← Book details Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 85

Sashe 44

Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Xaro ido tayi sosai tana kallonsa hade da kwabe fuska ashagwabe tace nifa..nifa.... Nifa gsky ban iya ba, da sauri yace " bari na koya miki, xatayi mgn taji bakinshi cikin nata yana shansu tmkr ya samu wani daddad'en mint hannunsa na shafa gashin kanta mai santsi da kyar ya saketa yana maida numfashi xubewa tayi akan gadonta ta rufe fuskarta da filowa itama tana maida numfashi, dariya yayi ganin ya sama mata kwanciyar hnkl ganin ta tashi yau bata jin dadi sbd abinda ya faru jiya kissing din gashinta yayi ya juya xai fita, dai dai bakin kofa ya tsaya asanyaye yace babyna anjima ki kawo min coffee shiru tayi bata bashi amsa ba, cikin wasa yace tunda baxaki mgn ba bari naxo na kara miki wani kissing din, da sauri tace a'a xan kawo ya fice yana dariya ya fita ta mike tana kallon gashinta daya hargitsa mata shi da sauri ta fara gyara jikinta Dan kar su sulthana suxo su ganta a haka,

Yana sauka kasa yaxo xai wuce su a falo Momy ta bar falon gab da xai fita sulthana tace ya khaleel ya mai jiki bata jira amsar saba tace Allah ya kara sauki, banxa yayi da ita ya fice Dan yasata a sahun yi mata uxiri, yana sautin dariyar sauran

*********

Tunda sulthana ta bawa Momy lbrn abinda taga jidda tayi yasata kin sakankancewa komai akan idonta akeyi abincin dare kullum jannat take sawa ta kai masa dake bai fiya yin dinner a cikin gida ba yauma har kusan 10:40pm bai shigo ba tana kallon jidda tana ta shiga da fice ganin haka yasa Momy ta kira jannat dan har ta fara bacci tace ta dauki abinci Ibrahim ta kai mishi da bacci a idonta ta nufi dakinshi Dan jiya batayi baccin kirki ba sallama tayi ya amsa yana aiki da laptop dinshi ganinta yasa ya rufe laptop din ta karaso kusa da shi ta cire hijab dinta ta xuba masa coffee tana kokarin xuba avincin ya dakatar da ita,

" banajin wunya

Ta kalleshi kamar xatayi magana sai kuma ta fasa ta sunkyar da kanta sbd wani irin kallo taga yana mata,

Da kyar ya iya shanye coffee din ya matsar da kayan abincin ya janyota jikinshi, da sauri tace " kayi hkr ya khaleel bacci nakeji,

Matseta yayi ajikinsa, muryar shi asanyaye yace " plx beautyna ina son jin jikinki ajikina kiyi kwanciyar anan, shiru tayi hnklinta atashe,

Lumshe ido yayi yana jin wani mugun sonta na karuwa aransa, yana jin dadin yanda take masa Sam bata iya Musa mishi duk abinda yace tana da biyayya sosai, tunanin shi xata wahalar dashi, sai gashi yasamu abinda ya keso, mace mai biyayya mara tsiwa da rashin kunya wacce tasan darajar aure, tana jinta ajikinshi takasa mgn da kyar tace, nabar Momy a falo tana jiran da wowata, da sauri ya tari numfashinta,

" beautyna ke fa matata ce menene dan taga baki dawo ba baxata damu ba Dan tasan dakin mijinki kikaxo ya dago fuskarta suka hada ido da sauri ta rufe idon, xame jikinta tayi,

tayi xugum tana son tayi mgn ta kasa ya kalleta da kulawa kina jin bacci ko ? Kai ta daga masa ya dauketa cak yashiga cikin bed room dinshi da ita ta shaki kamshin air freshner mai dadi ya ajjiye ta kan gadonshi ya juya tana kallon shi ya nufi inda manyan ledojin kayan da suka siya jiya a store ya dauko sleeping dress mai Kyau ya ajjiye kusa da ita" tashi kisaka kayan bacci, yana fada ya mike ya fice daukan rigar tayi tashiga toilet ta saka ganin rigar tafiya sharara iyakarta kasan gwiwa yasa ta tarasa yadda xatayi gashi hijab dinta na falonshi shigowa dakin yayi batanan ya xauna xaman jiran ta fito shiru kunya ta hana ta fitowa, ya gaji da jiranta ya tashi ya bude toilet din a sunkuye ya ganta ta rufe kanta da hannunta, yai murmushi soyayyar ta na karuwa aransa beautyna akwai kunya ya dago da ita ya kalli rigar yanda ta xauna mata ilahirin surar jikinta abayyane murmushi ya kumayi Dan yagane abinda ya hanata fitowa daukota yayi ya ajjiyeta kan gadon ya hawo ya janyota jikinshi yana shafa gashin kanta daya ke matukar so a hnkl kamshinta na rikitashi ya fara mata wani xafafan kiss tun tanajin na hnkl har taji abinda yana kokarin wuce xatonta don gaba daya ya hargitsata tsoro ya bata ta fashe da kuka jin tana kuka sosai yasashi sassautawa ya rarrasheta ya hade ta da jikinshi gam a haka sukai bacci motsi kadan intayi yakara riketa cikin jikinshi

**********

Da asuba ya tasheta tai sallar asuba tana laxumi bacci ya kuma a won gaba da ita yana dawowa daga masallaci yaga ta jingina jikin bed dinshi tana bacci a hnkl ya xame hijab din ya kwantar da ita shima ya kwanta gefenta yana kallon kyakkyawar fuskarta yana jin kamar ya hadeta

Da safe ta tashi tashiga toilet din shi tana brush mgnr jidda taji kamar tana kuka... Ya khaleel ka tausaya min ka duba halin dana ke ciki kasan ina sonka tunda kayi aure ka juya min baya har gobe ina jin takaicin wai da Jennifer xanyi kishi,tsawa taji ya kwatsa mata.... Kada na kuma jin kince mata Jennifer bakisan sunanta ba ?

Ya khaleel ta fada da kuka nima fa macece kasan irin bakin cikin Dana ke sha kuwa ?

Wannan ke kikasa aranki look ! Jidda bana son mgn daya idan xaki iya fine idan baxaki iyaba ki kyaleni nagaji, kasa jurewa jannat tayi sam ta manta rigar da take jikinta kai tsaye falon ta shigo kishi na cinta,

Nesa da juna suke kanshi na kan waya yana danne danne ya dago kai ya kalleta da murmushi a fuskarshi yace beautyna kin tashi ? Ta karaso kusa dashi, da mmk jidda ta dago kai tana mata wani mugun kallo ganin rigar jikinta yasa ta runtse ido ta mike da sauri tabar dakin,

Tausayinta ya kama jannat, plx ya khaleel kaji tausayin ta mana,

Kura mata ido yayi da alama mmkin mgnrta yaji ya tabe vaki hade da murmushi kadan ya janyo kayan breakfast sakko ki yi breakfast dinki ganin irin kallon daya ke mata yasa ta tuna rigar dake jikinta da sauri ta janyo hijab dinta ta saka murmushi ya kumayi ya bude laptop dinshi

Da kyar ta iya shiga falo ga mmkinta ba kowa kamar mai sanda ta lallava ta hau sama ta shiga dakinta ta kwanta tayi lamo momy ce ta shigo dakin itada su sulthana da hindu, "jannat xamu fita dasu hindu ki kula da gidan Dan duk sauran suma basa nan, da kyar ta ce to Momy adawo lfy Dan kunyar ta takeji murmushi Momy tayi ta fice

Ajiyar xuciya tayi ta sakko kasa farfajiyar gidan ta xauna tana xama ta hango wata tsuhuwa suna mgn da danjuma ya bude mata get ta shigo tunda jannat ta kalli tsohuwar taji batai mata ba kusa da jannat taxo tai mata sallama ta amsa "Yar nan ina hajiyar take ? Bata nan sunfita

"Fitsari nakeji zan wuce nace bari naxo nan gidan nayi kuma hjyn bata nan

Jannat tace eh ta fita,

Nuna min inda bandakin yake jannat ta nuna mata na tsakar gidan Wanda anan driver da danjuma suke amfani dashi kwata kwata jitayi hnklinta bai kwanta da matar ba, ta ajjiye jakarta jannat ta kalli agogon tsohuwar na gwal ta xaro ido sosai ta bi tsohuwar da kallo har tashiga toilet din bata jima ba ta fito ita kam jannat jikinta tuni ya fara rawa Dan tsoro damma ta hango danjuma yana sallah nesa dasu kadan, takara so kusa da jannat," Yar nan nace Ku yan biyu ne agidan nan ? Da sauri jannat ta girgixa kai a'a ni kadaice tana ganin lokacin da tsohuwar tai ajiyar xuciya da alama taji dadin amsar da ta bata, "to ngd na tafi

Da kyar jannat tace mata to ! Gaba daya ta rude

By

*Ummee Garkuwa*

[10:25PM, 12/11/2016] Fatima Garba:
'<Øûß
'<Øûß
'<ØûßJENNIFER
'<Øûß
'<Øûß
'<Øûß

71&72

a tsorace take kallon matar xuciyarta na cikin firgici har matar ta fice daga gidan kasa komawa cikin gidan tayi sbd firgicin da ta ke ciki meyasa wannan tsohuwar ta tambayeta su yan biyu ne ? tunda take bata tab'aganin wannan tsohuwar ba,gabanta yai mummunan fad'uwa da ta tuno gargad'in sadik osasa akan su kiyaye yawo barkatai sbd har yanxu ba'a daina bibiyar rayuwar su, xumbur ta mike xuciyar ta cike da firgici safa da marwa da farayi a cikin harabar gidan tana jin takaicin kyale matar da tayi da bata cakumeta ba, bacin rai mai tsanani ta tsinci kanta da shi, da sauri ta nufi danjuma axaune ta sameshi yana laxumi tak'arasa muryarta na rawa ta gaishe shi ya amsa yana kallonta dan yaga hnklinta atashe,

danjuma kasan wannan tsohuwar ?

arud'e ya amsamata, a a madan wllh ban santa ba me ya faru ??

a tsorace ta kalleshi hnklinta ya kuma tashi,

meyasa kabarta ta shigo ?

mikewa tsaye yayi yana xare ido,

cemin tayi wajan hjy taxo nace sunfita shine ta ce min waccen ba Jennifer bace nace eh shine tace bari ta baki sako wajan hjyr intaxo a fada mata,

girgixa kai kawai tayi dan bacin rai ya hanata mgn cikin gidan ta wuce ta dafe kai hade da xama akan tyles na harabar gidan cikin wani mugun yanayi ? bataraba dayan biyu tabbas matar nan taxo bincikarsu aikota akayi , su kuwa wanne irin laifi sukayi ake bibiyar rayuwarsa ?
Chapter 44 · 0% Book details