← Book details Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 85

Sashe 65

Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya shiga mota idonshi akanta yana tuna adadin missing d'inta da xaiyi bai gama rufe k'ofa ba yaga hjy murja ta bud'e mata k'ofar motar ta shigo ciki a kunyace,

murmushi ya kufce masa tuni ya nemi b'acin ransa ya rasa da murna ya kalleta sam ya manta iyayensu na gefe suna kallonsu,

"beautyna zaki min rakiya ko ?

kyafta masa ido tayi, ina murna ta hanashi kula,

"Alhmdllh naji dad'i sosai da wannan rakiya" dai dai lokacin da driver yaja motar su hjy suna musu addu'ar Allah ya tsare,

suna fita daga gidan ya janyota jikinsa yana kallonta itama kallonshi take da murmushi a fuskarta

"harna fara tunanin halin da zan kasance na rashinki kusa dani"

far tayi da ido,

"ni kaina na shiga wani yanayi na rashinka da zanyi"

"wow!"

ya rungomata sosai yana murmushi mai sauti,

da sauri ta kufce jikinta had'e da xare ido kallonta yayi da rashin fahimta da ido ta nuna masa bafa suka d'ai bane a motar tab'e baki yayi ya janyo ta jikinshi a kunnanta ya rad'a mata,

"ina ruwa na dashi babu wanda xai hanani shak'ar k'amshin matata mai dad'i"

marairaicewa tayi shafa lip dinta yayi ya girgixama mata kai

"kiyi hkr baxan iya xama kusa dake ban jiki ajikina ba"

ta kalleshi ya kashe mata ido d'aya

a haka sukaje airport basu b'ata lokaci ba suka hau jirgi yana rungume da ita har suka isa Abuja tare da security d'in da aka had'asu kai tsaye gidan Abba na cen suka tafi dan anan yace su xauna shi kanshi gidan xagaye yake da security jinjina kai khaleel yayi yana tausayin Abba gaba d'ayan shi arikice yake axxaluman mutanen nan sun rikita shi bashi da kwanciyar hnkl ko kad'an

suna shiga cikin gidan alwala suka d'auro sukayi sallar la'asar suna idarwa ya mik'e yana kallonta,

"taso muje muyi wanka"

kwab'e fuska tayi kamar xatayi kuka

"kaje kafara yi in ka fito ni sai nayi"

zaro ido yayi yana kallonta,

"tashi muje"

nuk'u nuk'u ta tsaya yi da kanshi ya mik'ar da ita yana k'ok'arin cire mata kaya rik'e hannunshi tayi tana dariyar dole

"tsaya tsaya ya khaleel bari na cire da kaina"

sakin ta yayi yana dariya ta cire kayan tsab ta d'aura towel suka shiga toilet kallonshi ta tsaya yi tana tunanin cire towel d'in ganin haka yasa ya janyo hand shower ya jik'ata da shi tana dariya da kanshi towel d'in ya sub'uce ya fad'o kamar wasu yara haka su ka d'inka wasa da hand shower d'in daga hannun wannan xuwa hannun wannan sun dad'e suna wasan ruwan sannan sukayi wanka shi kanshi wankan haka suka d'inka facin facin da kumfa sun b'ata lokaci mai yawan gaske sannan suka fito kowanne jikinsa d'aure da towel yana rungume da ita suka k'araso wajan mirror ya janyo wani towel d'in na daban ya tsane mata ruwan jikinta sannan ya mik'a mata ta tsane na jikinsa suka shafa mai suna tsokanan junansa da man shafawar,

bayan sun gama shafa man ya kalleta,

" kwalliya xan miki da kaina"

ware ido tayi had'e da dariya tana kallonshi,

ya d'auko powder ya shafa mata tana kallon mudubi tana mmk ya d'auko lip stick ya shafa mata a leb'e xata gyra ya tsayar da hannunta,

"no ! ban yadda ba ni zan gyra komai na hutar da ke "

haka ya bar fuskar yana kallonta ta jikin mudubi silent makeup yai mata kyau sosai ta tashi tsaye,

"gsky ya khaleel ka iya makeup zan bud'e maka waje na musamman ka dink'a yiwa amare mskeup dan kaxama babbn arties"

dariya yayi shima yana kallon bayanta da ta juya tana tafiya wajan inda kayansu yake,

"matata kawai na iya yiwa banda ita baxan iya a fuskar kowa ba"

ta d'auko musu kaya su ka shirya,

"zan tafi meeting da bak'on Abba inaga baxan wuce 2 hours to 3 ba"

ya rik'o hannunta suka isa k'ofa ya janyota jikinsa suna kallon juna ya shafa lip dinta da yake so

"kinyi kyau da wannan kwalliyar"

itama lip d'inshi ta shafa tace,

"kayi kyau da wannan shigar"

dariya yayi,

"duk abinda nai miki sai kin min ko?

itama dariya tayi had'e da yin far da manyan idanuwanta daya k'ara mata kyau,

"kai ka koyamin"

tafad'a idonsu cikin idon juna,

shafa cikinta yayi yana kallonta yana dariya k'asa k'asa,

sunkuyar da kanta tayi had'e da jin kunya ,

dariya ta bashi sosai,

"ki rama mana"

girgixa kai tayi kanta ak'asa,

birgesa tayi ya kalli kanta data sunkuyar dashi,

yasa hannu ya d'ago fuskarta da sauri ta rufe idonta

fuskarta d'auke da murmushi,

har yanxu hannunshi d'aya na cikinta yana shafawa,

"bud'e idonki beautyna"

a hnkl ta bud'e idon suka kalli juna da sauri ta rufe harda sa hannu,

"d'ago kanki plx"

ya fad'a muryar shi asanyaye,

ta bud'e idonta don bata son yi masa jayayya,

" ina sonki "ya fad'a had'e da yiwa hancinta kiss ta lumshe ido,

tana k'ok'arin janye jikinta ya kuma rik'ota

"ina xaki tafi ?

"katafi wajan meeting d'in karka b'ata lokaci"

d'age kafad'a yayi,

dariya ya bata yanda ya d'age kafad'ar,

"zantafi ammaa....

"amma me ?

bakinta taji cikin nashi yana tsotsarsu kamar me shan mint mai xak'i

yadad'e yana tsotsar bakin nanta sannan ya saketa yana fidda numfashi a hnkl itama munfashin take a hnkl kanta ak'asa

muryarshi a tausashe yace,

"amma sai naji lafiyar lip d'ina"

ya shafa cikinta yana mata wani irin murmushi

"ajiyata tana nan tafe very soon"

xaro ido tayi ya fice yana dariya,

yana jin sassanyar muryarta tana masa addu'ar Allah ya dawo mata dashi lfy,

yana tafe driver na janshi yana tunanin jannat d'insa yana jin tamkar ana k'ara mishi sonta ajiyar xuciya yayi yana nuna farin cikinsa da gdy ga Allah da ya bashi mace mai biyayya dan shi rayuwar sa yana son biyayya a haka yaje wajan meeting d'in sama sama yake jinsu sai da suka kusan kwashe 4 hours suna tattaunawa hnklinsa na kan ya koma gida ya shak'i kamshin jannat d'insa mai sanyaya masa rai

basu gama ba sai gaf da sallar isha'i duk hnklin sa ya tashi baiyi tunanin meeting d'in xai kai su wannan lokacin ba sai da ya tsaya yai sallah sannan suka taho akan hanya ya tsaya yai musu siyayya mai yawan gsk suka taho

suna shiga ya fito daga motar dan sauri bai bari sun k'arasa parking ba kai tsaye cikin gidan ya shiga had'e da sallama tana xaune a takure da ganinta kasan cikin damuwa take da sauri ta d'ago manyan idanuwanta tana kallon shi had'e da yin ajiyar xuciya siyayyar ya ajjiye akan center table d'in falon ya k'arasa kusa da ita ya xauna ya janyota jikinsa, hawaye ya gani kwance kan fuskarta xaro ido yayi yana jin ba dad'i yasan dole ta damu,

"kaina bisa wuya beautyna!

kiyi hkr meeting d'inne yaja mu tsawon wannan lokacin ni kaina banyi tunanin xai kai mu haka ba bazan kuma ba plx plx plx ina jin ba dad'i araina sbd na saki xubar da hawaye akan kyakkyawar fuskarki ban so ba yasalam !"

ajiyar xuciya tayi tana kallonshi duk ya rikice sbd ganin hawayenta lumshe ido tayi tana jin dad'in irin yanda yakeji da ita,

"ban xubar da hawaye na dan kadad'e ba nayi ne sbd ban san halin da kake cikiba"

k'ank'ameta yayi sbd yaji dad'in maganarta

"ina nan k'alau sai azabar tunaninki da nai tayi hnklina bai kwanta ba sai da najiki kwance cikin jikina"

k'asa k'asa yai da muryar sa

"ina sonki jannah !"

ta xame daga jikinsa

"ka gaji muje kayi wanka kaci abinci"

baiyi musu ba ya mik'e hannunshi rik'e dana ta yana murxawa taraka shi bakin toilet d'in ya shiga yai wanka ya fito da taimakonta ya sauya kaya ya kalli agogo 9:49pm

"ya khaleel taso muje kaci abinci"

wani irin kallo yake mata ya girgixa kai

"d'auko ledar dana ajjiye a falo"

ta juya ta fita ya bi bayanta da kallo had'e da lumshe ido bata dad'e ba ta dawo hannunta rik'e da manyan ledojin ta xaune ya bud'e manyan gasassun kajine da kuma siyayya kala kala

"zo muci"

girgixa kai tayi,

"naci abincifa"

kallon da yai mata ne yasa ta marairaice ta matso tana ci kamar tana shan magani kad'an taci,

"ya khaleel na k'oshi fa dan bai bana son jayayya da kai"

jinjina kansa yayi

bayan ya gama ci ya mik'e yana kallonta fuskarshi d'auke da murmushi

"taso muje muyi alwalar nafilar da xamuyi"

jikinta asanyaye ta mik'e suka d'auro alwala sukayi sallah ya dad'e yana addu'a sannan ya waiwayo yai addu'a tuni gabanta ya fara luguden fad'uwa dan tsoro bayan ya idar ya tsura mata ido yana tunanin abubuwa da yawa jikinta na rawa ta mik'e xata fita gaba d'aya ta rikice jikinta har ya fara rawa,

da mmk ya kalleta,

"ina xaki jannah !?

hanjin cikinta sai da yaka d'a dan tsoro

"dawo nan ki xauna ba inda xaki "

[5:27PM, 12/27/2016] Fatima Garba:
'<Øûß
'<Øûß
'<ØûßJENNIFER
'<Øûß
'<Øûß
'<Øûß

*Ummee Garkuwa*

99&100

sororo tayi tana kallomshi, jikinta na kyarma kamar mai jin sanyi.

kallonta yayi taso ta bashi dariya yanda lokaci d'aya ta firgice tana masa kallon tsoro kamar tana kallon aljani,

"dawo ki xauna"

a hnk take tafiya kamar tana kan wuta haka take jefa k'afa jikinta asalub'e ta xauna nesa da in da ta tashi kanta a k'asa.

tsura mata ido yayi yana mata wani shu'umin kallon yanda jikinta ke rawa lokaci d'aya murmushi ya sub'ce masa.

"jannah ! menene haka ?duk kika bi kika takurawa kanki ?"

a d'an tsorace ta kalleshi kamar xata fashe da kuka.

"ba komai"

yanayin yanda ta bashi amsa kana gani kasan ta fad'ane kawai.

yasaki numfashi yana kallonta yana jin sonta na masa yawo a ilahirin sassan jikinsa

ya tashi daga inda yake ya matso kusa da ita ya rik'o hannayenta da suke rawa,

murmushi yayi yana kallon hannun ya kalleta duk ta takura kanta sai nuk'u nuk'u take.

"jannah saki jikinki mana yau kika fara ganina?"yayi mgnr ne cikin sanyin murya.

girgixa masa kai tayi dan bata son mexa tace mishi ba.

janyota yayi jikinsa.

tsoronta ya k'aru hnklinta yai masifar tashi tana jin fitar numfashinsa da suke fita da sauri da sauri.
Chapter 65 · 0% Book details