sukutum duka nabar mata fa itake kula dasu da duk wani sha'aninsu Allah sarki murja wani gefen na xuciya ta na tausayin halin tada ke ciki danni da gske ina k'aunarta sbd k'aunar y'ay'ana data yi duk da na makirci ne !"

da yamma jikin jannat yai sauk'i ya khaleel ya d'auketa bayan hjy Nabila ta bashi tana tsokanar sa

" ga jannar ka nan kar kahana mu sakat Allah ya kare min ku ya sauketa lfy "

gidan su suka shiga hannunshi rik'e da ita wanka sukayi yanda suka saba take kowanne ya fara komawa nrml bayan sunfito daga wankan yanda suka saba xasu shafa mai ya janyota jikinsa hannunsa na shafar cikin ta tasa hannunta dai dai ciwon da garadan nan suka ji masa

"Allah yasa kalli yanda suka dokar min jikinka ?"

jinjina kai yayi

"axabar rashinki tafi wannan dukan xafi da k'una ! ni kad'ai nasan bala'in dana shiga rashinki duk lokacin da suke dukana babu abinda nake tunawa sai kyakkyawar fuskar ki hakan yana sa naji bana jin dukan duk xafin shi ina tsananin sonki jannah !"

wasu hawaye suka xubo mata

"ban san kaine rayuwata ba sai bayan baka nan baxan iya aiwatar da komai ba sai kana tare dani dan dakai nake iya komai cin abinci wanka kai ne rayuwa ta !"

girgixa mata kai yayi yana share hawayenta masu xafi da suka sauko mata

"meyasa kike son xubar min da hawayen ki masu tsada ?"

"hawayen farin cikine khaleel narasa wanne abu xanyi na farin cikin gani jikinka jikin da nai kwana hud'u bana tare dashi shiyasa ni xubar wannan hawayen "

rungumota yayi sosai tamkar wanda xa a kwace ta yana jin axabar sonta idanuwansa na k'ok'arin ingixo hawayen da suka cika masa ido !.

*Ummee Garkuwa*

[9:16PM, 1/11/2017] Fatima Garba:
'<Øûß
'<Øûß
'<ØûßJENNIFER
'<Øûß
'<Øûß
'<Øûß

121&122

*Ummee Garkuwa*

da sauri ya shanye hawayen bai xuba ba ahnkl ya janye jikinsa yana kallonta hannunshi nasha far cikinta cikin kasala yake magana

"ajiyata tana nan yadda na barta amma ...."

ware ido tayi tasa hannunta kan hannunshi daya ke shafa cikinta

"amma me....?"

dariya yayi mara sauti

"naga ya rame any'a kina kular min da shi kuwa?"

turo baki tayi ko me ta tuno da sauri ta sauke bakin tana dariya shima dariyar yayi yasan abinda ta tuno ta sai ta bakin ta

"ina kular maka dashi sosai fiye ma da yadda na ke kula da kaina"

xare ido yayi yana kallonta da manyan idanuwansa

ya girgixa kai

"bance ba ! bance ki kular min dashi fiye dake ba ! ina son ya xama 50&50"

ya saketa ya juya ya d'auko gown me kyau ta shadda ya mik'a mata ta amsa xata saka ya rik'e hannayenta

"ajiya na baki bance ki saka ba"

ya amsa yasaka mata ita yana murmushi

"kamar dan ke akayita tayi miki kyau sosai ! komai yana dacewa da jikinki beautyna!

murmushi tayi idanuwansu akan juna

"ngd sosai ya khaleel"

bayan sun gama shirin suka fito babban falo yana gyara link d'in hannun rigar sa ya d'ago kai yana kallonta

"yau fa muna da bak'i"

da mmk ta tambayesa

"suwaye xasu xo ?

"murnar me kike haka"

cikin xak'uwa tace

"sbd xamuyi bak'i"

murmushin da bayyi niyya ba ya sub'ce masa

"xasu xo xakiga ko suwaye"

ya fad'a cikin ko inkula

marairaicewa tayi tana kwab'a fuska

"plxxxxx !!!"

ya kalleta yanda tayi yayi shima

"plxxxxx!!!"

d'ank'aramin duka ta kai masa a k'irji yasa hannu ya dafe wajan

" washhhhh ! ki ka dake ni ? bazan yadda ba sai na rama a inda kika dake ni"

dariya tayi tabar wajan da tafiya da sauri ya xuba mata ito yana dariya

nesa dashi ta tsaya

suna kallon juna

ya tab'e baki

"xan dawo anjima kad'an "

"adawo lfy Allah ya kiyaye hanya"

"amin "

ya amsa ya fice ta dawo falon ta xauna had'e da xabga tagumi duk sai taji kewar sa ko kad'an bata son yai nesa da ita

bata dad'e a falon ba taji sallama kamar muryar sulthana tana d'ago kai suka had'a ido ta ita taci ado sunyi anko da mijinta haisam kamar amaryar daxata tare gidan mijinta

washe baki tayi tana mmkin xuwansu

"oyoyo ! oyoyo ! "

haisam ya k'araso suka xauna suka gaisa sulthana na tsokanarta

"lfy antinmu ya ajiyar mu ? hop ana kular mana da ita ?"

hararar wasa jannat tai mata tana girgixa kai haisam yai dariya had'e da mik'ewa

"babyna xan dawo nan da 3 hours ya khaleel na jirana"

cikin muryar jan hankali tace

"ok sweet ka kular min da kanka "

ya tsaya yak'i tafiya yana kallonta kauda kai tayi tana dariya muryarsa asanyaye yace

"taso mana muje "

turo baki tayi

"nifa gsky sweet idan naje raka ka....."

da sauri ya sunkuya gab da ita ya rufe mata baki da hannunsa

"kin san in bakiyi min rakiya ba baxan iya fita ba,

na riga na saba da hakan kin sabar min babyna yi hkr baxan miki komai ba"

da mmk jannat take kallonsu watak'il ma sun manta da ita a wajan

shafo sajen fuskarta yayi

"kinga yanda sajen nan naki yake miki kyau ?"

far ta yi da ido

"oh ya Allah ! ta shi muje babyna"

kafin tayi motsi ya d'aga ta cak ya janyota gab dashi yana mata wani irin kallo me cike da tsantsanr soyayya

"muje akwai sak'on da xan baki na manta d'axu ban baki shi ba"

hannunta ta d'ora asaman kafad'ar sa tana girgixa kai

"bayan nasan wayo kake min wannan sak'on dai ne na....."

rufe mata baki yayi

" no ! babyna baki sanshi ba wannan sabon sak'o ne na musamman akayi shi saboda ke !"

yaja hannunta suka wuce tana dire diren kwafa na shagwab'a

gaf da xasu fita ya tuno ashe fa da anty jannat a falon

"antynmu sai nadawo anjima" ya fad'a yana dariya k'asa k'asa yana kallon sulthana data kwab'e fuska dan tasan rakiyar me xata haifar.

murmushi jannat tayi ranta fes tana jin dad'in kulawar da yake da sulthana kamar ya had'eta tana xaune takusa 1 hour sannan sulthana ta shigo da gudu tana dariya babu jan janbakin data shafa aleb'enta

da mmk jannat tace "lfy kike gudu haka duk kin hargitse?"

dariya tayi ta xauna

"hmmm ya haisam fa da kyar na kwaci kaina na gudo idan xan biye masa hmmm.."

"ina janbakin naki ?"

wata iriyar dariya sulthana tayi

"yana bakin ya haisam"

"laaa Allah ya shiryamin ke sulthana"

jannat tafad'a tana dariya

"wllh anty jannat ya shanye shi tass haisam fa !?"

suna cikin mgn sukaji muryar Rubayya cike da mmk suka amsa sun shigo ita da mijinta prince A.K Garkuwa da sauri sulthana ta k'arasa suka rungume juna cike da jin dad'i bayan sun saki juna Rubayyan ta rungume jannat suna murnar ganin juna xama prince A.K Garkuwa yayi fuskar sa d'auke da murmushi nan da nan suka fara hira sam sun manta da shi .

"oh ku kam mata gaishe ku idan kuka had'u sai Allah rubyna sam kin manta dani ko ? kin sami y'an'uwa"

da sauri ta matsa kusa da shi ya rik'o mata hannu suna kallon juna

" sorry sweeter ! ya xa ayi na manta ka nasan kana kusa dani dan hankalina na kanka "

mik'ewa yayi ya mik'ar da ita gab da juna
Chapter 80 · 0% Book details