← Book details Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 85

Sashe 30

Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

khaleel ? Yakira sunanshi, khaleel ya kuma maimaitawa a tsorace yata bashi hade da girgixashi khaleel ! Da kyar ya iya bude ido ya kalli dady, cikin raxana dady yace meya sameka ? Kirjina dady yana min xafi ina jin xuciyata kamar xata fito, subhanallah khaleel ! Sbd me ? Yanxu yanxu fa lfyr ka kalau, mikewa khaleel din yayi tamkar xai fadi dady natafi daki zansha mgn da kyar ya iya mgnr,

Dady binshi yayi da ido yana mmkin ciwon nashi yanxu yanxu ace ana tunanin xuciya kamar xata fito ya salam ! Meya sami yaron nan farat daya haka ?? Haka ya cigaba da tunane tunane ko xai danko dalilin cutar babban nasa daya keso tamkr namaa tsoka daya a miya

*************

Kai tsaye dakinshi ya wuce shi kadai yasan yadda ykeji aransa abude ya tadda dakin ya shiga ciki a wahalce ya xauna kan 3 siter dinshi sai da ya xauna sosai sannan ya kula da sagir daye xaune yana kallonshi,

Sagir ! Yakira sunanshi, ya cije lebenshi xan rasa jenny ta,

Xaro ido sagir yayi, cike da mmk yace ban fahimta ba khaleel, da kyar khaleel ya bude baki cikin wani mugun yanayi na bakin ciki da bacin rai,

Dady xai bawa mahboob auren ta,

Subhanallah ! Sagir yace sbd me ? Ya tmby khaleel din daya runtse ido yanajin kansa kamar ana cakamasa kibiya, sbd yace tasu tafi xuwa daya,

Da mmk sagir yace to khaleel yanxu meye abinyi hnklina yatashi nikaina bana so karsa jenny, tsaki sagir yayi duk kai ka janyo wannan tashin hnklin taurin kanka ne yajamaka,

Kwfa khaleel yayi bana son fda plx kabarni naji da abinda nakeji shi kadai ya isheni, idan narasa jenny narasa dukkan farin ciki na rayuwata bana jin xanyi aure, dan konayi wacce na aura baxata taba jin dadin xama dani ba, kallonshi kawai sagir yakeyi dan ya kasa mgn, ina son jenny naso na aureta na reneta na bata ilimi ta goge da rayuwa har xuwa lokacin daxata mallaki hnklin kanta yanda xata iya rayuwar aure dani, da inaji ajikina jenny ta wace, yanxu tana so tafi karfina tayaya dady xai gane jenny itace mahadi na farin cikin rayuwata ? Dafe kansa yayi cikin mayuwancin hali har abada bazan daina son jenny ba,itace macen dana kalleta yanayi na sauya ita kadaice macen dana fara so har nake tunanin rayuwar aure da ita sagir kasan ya akayi jasan Jennifer?

Girgixa kai sagir din yayi,

Kwanciya khaleel yayi hade da tsirawa cillin din dakinsa ido

Ranar lahadi ne da yamma Momy ta ce ya kai wata abu Yar aikinsu kasuwa xatai mata siyayya bayan sunje yai parking dai dai bakin kasuwa wajan kofar gidansu inda mamansu take sai da abinci yana xaune cikin mota ya hango baban avokinsa da ya rasu xaune cikin rumfan murmushi khaleel yayi dan mutumin yana da matukar kirki tun suna yara abokin nasu ya rasu amma khaleel bai manta da shi ba dan yana xuwa gaishe ahi lokaci xuwa lokaci futawa yai daga cikin motar yana sanye da wando 3 quarter da riga maroon ta dan kamashi kadan hannun shi rike da mukullin mota yayo rumfar wajan Baban abokinsa ganinshi yasa mutumin yin dariya hade da fadin sunanshi, khaleel d'ana kana duniya ? Dariya shima khaleel din yayi hade da sunkuyawa baba barka da yammaci,

Yawwa khaleel tashi ga benci nan xauna ya gida ya aiki ya iyayen naka? Mikewa yayi ya xaune hade da fadin suna nan lafiya baba,

Mashaa Allah khaleel har yanxu dai ba iyali ko ?

Kai khaleel ya sunkuyar hade da murmushi ankusa baba,

Af kullum amsar kenan ankusa ba, to ubangiji Allah yasa,

Khaleel ya amsa da amin

Shiru Baban yayi, duk lokacin Dana kalleka sai na tuna da khamis, Ubangiji Allah yaji kanshi da rahma,

Amin baba,

Karasowa tayi tai musu sallama suka amsa kan khaleel akasa bai kalleta ba ta mikawa baba plate na abincin daya siya ta juya xata tafi baba ya kirata, Jennifer xo ki tambayi khaleel me yakeso? Dago kansa khaleel yayi suka hada ido gabanshi yaji ya fadi da karfi wani abu yaji yam tundaga kansa har dan yatsan kafansa da sauri ya sunkuyar da kanshi muryarta yaji me matukar dadi, me xa'a kawo maka ? Girgixa mata kai yayi hade da kara kallonta mmk sosai abin yabashi ganinta yayi adire kyakkyawa Sam batayi kala da sunanta ba aslima shi yafi ganin kamarta da Hausa fulani a hnkl a hnkl gaban nashi ya rage faduwa mmkin kansa yake baba na cin abinci yana mishi hira shi kam hnklinshi nakan sabon sauyin daya samu kansa ciki bai taba kallon mace duk kyanta da tsarinta yaji wannan yanayin yanayi wa mutane kwarjini yau shi akaiwa kwarjini yarinya karama hnkl ya kallo bangaren da take xaune akan benci cikin runfar nesa dasu kadan karantar yanayin da ta ke ciki yayi sbd ya karanci sanin yanayin halayyan dan adam tana da nutsuwa sannan tana cikin damuwa haka kawai yaji tausayinta ya kamashi, kwala kiran sallah akayi, araxane yaga ta kalli inda kiran sallar yake fitowa gaba daya ta bada nutsuwanta akan sauraren kiran sallar mmk sosai ya kama khaleel bai tsure da mmkinta ba sai da suka debi ruwa arumfar tasu shida baba suka fara alwala kura musu ido tayi tana kallon alwalar kana gani kasan alwalar birgeta tayi jinjina kai khaleel yayi ya mike Abu ya hango ta nufosu tagama siyayyar yace ta shiga mota ta jirasu xasuyi sallah xuciyar cike da mmkin yarinyar da kuma tunanin son taimakonta suka shiga masallaci

Bayan sun idar da sallah sun fito shida baba ya kira Jennifer xai biya kudin abincin daya ci da sauri khaleel ya xaro kudi ya tambayeta nawane kudin tace 500 ne ya bata 1k ta tafi kawo masa changy yace ta barshi baba yai gdy shikuma khaleel din ya shiga mota dai dai lokacin da Maman david takara so wajan baba Jennifer tace wai a bar changy? Gyda kai baba yayi bani na biya ba khaleel ne dan gidan Dr bashir na g.r.a xaro ido Maman David tayi, hee ! Baba meyasa baka kirani nayi gaisuwa ba ? A kamfanin babansu fa Baban David yake gadi kamfinsu na takalma ai mutanen kirkine baba, Allah ya saka angode ta wuce tana mmkin ganinshi ana sbd tasan dan manyan mutane ne

*****************

Wasa wasa kullum khaleel ya xauna bashi da aiki sai tunanin yarinyar nan ba yanda baiyi ba ya share ya kasa da kyar akai 1 week da kyar ya samu ya xakulo dabara sbd yaji daxu Momy tana anemo mata Wanda ya iya girki kafin bikin Abu yaxo da yamma ya shirya ya nufi unguwarsu kai tsaye rumfar Maman david yaje bai samu Jennifer anan ba sai Maman david din yatarar ga mamakinsa yana xuwa yaga Maman David da sauri taxo wajanshi dan ta ganeshi sannu da xuwa oga amsawa yayi sannan ya xauna ta gaishe shi da girmamawa ya amsa shima tace me xa a baka yayi Jim ya dago kai kenan ya hango almarai ya dan saki numfashi ya xaro Damin kudin ya mika mata abawa wayen cen almajiran da murna ta amsa bayan ta raba musu duka abinci ta kawo kudin wai sunyi yawa yace ta barshi da murna ta fara gdy ta xauna nesa dashi kadan ta hau surutu ai oga Allah yaska muku da alkairi irin taimakon da kukeyi megidana ma a companyn Ku na takalmi yake gadi ajiyar xuciya khaleel yayi dan yasamo mafita yayi murmushi kadan bakomai akwai mgnr dana keso muyi gyara xama tayi inaji,

Sunana khaleel Dr bashir,

Bude baki tayi da mmk Kaine khaleel ?

Daga mata kai yayi

Momyna tana son Yar aiki wacce xata dinka yi mata girki ko kina da wata hanya daxaki mata naga kin iya girki sosai,

Washe baki tayi cike da murna sosai ma oga khaleel ina da hanya dan ina da y'a Jennifer itama ta iya girki sosai, Hamdala khaleel yayi cike da jin dadi, OK amma kafin nan naga cen gabanku kadan sun bude catering skul ko ? Inaso taje cen tayi training na 3 months kafin tafara aiki dan Momy kafin ta dau mutun tana kai shi catering yai training, jim Maman David tayi dan bata da kudin daxata iya biya mata hakan yakaranta a fuskarta yasa yaxaro damin kudi Wanda yasan yafi na catering din yawa ya mike hade da mika mata gashi aje ayi mata register, ta amsa tana xabga gdy

Wannan shine dalilin zaman Jennifer gidannan kuma tunda taxo na fuskanci tana sona tun ban yarda sonta nake ba har sai da na yaddarwa kaina ta tsunduma son jenny so kuma ba na wasa ba naso na aureta na maida ita cikakkiyar mace ya girgixa kai hade da cije lebenshi sagir kasan banta ba burin soyayya da karamar yarinya ba ? Babban burina shine auren mace wayayyiya wacce at least ace tagama degree dinta tasan rayuwa tasan menene aure, tana da cikakken hnklinta, bani da burin auren yarinyar da komai kai xaka koya mata ciki kuwa harda soyayya batasan yaxatayi ta farnta mk ba kana fishi da ita itama tana fushi da kai, dariya sagir yayi da sauri khaleel ya galla masa harara kaifa dan iskane dariya kakemin ?

Sorry abokina ina mmkin yanda akayi bakasan yaran yanxuba tarr suke ganinka abinda yaran xasuyi wata babbar baxatayi ba, tsaki khaleel yayi baxaka ganeba sagir !

Kayi hkr khaleel

Cije lebe yayi bakasan me nakeji ba Kalmar nan ta hkr da ka fadamin jinayi kamar ka Debi narkak ken ruwan dalma ka xubamin ajikina,

Wani irin xaro ido sagir yayi hade da fadin Allah ya kawo sauki

***************

Dady ya tarasu kaf mutanen gidan a babban falo harda su hindu sulthana da jenny yayi gyran murya yana kallonsu 1 by 1 shikadai yasan wanne irin yanayi yake jin kansa,
Chapter 30 · 0% Book details