← Book details Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 85

Sashe 23

Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Shiru yayi yana kallonta dan shi Sam bai yadda ba ita bace bace wayar shi ya ciro ya kira mahboob bata dade tana ring ba ya daga yace dan Allah mahboob hadani da Jennifer zan sata wani aiki gata ma muna tare a kitchen ya mika mata waya atsorace ta amsa ya rasa mai zaice da yaji muryarta tabbas itace ya kalli hindatu datake gabanshi ya kuma saurari muryar Jennifer da kyar ya saita kanshi yace ta dafa masa indomie yana nan tafe ya kashe wayar ya kalli Hindu tai murmushi kadan yasaki numfashi ikon Allah Allah mai halitta kin San wani abu ? Kai ta girgixa dai dai da maganar Ku iri dayace ba banbanci yanxu ya kikeso ayi ? Ina so duk yadda xa ai yanxu ka kirata taxo nan office dinka muga juna kamata yayi kitashi muje gidanmu kai ta girgixa masa koda zanje gidanku to ba yanxu ba kai tsaye numb din Jennifer ya kira ta daga atsorace yace taxo xata rakashi kasuwa akai kayan matan da yake son siya amma a office xata sameshi yanxu yanxu danjuma ya kawota ganin cewa a gaggauce yace yaxo yasa ta fito da sauri ta fada wa danjuma ya dauketa suka taho

****** *******

Basa bata lokaci ba suka iso yace danjuma ya juya ita kuma ya shigo da ita a tsorace take dan gani take kamar wata muguntar ya shirya mata ta ga mace axaune amma bata ga fuskar ta ba sai da taje gab da ita ta saci kallonta karaf suka hada ido a kidime suka mike lokaci daya suka mike hade da kurawa junansu ido Jennifer ta nuna ta da yatsa wacece ke ? Hawaye ya xubowa Hindu tace wa haisam kayi namijin kokari Dole ka kasa tantanceni da wannan halittar Alhamdllh lallai wahalata taxi karshe ki karemin kallo ni Yar uwarki ce rungumeta tayi ita dai Jennifer mmk da ta ujjubi ya hanata mgn ta xauna jikinta na karkarwa Hindu tace dole ki kasa mgn tashi muje ki nuna min iyayenmu abakinsu xamuji komai haisam ya mike gsky kam.dan al'amarin naku akwi son jin dalili gaba dayansu suka mike itakam Jennifer binsu kawai take har suka shiga mota dake haisam yasan hanya kai tsaye ya hau titi Hindu ta kalli Jennifer kinki mgn ta kawo wani gwauron numfashi sannan tace mmk ne ya kamani ban taba tunanin haka ba sai ga shi na ganki wllh babu wani abu daya banbantani dake axahiri sai dai ko abadini nayi mmkin wannan ikon Allah ni kaina banyi tunanin tsananin kamarmu dake takai haka ba dai dai da murya fa ko ba'a fada ba ai ansan mu yan uwan juna ne haisam ya tsaya dai dai kofar gidansu Jennifer kai tsaye cikin gidan suka shige a daki suka tadda Maman David ita da papa da David da yake kwance akan cinyarta da gudu Jennifer ta karasa hade da fadawa jikin Maman David da oyoyo my jenny su haisam suka karaso shida Hindu araxane Maman David take kallon Hindu murmushi tayi hindun ta shigo Jennifer ya nunawa mama Hindu mama dama mu biyu kika Haifa ? Ya akayi baki taba fadamin ba fata rai tayi ke kadai na Haifa wannan ban Santa ba sam papane ya kalli Hindu da mmk yace wannan wanne irin kama ne ? Mikewa mama tayi me kuka xo yi ?, tacewa haisam kuna son sawa yata wani irin tunanine ? Dama sam hnklina bai kwanta da yin aiki a gidanku ba Ku tashi Ku fita ni yata ita kadai na Haifa bansanki ba ke ta nuna Hindu hawaye ya saukowa Hindu ko baki fada ba ni nasan ba ke bace uwarmu hannu tasa cikin riga ta xaro karamar bindiga ta nuna kan David ko ki fadamin gsky kona kashe ramammen dan nan naki kuka mama tasa plx karki harbeshi haisam ya mike Hindu kibi ahnkl kada ki harbeshi idan har bata fadi gsky ba kashe shi zanyi inkashe wancen mijin nata me kwala kwalan ido jin an ambaci papa yasa yace ko baki harbemu ba dole gsky tai halinta kuka Jennifer tasa kina da hnkl dan sunce ba iyayenki bane shine xaki kashesu ? Yimin shiru ! Hindu ta kwatsa mata tsawa ba iyayenki bane papa ya mike ina zaka hindu ta fada tana Nunashi da pistol din hannunta ya daga hannu sama zan dauko muku wata shedane yana ina ? Ta tmby shi yanuna wani tsohon akwatunshi haisam ya tashi da Kansa ya dauko papa ya bude jikinshi na rawa ganin anbude akwatin yasa mama rushewa da kuka wata leda ya dauko acikin akwatin ya xaxxageta kayan jarirai na sanyi da wani karamin dankunne da awrwaro na gwal suka fado sai envelope ya ciro wani karamin pix tabbas Jennifer Yar uwarki ce dan gashi nan a pix din da muka tsince ta ya mika mata pix din ta kalla hawaye ya sauko mata duk wayan nan kayan ina da irinsu ya akayi ka tsince ta ??,

Yana rubuce ranar talata a shekara ta 1995 watan July anan garin KANO a unguwar janbulo da safe muka tadda an ajjiye ta agefen bola dai dai kofar gidanmu nacen jikinta dauke da wannan kayan kunnanta da wqnnan barimar hannunta sanye da wannna awarwaron sai wanna envelope din aciki ansaka wannan pix din da kuma takaddanta na haihuwa wannan ranar ta nuna watan ta daya da kwana goma cif rushewa da kuka sukayi dukansu hindu da Jennifer ita hindu tana kukan bakin cikin wannan ramari cikin kuka tace rana daya aka wullar damu hannu tasa a aljihu ta ciro barima irin ta Jennifer da awarwaron sak iri daya sauran kayan suna cikin mota itakam Jennifer kukan tarasa gane kanshi babban bakin cikinta bata San wace rayuwa xata faraba da mmk papa yace kina nufin kema wullar da ke akayi ? Kai ta daga masa tabbas ina so kubani yar uwa ta muje mu binciki asalin iyayenmu papa mungode da taimako Jennifer ta tsaya da kukan ngd iyayena har gobe Ku iyayene kuna raina amma kuyi hkrin rashina na wani lokaci lokaci daya naji ina son ganin aslin iyayena dole zanbita baxan iya xama da wannna daukin ba takarsa da kuka mama kukan takeyi nabaki goyon baya jenny Allah yabaku Sa 'a hindu ta mike haisam ya mike xuciyarshi cike da tausayinsu Jennifer fa ma mikewa tayi tana kuka mama xan dawo nan da kwana 2 tafice da sauri tana kuka suka shiga mota gaba dayansu

****** *******

Haisam ya ce ina xamu hawaye na sauka a idon hindu tace gidana dayake cikin hotoro g.r.a ya ce ita kuma Jennifer fa ? Shine ban San ya xamuyi ba muje cen din ma yanke shawarar yadda xa ai basu bata lokaci ba suka iso kai tsaye falo suka xauna dukkansu jikinsu asnyaye Jennifer tace ta ina xamu fara Neman iyayenmu haisam yace wai Hindu wacece wannan matar dana ganki da ita a saudiyya? Tai masa wani irin kallo saudiyya ??ta maimaita yes ya fada yana kallonta ko bake bace sulthaana ? Araxane ta mike cike da jin dadi bani bace Alhamdulillah bani bace shikenan wahalar mu ta yanke iyenmu nacen duk yadda akayi matar nan itace mahaifiyar mu ikon Allah haisam ya fada tabbas kuwa dan akwai sulthana ban da yanxu kince min ba ke bace baxan taba yadda ba dan yanda kuke tsananin kama da Jennifer haka take da Ku itama Jennifer dadi taji ya kamata yanxu ya xa ayi muje saudiyyan ni in kun yadda ma gobe muje kai haisam ya girgixa mata baxaiyiyu gobe ba nan da 1 week dai haisam plx hindu ta fada xuciyata tana cike da kwadayin son ganin iyayena ki kwantar da hnklinki dolene sai munyiwa Jennifer biza cikin satin nan dai ajiyar xuciya Jennifer tayi haisam ya kalleta yanxu wqcce shawara kuka yanke ?? Tame ? Suka tmby shi Jennifer mana anan zan barki a a ya haisam tare xamu koma gida dan bana son kowa yasan wannan zancen har sai mungama iyayenmu plx ka rufa min asiri murmushi yayi bakomai gobe gobe zansa a fara miki shirye shiryen tafiya ya mike yana kallon Hindu kefa kutafi Ku barni anan dan bani da wata matsala suka wuce a cikin mota Jennifer ta dake ya haisam ina son tmbyrka ? Wai shin ya akayi haka ta faru ya kwashe komai ya fada mata ta fashe da kuka yana rarrashinta har suka so gida

*******************
Chapter 23 · 0% Book details