← Book details Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 85

Sashe 47

Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jannat d'akinta ta wuce tana jin dad'in sunfara nasara akan makiyansu tunda har sunji sunan iyayensu matsalarsu dayace tayaya xa'a ga ched'en ? Dakinta ta shiga yaraf ta xauna gefen gadonta CHED'E ta maimaita sunan tun tana yarinya take jin sunan sosai Ashe mahaifinta ne gabanta ya fadi anya kuwa?

Xuciyarta na rawa akan haka babban mutun kamar wannan yarasa yayansa har uku ? Tayaya? Wannan lamari nasu da d'aure kai yake, tsoro ya darsu aranta SBD tunowa da gargadin osasa akan muddin aka San da xamansu cikin gidan nan akwai babban had'ari, hade kanta tayi da jikin bango tana runtse ido ranta ma suya xuciyarta na k'una bata da babban buri irin taji dalilin dayasa akewa rayuwarsu haka hawaye mai xafi ya sauko mata ta runtse ido, tana kiran Allah akan ya kawo musu d'auki,

Da yamma suna kitchen gaba d'ayansu dan su Jidda da iyayenta sun dawo daga unguwar da suka tafi bayan sunyi breakfast, bak'uwar

Mota ce ta shigo gidan,

Da sauri Momy ta saki murmushi ganin motar, matar ta fito, Momy tace jannat kunga kanwata hjy safiyya wacce muke uwa daya uba daya mu biyune kawai tana maid cen Maiduguri anan take aure, tunda ta fito daga mota ta saki fuska tana dariya da sauri Momy ta tashi suka rungume juna suna murnar haduwa falo suka wuce,

Bayan sungama girkin suka jereshi a dining suka xauna a falo Momy da kanwarta suna sama cen b'angarenta,

Da daddare har d'akin jannat Momy ta kawo Anty Safiyya ta rungume jannat y'ata amaryar babana ta ajjiye mata wata katuwar leda suka xauna gefen gado turarirrika ne irin humra masu Kyau da wasu kayayyaki Wanda jannat bata sansu ba, tana murmushi Anty Safiyya tace xan gyara y'ata kam dago fuskarki ki kalleni ni uwace kinji babu irin wannan kunyar,

Kinga wannan turaren wankane idan xaki shiga wanka ki xuba shi cikin ruwan wankan wannan idan kika fito daga wanka ki shafe duka jikinki, wannan na gashi ne,

Wannan na kayane, haka taita yi mata bayanin kayayyakin da suke cikin ledal harda sabulu na musamman Wanda ake hadawa sbd amare, kisaki jikinki jannat zan had'aki kafin lokacin da xmusha biki ubangiju Allah ya albarkaci aurenku Allah yai muku albarka, can cikin makoshin ta ta amsa da amin, suka mike suka fita tana fad'a mata akwai sauran kayan Wanda sai nan gaba kad'an xata fara amfani dashi, suna fita ta shak'i kamshin turarirrikan masu dad'i Dan gaba d'aya d'akin kamshinsu yake itakam tana son kamshi ta shi tayi ta shiga toilet ta xuba na wankan tanayi tana jin dadin kamshin da sabulun mai matukar kamshi bayan ta fito ta shafa sauran har na gashin kai tuni taji wani sabon yanayi, ko ina na jikinta na fidda daddad'an kamshi haka tayi bacci xuciyar gefe guda tass daya gefen firgicin yanda ratuwarsu take, karfe 3:00 ta tashi tafara nafilfili har asuba bata koma bacci ba sai da gari ya fara haske,

11:00 ta tashi taiwa wanka ta saka kaya material ne blue da kwalliyan silver ya karbeta Dan colour din skin tone dintane ta fito babbn falo ta hangosu xaune suna hira dukansu harda Anty Safiyya, yau kam ba umman Jidda da yan'uwanta ta gaishe su suka amsa musamman Anty Safiyya da kulawa take amsa gaisuwar kije kiyi breakfast kada yunwa ta lahantamin y'ata, murmushi jannat tayi ta k'arasa dining tayi breakfast, Momy tace d'auki na yayanku ki kai masa yau ma baifito ba, kunya ta kamata ta d'auka ta fita kanta ak'asa tak'arasa b'angarensa tai sallama tashiga d'akinsa ya fito daga wanka yana d'aure da towel ganinta yasa yasaki murmushi itama murmushin tayi ta sunkuyar da kai ta ajjiye kayan tana gaishe shi ya amsa yana kallon shigarta da tai mata Kyau ya karaso kusa da ita ya janyota jikinshi, yana shinshinar wuyanta yana jin daddad'en savon kamshin dayaji tanayi yarasa gane kalan k'amshin Dan ko ina na jikinta kamshin yakeyi, ya saketa yana mata wani kallo dan yau ganinta yake kamar ba itaba, kanta ta sunkuyar ya dago da fuskar, muje ki shafa min mai, ya janyo hannunta suka shiga bed room dinshi ta shafa masa man tana jin kunya shikam yana so ta saba dashi sosai Dan tarage jin kunyarsa, tana gama shfa masa suka hada ido tai dariya ta juya da sauri xata fice ta waiwayo, ka saka kaya ina jiranka a falo, ya bita da kallon sha'awa yana jin dad'i ya tashi ya shirya cikin shigarsa ta kana nan kaya top yasaka ash colour da blue black jeans ya fito ya sameta remote a hunnunta tana canza channel, ya xauna ta xuba masa breakfast dinsa yana yi yana kallonta yana gamawa, ya mike, tana kallonshi ya janyo hannunta suka koma bed room dinshi, tsoro ya kamata dan lokaci daya taga ya canxa mata janto jikinshi yayi, ahnkl yake mata mgn kamar rad'a, kalamai yake mata da wata iriyar murya dabasan yana da itaba yana shafar jikinta ya xame dankwalin kanta, yannu yasa ya xuge xif din rigarta, gabanta ya fadi ta janye jikinta da karfi,

Ya kalleta da idanuwansa suka fara canxa kala,

No ! No ! Jannat plx nagaji da dauriya, jikinta ya fara karkarwa dan wani irin xaxxafan kiss yake mata cikin wani yanayi, yana maganganu, ina sonki jannat ina son kamshin jikinki, yafara haukata ta da wani Salo na daban tafara mayar masa da martanin kiss din daya ke mata,

kmar ta tunxirashi, ya fara wuce xatonta, tayi tayi ta kwace kanta ta kasa, tasaka masa kuka agigice dolenshi ya hkr dan bayason jin kukan ko kadan haka ya rungumo ta jikinshi yana shafa bayanta tana ajiyar xuciya, ta mike ya kuma rukota, beautyna kada ki rabani da lallausan jikinki plx ya maida ta jikinshi yana jin kamar ya maida ita cikin cikinsa sun dade a hakan da kyar ya kyaleta ta fito tana jin tausayinsa,

Washegari dady ya tarasu a falonshi na sama dan shida kansa yake b'oyewa bayasan rigimammin k'annansa su San abinda yake faruwa, ya kallesu dukansu,

Zantafi Abuja munyi waya da Alhaji Nasir ministern man fetur xamu hadu da President dan shi kadaine mutumin da xai iya ganin Adam ched'e bata re da wani shamaki ba cike da murna suke masa addu'ar Allah ya dawo dashi lfy yaji dad'in yanda yaga sunata nishad'i sosai mahboob ya kaishi airport ya wuce abuja yana tabbatarwa da kansa samun nasara

Yana sauka ya hadu da drivern Alhaji nasir ya kaishi gidansa suka tattauna Dan amininsa ne tare sukayi kuruciya bayan sungama suka tafi wajan President sbd yasan da xuwansu kai tsaye gidanshi suka wuce suka sameshi a falonsa na musamman da yake saukar baki way'anda suke da muhimmanci,

Yana ganinsu ya saki murmushi, Dr bashir rabona dakai shekara shida kenan kullum kana nan a yanda kake, dariya dady yayi yabashi hannu suka gaisa bayan sungama gaisuwa, President ya kuma kallon dady,

Dr bashir meyasa kaki yadda da shawarata? Siyasa ta dace dakai danshi mulki yana neman mutane irinka masu adalci ina fata xuwan nan dakayi kaxone dan ka fada min ka yanke ahawara xaka shiga siyasa Dan ka kwatowa talakawa yancinsu ?

Girgixa kai dady yayi dan sam bai son xancen ya kalli President ba wannan bane ya kawoni ina son wani taimakone,

Da mmk President yake kallonshi yanxu bashir dan kana son abu awajena sai ka kirashi da taimako? Murmushi dady yayi, ina son kai min hanyar da xanga Adamu ched'e

Ajiyar xuciya President yayi yana jinjina kai yai murmushi yana kallon dady,

Ni kaina rabon dana Sa ched'e a idona na manta shima irinkane ba ruwanshi da yan siyasa tsakanin mu dashi idan muntashi kanfen mu kirashi awaya mu tambayeshi kudi ya bamu muyi canfen dashi waya kwai xamuyi yasa aturo mana wani xubin ma ko ka kira wayan yaransa ke d'agawa ganin ched'e ba karamin babban aiki bane yanxu xakaji cen gobe ka jishi acen,

By

*Ummee Garkuwa*

[11:56AM, 12/13/2016] Fatima Garba:
'<Øûß
'<Øûß
'<ØûßJENNIFER
'<Øûß
'<Øûß
'<Øûß

75&76

By

*Ummee Garkuwa*

Dafe kanshi dady yayi Sam bahaka yaso jiba, ya kalli President fuskarshi da damuwa,

Yanxu ba yadda xa,ai mu hadu kenan?

Jim President yayi eh to akwai wata tattaunawa dana keso muyi dashi kasan shi Idan kana son ganinsa sai ta hanyar taimako akwai wani filinshi ana cikin abuja Ina son ya bamu filin xamu gina gidan marayu, akan hakan xai iya xuwa kasan shi adaline yana taimakon marayu sosai, damuwar shine vana tunanin xai xo da wuri sbd baifi 3 weeks da barin 9ja ba yaxo kano shida iyalinshi, dan ministern tsaro ya fadamin cewa ched'e yana son abashi mutanen da xasu masa tsoro, da sauri dady ya kalli President, yana tuna lbrn da jannat ta bashi na taga wata mata tabbas duk yadda akayi matar tana da alaka babba da jannat din,

Kayi hkr bashir xanyi waya dashi Adam ched'en duk yadda mukayi xakaji ka jirani nan da 3 dys,

Dady yace bakomai xai jira suka cigaba da hirar yau she rabo,

Bayan kwana 3 din suka dawo wajan President, yana ganinsu ya girgixa kai,

Su ka gaisa,

Bashir kaga abinda na fada maka ko ?

Wllh babban yaronshi ya turo wai duk abinda xa ai ga shi nan ya turo wakili ayi,

Dady ya girgixa kai shima ranshi ajagule bai so haka ba a daddafe suka gama hirar da President ya dawo gidan shi na abujan yana jin takaici kala kala bai son wanne kalan rarrashi xaiwa yaran nan ba tunda ya taho safe da rana cikin kiranshi suke duk sun kagu ya furxar da iska xuciyarshi ba dadi, baiyi tunanin haka abin xai cabe ba, kafin asansu an wahala anganosu kuma xa a kuma shan wta wahalar ? Ya rabbi, Allah kawarware mana wannan hadin Allah ka haka yai ta addu'a yana tnanin yanda xaije wa da iyalin shi wannan maganar Mara dadin ji

Bai kwana ba sbd ji yai garin ya isheshi jirgin yamma yabiyo ya dawo gida suna ganinshi suka taso da murna da jindadin ya kallesu tausayinsu ya kamashi kamar yai musu kwalla tunanin shi wanne irin yanayi xasu shiga in sukaji cewa ba a dace ba,
Chapter 47 · 0% Book details