← Book details Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 85

Sashe 37

Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tureshi tayi, sbd jin haushin mgnrsa, da fada tace masa, wanne àbu nake boyewa ?

Cikin ko inkula yace yace, Wanda kikeso,

Runtse ido tayi mgnr ta mata zafi har yanxu yana nan da wannan tunanin ? Dole kam ta sauya Dan taga abin xai wuce gona da iri,

Rike kugu tayi tana kallonshi, ni babu Wanda nakeso babu kuma abinda nake b'oyewa,

Aurenka kuma bani na xab'a ba kusan dolenshi ma akaimin, ta juya ta bude kofa ta fice hade da yi masa Harar sama da k'asa

Wani mugun mmk ne ya kamashi ya xauna yana nanata xancen,

" kusan dole akai mata ?

Gaba daya yaji kanshi wani iri ta bashi mmk baiyi tunanin ta iya tsiwa hakaba,

Da matukar jin haushi ta nufi bangarenta ta kwanta tana mmkin halin khaleel haushin sa sosai ya kamata ta gaji da wannan rainin wayon, kallonta kawai yake bai sonta ba,

Tsaki taja xaka sha mmk na, ta kwanta ranta abace cike da jin haushin shi,

*****************

Washegari da rana suna dakinta inda suka saba zama suwaiba ta shigo sbd tana koyawa jannat karatu, bayan sun gaisa, sulthana ta kalli hannunta da mmk tace suwaiba ina son henna waye yai miki ?

Zama suwaiban tayi tana murmushi ni nayi sulthana, wow ina so kiyi mana nida Anty jannat banda waccen ta nuna hindu Dan ko kin mata ba Kyau zaiyi ba, kin ganta cen duk itace mummunar mu,

Dariya sukayi banda hindu datake hararar sulthana, da dariya suwaiba tace haba duk kamarku daya ni kaina da yanayin shigarku nake tantance ku, Baku da banbanci, bari naje na hado kayan kunshin in dawo,

Bata dade ba ta dawo tai wa sulthana me Kyau sannan ta fara yiwa jannat ana gama mata na hannu wayarta tai kara hindu ta dauka ganin Mr coffee yasa tace jannat waye kuma Mr coffee? lokaci daya sukayi dariya da suwaiba, kar ta katse fa " ajjiye kwai hindu tunda lalle ne a hannuna haka wayar tai ta kara har ta tsinke sai wajan 4:00 tagama musu lallan mai Kyau dake gwana ce suwaiban ta kware sosai yayi Kyau

Toilet tashiga tai wanka kafin ta fito suma sun tafi wankan ta dakko kayan daxata Sa ka English wears ne murmushi tayi da ta kalli kayan yayanta Emanuel ne dayaje jos ya siyo mata su atsaraba satin da xasu shiga wannan wahalar rayuwar bata taba Sa kayanba body hock ce pink me karamin hannu da siket dinta bai karasa sauka kasa ba sun mata Kyau sosai ta tsaya gaban mudubi tana taje kanta bude kofa akayi ta xaci su sulthana ne ganin shi tayi cikin madubin ta hade rai tai kamar bata ganshi ba ya xuba mata ido Hannunshi sanye cikin aljihu,

"Bakiga miscalled dina ba ?

Banxa tayi dashi kamar bata jiba,

Mmkinta yake, bakyaji ina mgn ? Ya fada da fad'a,

Ya b'una fuska tayi mgnr takace bata da amsa,

Kadan yarage yasaki baki sbd mmk,

Mikewa tayi tana gyara xaman siket dinta, ya karewa shigar ta kallo tai mata Kyau ya kalli kirjina gabanshi sai da ya fadi,

Adake yace meyasa baki daga ba ??

Far tayi da ido "sbd bani da abinda zance,

Ta gama kaishi karshe a mmk tambayar kansa ya fara yi dama haka ta iya tsiwa ?

Har ya juya xai fita sai kuma ya dawo hade da fincikota, jikinta na gogan nashi idonta kir akanshi, ki kawo min coffee dakina ina jiranki, fincike jikinta tayi ta kasa sbd bakaramin riko yai mata ba, shiru tayi tana kallonsa, da tsawa yace ko bakiji ba murguda baki tayi, da mmk ya saketa lallai yarinyar nan ta shammaceshi, ta koma nesa dashi, ya fice daga dakin, tayi dariya ta cigaba da taje gashinta, mutun sai kafiya da riqak'k'en ra'ayi taja karamin tsaki

******

Ya kalli agogan hannunsa 11:30 ya furxar da huci me yarinyar nan take nufi ? Kodan taga yana hada jikinshi da nata ? Tun kafin magrub yace ta kawo masa coffee har yanxu bai ganta ba ? Dalilin daya Sa baison yarinya kenan dafe kanshi yayi idanfa yayi sake rainashi xatai shi mutun ne da baya son raini shiyasa ko k'annan sa baya wasa dasu xabura yai ya mike ya fice daga dakinshi kai tsaye bangarensu yayi yashiga dakinta tana kwance ta na bacci ya kalli beauty face dinta tayi kyau da baccin, tsura mata idanuwansa yayi yana kallonta, a hnkl ya xame bargon jikinta ya kalli hannunta dayasha lallai mai kyau yashafa hannun sbd yana matukar son lalle motsi tayi ya cire hannunsa ta juya daga kwanciyar ya kalli gashin kanta cikin sha'awa yakai hannu ya shfa kan, xabura tayi ta mike idonta taf cike da bacci ta galla masa harara menene haka ? Hada rai yayi ban sani ba ya mike tsaye, daxu nace ki kawomin coffee meyasa baki kawo ba ? Ya b'una fuska tayi "mantawa nayi ta fada tana gyara kwanciya, jannah ! Ya kira sunanta da tsawa har sai da ta tsorata,me kike nufi ne amarairaice tace kayi hkr plx bacci nakeji,

Mantawa nayi,

" kinga bana son musu ko gardama kina jina ya fada hade da xare ido, na kyaleki sbd yau kika fara kada ki kuskura ki kara maimaitawa, ya fice daga dakin ajiyar xuciya tayi hade da hararan bayansa, idan baxaka canxa ba ya khaleel nima yanxu na fara ta juya ta cigaba da baccinta,

Da safe bayan sunyi breakfast suna hira ga al'adarsu, muryar Jidda taji tayi sallama suka shigo ita da mamanta da gudu zahra ta rungumesu gaban jannat ya fadi tasan wannan xuwan ba alherine ya kawosu ba

By

*Ummee Garkuwa*

[7:22PM, 12/5/2016] Fatima Garba:
'<Øûß
'<Øûß
'<ØûßJENNIFER
'<Øûß
'<Øûß
'<Øûß

61&62

Da murna zahra take oyoyo Anty Jidda,cikin fara'a Momy tace sannunku da xuwa hjy hadiza, fuskar Jidda ba yabo ba fallasa ta xauna kusa da ya khaleel kamar xata shiga jikinshi, wani kishi azababbe ya tasowa jannat, hjy hadiza kuwa fuskarta aturbune ta xauna tana wa falon kallon ya tsina, Momy tace ina Sa'a bari aka wu muku ruwa, wani kallo hjy hadiza taiwa momy a'a Ku barshi, ayatsine ta kalli su jannat, ta kalli momy,wai hjy Fiddausi meya ke damunku keda yaya bashir ? Da mmk Momy tace kamar ya ?

Tsaki hjy hadiza tayi haka kawai Ku kwaso yara har 3 Ku xauna tare dasu bakusan asalinsu ba, wllh nasan wannan shirin duk nakine Fiddausi ke wacce iriyar mutunce ?? Wato ke ta Allah ko ? Taimako kikeyi ?

Tsaki ta kuma, da kallon raini tabi su jannat dashi, malamai atashi abani waje zan gana da dangina da y'ay'ana, sulthana ta mike,tana harare harare, agana lfy tayi sama suma suka bita,

Cikin fada hjy hadiza ta nuna sulthana wacce fitsararriyar fa ? Daga ganinta bata da mutunci,kwafa tayi wllh Fiddausi kin cucemu, ran mommy abace tace ya'isa hadiza ni ba matar kaninki bace wan ki na ke aure, zaki dinka yab'amin duk mgnr da taxo daga bakinki ? Zaro ido hjy hadiza tayi oh ! Sannu bashir, to ! Ko shine yai ba dai dai ba sai na fada masa balle ke ! Yana ina ? Momy tace ya fita sai anjima zai dawo, ta waiwayo kan khaleel da kanshi yake kan danne dannen waya, sannu ibraheem bani da kimar daxaka gaisheni ko ? Da kyar yace mata sannu da xuwa, cikin ranshi yana jin haushin matar Dan ba yadda xaiyi da ita sbd kanwar dady ce cin fuskar da takewa Momy baya so, mikewa yayi xai fita, ita kanta hjy hadiza tana shakkar shi Dan tasan bashi da wasa, dawo Ibrahim akwai mgnr da xamuyi da kai, da wowa yayi ya xauna batare da ya kalleta ba, ya mgnr ka da jidda? Cikin jin haushinta yace, ni na manta da wannan maganar amma nasan dady yana sane ita,yanayin yan da yai mgnr kana kallonsa Kasan ba wasa, mmk ya kama hjy hadiza, lallai Ibrahim ka manta da yar'uwar ka Jidda sbd ka auri arniya saniyar bare tsintacciyar mage wacce bata xama...... Mikewa yayi, umma! ya fada axuciye,

"yanxu jannat ba arniya bace ta musulunta, idan tsintacciyar mage ce mutun ce kamar kowa ya halatta a aureta akuma xauna da ita plx umma ke babbce sannan kuma uwa, ya kamata ki tausasa maganganunki, ya juya xai bar falon Jidda tabi bayanshi, tagumi hjy hadiza tayi Tabbi ! Aiki jaa yarinyar nan tagama da Ku kaf, anya kuwa yaron nan a hayyacinsa yake ? Yana min mgn kamar zai kawo duka ? Zama bai kamani ba, Momy ta mike hade da fadin Allah ya kyauta tayi sama tana jinjina halin hjy hadiza, ruby ma bayan Momy tayi Dan ta tsani halin kanwar Baban nasu zahra tayi zugum Sam bataji dadin cin mutuncin da umma Taiwa momynsu ba

*********
Chapter 37 · 0% Book details