← Book details Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 85

Sashe 41

Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da rana sulthana tana gardin dayake bayan babban kitchen tana xaune tana tuna rayuwar ta mai dad'i wanda ayanxu komai ya cab'e ta koma kamar ba ita ba tagumi tayi, duk irin gatan da umminta ta nuna mata ba ita ta haifeta ba hawaye ya sauko mata ta samu gata duk da kasancewar ta cikakkiyar Mara kunya umminta bata taba nuna mata wata alama ba, motsi taji a kitchen ta tashi ta lek'a ta jikin k'ofar baya ta hango jidda ta d'auko flast din abinci ta xuba sulthana na hangenta ta jikin wata Yar mitsitsiyar k'ofa da akayita dan lek'e, gani tayi ta fito da leda a hannunta ta xaxxge magani akan abincin, xaro ido sulthana tayi tana mmk ta rufe flast din ta bude loka ta ajjiye ta fito daga kitchen din tai b'angarenta da sauri sulthana tabi bayanta da niyyar ta nuna mata ta ga abinda tayi kafin ta k'arasa ta shige d'aki ta fad'a toilet

Cije yatsa sulthana tayi, dabara ta xo mata da sauri ta koma ta juye abincin acikin wani plate na daban ta ta wanke flast din ta xuba wani abinci ta mayar lokar da ta ajjiye ta fito tana mmk jikinta har rawa yake direct dakin momy ta wuce ta sameta xaune tana laxumi kusa da ita taje ta xauna tayi ta gumi,

Momy ta kalleta cike da kulawa, sulthana meyasa meki? Hawaye ya sauko mata, cikin kuka tace momy halin da muke ciki na masifa ma ya ishemu way'an cen mutane suna k'okarin kara jefamu cikin wata sabuwar masifar,

Atsorace momy tace wacce masifa sulthana ta share hawayenta ta kwashe abinda taga jidda tayi da yanda ta sauya abincin, tagumi momy tayi jikinta asanyaye,

Momy irin wad'an nan abubuwan sai dai nagani a novel ko a film yau na gani da idona, ina tsoran kada wani abu ya samu Anty jannat ita da ya khaleel kiyi wani abu momy,

Kwantar da hnklinki sulthana Allah ya fisu babu abinda xai faru bi'ixnillah zan kuma d'au gagarumin mataki abinda nakeso dake kada kifad'awa kowa sbd xaki d'aga musu hnkl zan Sa musu ido sosai daga ita har mahaifiyar tata kedai abinda nakeso dake ki cigaba da shan maganinki akan kari ki dage da addu'a kinji ko ? Ta mik'e naji Momyna inshaa Allah xan kiyaye asanyaye ta fice tana mmkin abinda ta gani ita kanta xata sawa jidda ido sosai tunda ta fuskanci inda suka sa gaba

**********

da safe bayan sungama breakfast jidda ta kalli momy,

mom banga ya khaleel yaxo yin breakfast dinshi ba,

da sauri momy tace eh jannat tashi ki kaiwa yayanki breakfast, had'a rai tayi dan ba haka taso ba ranta ya b'aci ta mike tai b'angaren d'akinta sulthana ta bita da kallo tana murmushin k'eta

a kunyace jannat ta shi ta d'auka tai b'angarensa sallama tai masa ya amsa hannunshi rik'e da laptop yana amfani da ita tana shigowa ta b'ata rai ta turo baki ita a dole fishi take dashi,

yaji dadin ganinta bata ran datayi yasashi murmushi ya xuba mata ido kusa dashi ta ajjiye flst din ta gaishe shi ya amsa yana murmushi ta cire hijab dinta ta xuba masa tea a cup ta mik'a masa ya amsa ta hada masa komai ta mike xata ta fi

" ina xaki tafi ?

bata waiwayo ba tace zan koma cikin gida ajjiye cup dinshi yayi ya janyo hannunta ya xaunar da ita,tana ta fusge fusge dariya ta bashi ya tallo bo fuskarta, fushin me kikeyi ?

ta juya ido ni ba fushi nakeyi ba,

haka kawai yaji yana son tsokanarta dan kawai tai masa yarinta any'a kuwa wannan jannat ce ? ya k'ura mata ido cikin wasa kodai sulthana ce ?

jannat din dana sani bata da tsiwa matsoraciya ce bata iya fada ba,

kallonshi tayi da sauri niba matsoraciya bace ta fada tana murguda baki, yayi murmushi me fidda sauti yana shan tea din ya ce idan jannat ce me ya sameki kwana biyu ?

ta kalli cup din hannunshi ta kara hada rai ni babu abinda ya sameni

hada ranshi yayi ya kalleta , ki fadamin meya ke damunki ?

kwana biyun nan narasa gane damuwarki, tun ranar da nai miki mgn akan ki fadi abinda kikeso ki huta da boye boye shine kike fushi,

ranta ya baci bata son wannan magnr ko kadan,

xuba mata ido yayi yana kallonta, ta dago kai ta kalleshi, kana son jin wanda nakeso ?

ajjiye cup din daya ke shan tea yayi yana gyada kai akufule tace,wanda nakeso ba shi na aura ba

kallonta yayi da mmk ta marairaice, ban aure shi ba kuma ina sonshi sosai,

kishi mai xafin gsk ya taso masa ya fincikota agabana kike fadamin kina son wani ?

xaro ido tayi tana kokarin kwace kanta,

tambayata kayi na baka amsa plx ka cikani sakin ta yayi, yana jin ba dadi aransa ta mike xata fice ya kuma fincikota, ya xare mata ido,kikace kina sonshi sosai ? kai ta daga masa atsorace

matseta yayi da jikinshi har sai da tayi kara ? dolene ki cireshi aranki baxaiyiyu ina aurenki kina son wani ba, ya saketa ta fice da sauri,

sai bayan ta fita yake jin haushin abinda yai mata kamar wani karamin yaro yake mata fadan ta cire wani aranta, tsaki yai shi sam bai son yayi hakan ba sbd kishin daya ta so masa, anya kuwa da gaske take masa ? idan kuwa har haka dinne xai san matakin da xau dauka dan yana matukar sonta yna kishinta

tana fita daga dakinshi ta waiwayo tana kallon kofar murmushi tayi ya khaleel kenan abinda kakeson ji baxaka ka taba jinshi ba idan har bakai kafara fada ba ta wuce tana jin dadin yanda lokaci daya tai nasarar cire masa wancen tunanin ta hau sama tai alwala tayi sallar walaha ta dade tana addu'a akan Allah ya kawo musu mafita na halin da suke ciki

************

da daddre momy ta fito daga dakinta xataje dakin dady giftawar mutun ta hango a k'asa taji tsoro ta dake da kyar ta lek'a abinda ta gani ya bata mmk ta kalli agogo 11:38pm da sauri ta shiga dakin dady tace ya xo yaga wani abu ya biyo bayanta suka sauko kasa da mmk yake kallon umman jidda magani ne a hannunta tana barbade falon dashi tsawa ya kwatsa mata ranshi ab'ace hadiza !! menene haka kikeyi ??

by

*Ummee Garkuwa*

[9:10PM, 12/8/2016] Fatima Garba:
'<Øûß
'<Øûß
'<ØûßJENNIFER
'<Øûß
'<Øûß
'<Øûß

67&68

a raxane ta dago kai ta kalleshi yana sauka daga stairs momy na biye da bayansa, menene haka hadiza ?

cikin yadda da abinda xata ce masa ta kalleshi ta marairaice yaya bashir akwai matsala,daxu naje wajan malamina yake fadamin yaran nan ba banxa suka barka ba sun maka asiri sosai kuma yayi tasiri ajikinka,ya fadamin ma xamansu cikin gidan nan babu alkairi ka koresu wannan maganin danake barbadawa shine makarin asirin da suka maka dan yace gidan nan xagaye yake da layun da sukai maka binne, kallon takaici yake mata kamar ya rufeta da duka yace,

meyake damunki hadiza ? meyasa kika bata kanki da wannan banxar rayuwar ? wannan wacce gurbatacciyar rayuwa ce kika dora kanki akai ? wanne irin asiri kuma ? yaran nan nina janyo su jikina basu suka kawomin kansu ba, ki dinka abu da tunanin me jibi xata haifar, kina da yaya xaki samu jikoki idan suka fada irin wannan rayuwar xakiso su hadu da hannu nagari shi alheri dankone mai shi yake bibiya,

da mmk take kallonsa, yaya bashir ka yadda da abinda nake fada maka kasan baxan cutar da kaiba ba xanso wani ya cuceka ba, tsawa ya kwatsa mata haushinta ya kamashi cike da kuluwa yake girgixa kai dan mmkinta yagama kureshi, bansan a inda kika samu wannan tarbiyyar ba dan iyayenmu ba irinta suka dora ki akaiba, wannan yaxama shine last kada kikuma shigomin da irin wannan karerakin ni ba mutumin banxa bane nasan me nakeyi kije ki tubarwa Allah muddin kina son xaman lafiya ki kiyaye, bana son karajin wayannan xantukan na karyar banxa da wofi, ya kalli momy ki fdawa yaran nan su wanke wajan nan gaba daya, ya hau sama momy ta tsaya kan stairs din tana neman nimbers din ma'aikatan gidan, ran umma abace tacewa momy idan kin hanashi karya tsubbinki anan baki isa ki hana wanda xanyi a bayan idonki ba ta gallawa momy harara tai bangarenta momy takira yaran cikin daren suka wanke falon

***********

washegari da safe momy xama tayi a kitcean tana kallon jidda da ummanta suna ta xirga xirga taki barin kitcean din har sai su suwaiba suka gama hada musu breakfast aka jeresu a dining suka hadu nan kowa ya karya banda khaleel dan tun xuwansu jidda bai fiya xama aci abinci da shi ba, bayan sungama tacewa jannat ta dauki nashi ta kai mishi tana kallon irin kallon takaicin da umma da jidda suke yiwa jannat a kunyace ta ratsa ta gabansu ta dauka tai bangarensa sallama tai masa ya amsa ya fito daga wanka jikinshi daure da farin towel dan karamin a hannunsa yana goge ruwan kanshi dashi, kallo daya tai masa ta kauda kanta ta ajjiye kayan ya karaso kusa da ita ya xauna ta gaishe shi ba tare da ta kalli inda yake ba ya amsa yana kallonta ta mike xata fita ya dakatar da ita,

"ina xaki tafi baki xuba min ba,

ta kalleshi kunya ta kamata sbd ba riga jikinshi ta sunkuyar da kai naga baka shirya ba, dawo ki xauna xanje na shirya tunda naga kina jin kunyar kallona, ya tashi ya shiga bed room dinshi tayi ajiyar xuciya ta cire hijab din ta xuba masa tea a cup da soyayyan dankali ta hada masa da plantains ya shigo falon nasa ya saka wando 3 quarter da riga me gajeran hannu ya xauna ta miko masa cup din ya amsa dayan hannun nashi rike da remote xai kunna tv shiru sukayi dukansu suna sauraron lbaran bbc a hankali ta mike xata fita ya riko hannunta ta fixge hannun ya kalleta yaga ta hada rai,

"fushin me kikeyi ?

ni ba fushi nakeba,
Chapter 41 · 0% Book details