← Book details Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 85

Sashe 17

Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari bayan yan gidan sungama cin abincin rana Jennifer ta fito tana kwashe kayan tana kaisu kitchen dukansu yan gidan suna babban falo kamar ko yaushe suna hirarsu ke ! Taji muryar ya khaleel yana kiranta ta tsaya cak zonan da sauri tai cikin falon ba wanda ya kalleta sai Momy key ya mika mata shiga dakina ki dauko min jakar akwatina ta amshi key din ta fara tafiya taji Momy nace mishi time fa ya kusayi katashi mana tafice dakinsa ta nufa a hargitse ta tadda dakin ta sunkuya ta sunkuci jakar tafito ta taddasu atsaye jikin motocinsu ta ajjiye jakar tana miko masa key din nop ki koma ki daukomin dayar guda biyu juyawa tayi ta koma ta dauko dayar har ya shiga mota shida Jidda suna baya driver na gaba dayar motar kuma Rubayya ce zahra na kusa da ita Momy ta kalli Jennifer ko xaki bisu shiru tayi tana murmushi jeki ki dauko gyalenki kiyi musu rakiya jiknta asanyaye ta je daki ta dauko gyale ta shiga bayan motar da Rubayya take ja suka bi bayan motar su ya khaleel

Bayan sun je airport din Jidda na zuba masa shagwaba ta rike masa hannu har time din da akai kiransu tasa kuka ya tsaya yana kallon fuskarta yasa hannu ya goge hawayen da ke xarya a fuskarta kiyi hkr plx 1 week kawai zanyi zan dawo tarike masa hannu biyun duka zanyi missing dinka sosai a wannan week din sannan tasaki hannun kallon Jennifer yayi ke ! Xo ki dauki jakar nan kibiyo ni da ita turuss gaba dayansu sukayi suna mmk da sauri Jidda tace bari na daukar maka a a ajjiyeta tamiki nauyi ganin ba wasa a fuskarshi yasa ta ajjiye jakar da tai saurin dauka sbd yace na dauka hannun Jennifer na rawa ta dauka tabi bayanshi yayin da suka rakata da muguwar harara sunyi tafiya sai da suka xo dai dai wajan da ba dama Jennifer ta shiga ya tsaya yana kallonta murmushin mugunta ya watsa mata da sauri ta sunkuyar da idonta tana son gane fassarar murmushin ke ! Yace mata kina da abinda xakice ?? Tayi shiru tana juya tmbyrshi dan tarasa gane kanta kina da damuwa ne ? Ya kara tmvyrta muryrta na rawa tace bani da abinda xance bani kuma da wata damuwa murmushin mugunta ya kumayi hade da cije lebenshi na kasa ya sunkuya ya dauki jakar da ta ajjiye yai gba tana waiwayo taga duk sun xuba musu ido gabanta ya fadi Takara so kusa dasu dukkansu suka bita da kallon tuhuma mota suka shiga Rubayya na xaune wajan driver zahra na kusa da ita Jidda ta bude baya ta shiga Jennifer ma bayan ta shiga Rubayya taja motar Jennifer Jidda takira sunanta naam ta amsa tana jiran tuhumar daxatai mata menene tsakaninki da khaleel? shiru tayi tana jinjina tmvyr Rubayya ce tai mgn muryarta asanyaye haba Anty Jidda menene kuwa a tsakaninsu ?? Kintaba ganin wani abune sabanin yau ? Mgn ake miki kibamu amsa! zahra ta kwasa mata tsawa Jidda ta kalli Rubayya datake tukin mota bantaba ganin wani abu kuma fatan ganin koma menene in dai akan ya khaleel ne me kuke cewa bayan kunbar kusa damu ? Shiru Jennifer tayi dan tarude tarasa amsar bata inbanda hawaye dake xubar mata a a va kuka nace kiyi ba amsa xakibani tsaki zahra tayi dama munafuki saurin kuka gareshi kin fiya shishshigi kitsaya matsayinki na Yar aiki kibar ganin kinxo gida da manyan matasa samari kyawawa dukkansu bavu sa'anki ke bari kiji gaba dayansu suna da yanmatan da xasu aura koya mahboob din da kike shishshige masa yana da wacca xai aura mufeeda Yar gidan ambassador na India in banda kwadayi ina ke ina xuri'armu ? Kibani amsata malama kar xuciyata ta fashe Jidda ta fada cikin tsawa da daga murya dabara ta fado mata cikin muryar kuka tace cemin yayi na dinka gyara masa daki ina karkadewa baya son ya dawo yaga yayi kura ko datti Hamdala Jidda tayi Rubayya tace shiyasa zargi bashi da amfani kunji ko ? Hankalinku sai ya kwanta dafa kafar Jennifer Jidda tayi kiyi hkr ina son ya khaleel fiye da tunaninki ban taba ganinshi da mace ba sbd yanda halinsa yake na rashin damuwa da mace ganinshi danayi dake naji takaicin da ban taba ji ba kiyi hkr tsaki zahra ta ja meye abin bada hkr ? Warning xaki yi mata ta fita sabgar mazan gidanmu dan masu ajine babu irinta bankiba ko mai gadi ko danjuma driver ya isa haka zahra Rubayya ta katseta mgn ta wuce tsaki zahra ta kumayi plx Anty Jidda mikomin air freshener na kusa dake warin rashin sarki ya dameni ta mika mata tafeshe motar dashi Rubayya ta kunna wakar India tana ji tana bin wakar hade da kyada kai alamun tana son wakar hawaye ya saukowa Jennifer ta runtse ido tana mmkin yan gidan wasunsu masu kirki wasu marasa kirki

By

*UMMEEYY*

[7:22PM, 12/5/2016] Fatima Garba:
'<Øûß
'<Øûß
'<ØûßJENNIFER
'<Øûß
'<Øûß
'<Øûß

29&30

Suna shiga gida daki ta wuce xuciyarta na kuna akan abinda zahra tai mata wai tana warin rashin tsarki girgiza kai tayi ita tasan Kristen ce ita amma tana kula da kanta asalima tasha taji ance bata kama da yare why zahra take mata haka ?? Tayi imanin babu abinda zahra ta fita na kyawun jiki asalima tasan tafita kyan fuska dana jiki harda na hali tunda ita bata kyamatar dan adam a kitchen ta yaradda Suwaiba tana aiki takusa gamawa Jennifer tasa hannu suka fara aikin suwaiba ce ta kalli Jennifer cikin kulawa Jennifer anya kuwa kina lfy ? Me kika gani ?? Naga ba haka kika fitaba kin fita cikin farin ciki kin dawo da bacin rai ko dai sun miki cin mutuncin da suka saba musamman zahra wllh ina gida ina addu'ar Allah yasa Ku rabu lfy dan wulakancin zahra ba Wanda ta bari hawaye ne ya saukowa Jennifer suwaiba ta fadi sunanta cikin muryar kuka shin Kristen awajan wasu ba mutun bane ??baxan iya cewa duka ba amma acikin kalilansu ina samun cusgunawa da wulakanci sosai durkushewa tayi awajan sakamakon kuka dayaci karfinta meyasa baxasu fahimta bane ? Baxasu fahimceni ba ina cikin matsala suwaiba matsalar dana ke ciki ta wuce tunani dan ta daukan rai ce ! Ta rushe da kuka suwaiba ta xaro ido cikin mmk tace bangane ba Jennifer ?? Ta daukan rai ? daga mata kai tayi tana goge hawaye karbar musulinci dai dai yake da daina numfashina ! Subhanallah suwaiba ta fada babu mai kashewa ko rayawa sai Allah kada wannan ya firgita ki kar ya baki tsoro girgixa kai takumayi tana cigaba da kukan suwaiba baxaki gane bane akwai abubuwan dana ke jira da lokaci yayi zan yankewa kaina hukuncin daya dace ta mike da ga durkutsan datayi zahra ta cimin mutunci sbd suna ganin kamar akwai wani abu tsakani na da ya khaleel xare ido suwaiba tayi cikin mutuwar jiki dan Jennifer ta bata tausayi kiyi hkr kin San kowanne mutun da kalar tunaninsa da kuma imaninsa wasu gani sukeyi kamar su na daban ne da Allah ya haliccesu da baiwa irin tasa ko dukiya Kyau ko wata baiwa su kam me xaisa suyi tunanin wani abu tsakanin ki da shi ? Hawaye na bin fuskarta ta ce sbd son xuciya me ya khaleel xaiyi dani ? Nifa Kristen ce abar kyamata sannan ba Yar kowaba mamana abinci take siyarwa ta kuma fashewa da kuka son xuciyane yasa sukai tunanin haka bayadda xa ai ya khaleel me ji da kansa me son addininsa ya iya jina aransa shi din sai manyan yara irinsu Anty Jidda tsarinsa da haduwar Sa Sam ba irin tawa bace takarasa mgnr da kuka kiyi shiru Jennifer ba Wanda yafi wani acikin halitta sai mai tsoron Allah kada kisa hk aranki yai miki tasiri komai yana iya faruwa hukuncin Allah yana sauya komai suwaiba jennifer ta kira sunanta kiyi shiru plx yarenmu ba daya ba haka ma addininmu amma ina jinki kamar yar'uwata nasan Ku musulmin kun San girman alkawari toh alkawarin ne xaisa na fada miki abinda ya khaleel yake min yana yawan tsareni da tmbyr ina da damuwa ? Ko ina da abinda zance musamman lokacin dayake waya da Anty Jidda me yake nufi ?? Tasa hannu da share hawayen da ya xubo mata ina son ya khaleel suwaiba ta xaro ido amma koda soyayyarsa xata kasheni baxan taba fada masa ba sbd ruwa ba Sa an kwando bane yafi karfina ina ganin hakan yagane a tattare dani shiyasa yakemin tmbyr nan dana dauketa ta rainin wayo duk da nasan babu aibu a addininmu mace tace tana son namiji amma shi tunda ya nuna haka yake son yaji na furta tokam baxai taba ji ba matsowa suwaiba tayi kusa da ita nikaina Jennifer na fuskanci akwai abinda ke son faruwa tsakanin ki da shi musamman yadda ba ya iya cin abincin kowa sai naki duk yawan ma'aikatan gidan nan ba yadda kowa ya shiga dakinsa sai ke ciki kuwa harda kannansa hakan yana daure min kai lallai kam yana ganin soyayyarshi a wajanki shiyasa yake miki wannan tmbyr ruwa ba sa'an kwando bane ya khaleel kam hakimtaccen namijine basarake me ji da gayu da miskilanci da Kyau da kuma aji da wayewa ko ba'afada ba ansan yafi karfinki mutumin da mgn ma cikin kasaita da isa yakeyinta babban kyawun halinsa shine baya wulakanta kowa to Harkan mutum ma bai shiga ba bare ya wulakanta ka hakane suwaiba zan cireshi araina duk Dana San da kyar in xai ciru addu'a xaki tayani zo mutafi daki tunda mun gama
Chapter 17 · 0% Book details