← Book details Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 85

Sashe 74

Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

babban burina naga kin ajjiye min ajiyata"

ya bata dariya

"ajiyar nan taka na bani dariya idan kana fad'inta"

shima dariyar yayi yana shafa cikinta da tun xamanzu yake shafa cikin

"xakiyi dariya ne idan kika tashi sauke min ita"

b'ata rai tayi cikin shagwab'a tace

"na fasa sauke maka ita tunda kana so na wahala"

shima kwab'e fuska yayi ya kwaiwayi yanda tayi mgn

"ni banso jannah ta tawahala da

da yanda zanyi dana dawo da ajiyar jikina sbd na hutar da beautyna me d'an k'aramin lip me kyau"

birgeta yayi sosai dan bata tab'a ganin namijin da yai shagwab'a tai masa kyau irinshi ba dariya tayi tana jin sonsa sosai

"daga yau na dena shagwab'a tunda ka iya"

tab'e baki yayi

"da kuwa kinci nad'a"

xaro ido tayi

"laaa nad'a?"

kama bakinsa yayi yana dariya

"ban fad'a ba ! na isa ! in daki ajiya ta indaki beautyna, kin san irin nad'ar da zan miki ?"

girgixa kai tayi had'e da cukuma fuska wai dagaske tana fushi.

dariya cukume fuskar ta bashi

"kinyi kyau anjima in dare yayi zan nuna miki nad'ar dana ke nufi"

"ni yanxu nakeso"

ta fad'a tana juya baki.

wasu abubuwa ya fara mata tana dariya ta kwace daga jikinsa

"kabari sai anjiman ka nuna min "

shima dariyar yake yace

"nima ban yadda ba yanxu zan nuna miki "

da gudu tayi bed room tana

"ban yadda ba "

bin bayanta yayi

"ni kuma yanxu nakeso"

shiga bed room d'in yayi ya tadda ita cen k'arshen gado ta duk'unk'une tana dariya

tsaya wa yayi yana kallonta cike da birgewa

"yanxu zan koya miki abinda kike son sani"

yayo inda take dukansu suna dariya mai cike da tsantsan k'auna had'e da shauk'in junansu.

3 days a go

kwana kin nan uku datayi tare dashi ta ga gata iri iri motsi kad'an in tayi ajikinsa takeyi baya barin ta tai aiki ko kad'an sbd yace ajiyar sa batai kwari ba baya son awahalar masa da ita.

tana kwance jikinsa suna kallon indian series data ke so ya shafo gashin kanta

"beautyna gobe fa xamu tafi "

da mmk tace

"ina ?"

ya saukar da idonsa kanta.

"inda na shirya mana xamuje mu ci amarcinmu"

murmushi tayi

"Allah ya kaimu goben"

" amin ki shirya tarar wata ajiyar"

xaro ido tayi ta juyo tana kallonsa,

"banda wacce aka ajjiye"

d'aga mata gira yayi

"ina son ajiyar ta xama biyu"

sauke numfashi tayi ta mik'e daga jikinsa

"tunda abin hakane nima zan maka ajiya"

dariya yayi sosai ya tallabota,

"kinyi ajiya tuntuni jannah ! kin ajiye ....."

ka tseshi tayi da

"irin ajjiyar da kai min zan maka"

dariya sukayi dukansu.

washegari da safe suka gama shirinsu gida suka wuce sukayi sallama da su sannan driver da ma su tsaron su suka rakasu airport.

*Ummee Garkuwa*

[9:26AM, 1/9/2017] Fatima Garba:
'<Øûß
'<Øûß
'<ØûßJENNIFER
'<Øûß
'<Øûß
'<Øûß

111&112

*Ummee Garkuwa*

satin su 2 a dubai suka wuce Singapore sun sha amarcinsu sosai sun nunawa junansu soyayya satinsu 2 acen Abba ya kirasu awaya akan su xo hjy murja bata da lafiya sosai ba shiri suka dawo batare da sunyi adadin kwana kin dasuke son yi ba tun acikin jirgi jannat take kuka sosai sbd basu san yadda jikin hjy murjan yake ba gaba d'ayansu hnklin su atashe yake har suka dawo 9ja kai tsaye gidan su suka wuce suka tadda shi empty ba kowa duk suna asibiti megadin su ne ya fad'a musu asibitin da suke nan cikin G.R.A lameedo crescent kai tsaye asibitin suka xarce a babban d'aki suke wanda d'akin an wareshi ne sbd kwantar da manyan mutane tunda suka shiga hnklin y'an'uwansu ya dawo kansu kowa na mmkin dawowar tasu dan basuyi tsammanin su yanxu yanxu ba hjy murja na kwance kan gadon marasa lfy ta rame kana ganinta kasan tasha jinya da sauri ta tashi daga kwanciyar datayi tana kallonsu fuskar ta d'auke da murmushi hannu ta nik'owa jannat

"Alhamdulillah jannat kin dawo xo na rik'eki naji ko kece ba gixo kikai min ba"

hawaye fal idon jannat ta k'arasa kusa da ita ta rik'e hannunta k'am tamkar wacce xa'a kwace ta.

hannu ta mik'owa khaleel dayake a tsaye yana kallonsu fuskarshi d'auke da tausayinsu.

"matso khaleel ngd wa Allah daya dawo min da ku lfy ban mutu ba"

hjy Nabila tadake gefenta a xaune tayi tagumi muryar ta asanyaye tace,

"haba murja tun yaushe zan fad'a miki ki daina wannan zancen ? cuta fa ba mutuwa bace kin damu bakiga jannat ita da khaleel damuwar hakan har ciwonki ya tashi gasu nan sun dawo kusa dake ki saki ranki,

ki daina sa damuwa aranki Allah xai kiyaye miki su"

tak'arasa idonta fal hawaye.

tunda ta fara mgn falon yai tsit suna kallonta har tagama

wani irin murmushi hjy murja tayi cikin muryar mara sa lfy dasuka fara warwarewa tayi mgn

"bana ji na dai dai idan har bana jin nimfashin su kusa dani babban burina duk na waiwaya naga idanun y'ay'ana "

momy tasa baki,

"yanxu ga sunan sun dawo kusa dake ki cire damuwa murja y'ay'anki sun dawo"

dady da Abba ne basu ce komai ba sai binsu da ido,

jannat da hawaye suka cika mata ido tuni suka b'alle hawaye ke xuba kamar an bud'e fanfo

zaro ido sulthana tayi tana kallon jannat dake tsiyauar kwallah

"anty jannat hawayen me kike ? kun tafi kun barmu da kewa kina cen kina hutawa kinyi k'iba da kyau kin xama k'atuwa kin bar umma da kewa gashi nan har ciwonta sai da ya tashi,

kukan me zaki ai mun gama kuka tunda ta warke fatanmu Allah ya bata lfy ke kuma Allah ya sauke ki lfy "

idonta fal hawaye hakan bai hana ta jefi sulthana da uban harara kamar idanuwanta zasu fad'o

hjy Nabila sunkuyar da kai tayi fuskarta k'unshe da murmushin jin dad'i dan taga y'arta ta ta canza alamun akwai motsi a cikinta dan ga alamu nan b'aro b'aro sun bayyana

momy kam hamdala tayi axuciyarta najin dad'in samun jikanta na farko a duniya itama yau taxama kaka.

k'ara rik'e hannunta hjy murja tayi tana hararar sulthana kad'an

"karki matsa mata yanxu lallashi take buk'ata Allah ya sauki jikana lfy"

dukansu suka amsa da amin

hajiyarmu tace

"banda muna asibiti dana yi gud'a Alhamdulillah ! ina kallonki nasan jikata akwai kyakkyawan motsi a jikinta"

tuni ya khaleel ya manta a inda yake

"hajiyar mu da gaske kikeyi jannat tana da ciki ?"

hararar wasa tai masa cikin wasa tace

"ah 'ah bata dashi sai k'aton toilet"

dady da Abba ficewa sukayi fuskokinsu k'unshe da murmushin wannan lbrn na samun k'aruwar da sukayi..

khaleel ne yai hmdl mai cike da xak'uwa da murna matuk'a dan bai tab'a tunanin ajiyar tashi ta xaunu ba

"Alhmdulillah na zama baba nima Allah na gode maka da wannan ni'ima jannat! Allah ya biyaki "

sulthana kwashe wa tayi da dariya da sauri ta kame baki tana kallon hjy murja

ta waiwayo kan ya khaleel daya xubawa jannat ido yana jin kamar ya had'iye ta,

"majnun kalli umma da hajiyarmu da momy kada kayi sub'ul da baka"

waiwayo wa yayi fuskarshi kamar ammasa albishir ko kad'an baxai iya k'iyasta abinda yakeji na game da farin ciki

"suma suna cike da murna sun sami jikan su na farko,

kada kidamu k'anwata yau babu wannan

abune na farin ciki bazan iya k'iyasta miki yanda nakeji ba zan xama uba ga d'an da jannat xata haifa mana"

da sauri jannat ta kwatse shi da shagwab'a

"habaaa ya khaleel ! kabarii manaaa kana kallonsu momyyy faa"

kama bakinsa yayi yana kallonta

"sorry sorry beautyna kada ki yi fushi kin san ba ke kad'ai bace "

murmushi hjy murja tayi

"ya khaleel angon k'arni kwantar da hnklinka baxatayi fushi ba,

ina ita ina yin fushi bayan tasan ba ita kad'ai bace ?

jannat yi shiru saki fuskarki "

salati momy tayi hjy Nabila ta tayata.

" oh ! zamani Nabila kalli ikon Allah uwa da y'ay'anta tana tayasu sakarci?"

hjy Nabila tace

"hmm kasa mgn nayi uwar da y'ay'an sai a hnkl"

hajiyarmu tai dariya tana kallonsu

"kunga kada mu matsawa jikokina kuma ba'a hanaku yi ba ku kyalesu su warwasa"

hindu da ta zabga tagumi tana mmkin surutun su da rashin kunya ta ya mutsa fuska

"wai kun manta a asibiti muke ?"

hajiya murja ta kalli hindu.

"hindu na warke ni kam babu wata sauran cuta kuma yanxu babban fatanmu Allah ya sauki y'ata lafiya"

ta k'arasa mgnr tana kallon jannat fuskarta k'unshe da murmushi.

kwanan su 2 da dawowa aka sallami hjy murja daga asibiti sbd ta warke.

hankalin dangi biyu na kan cikin jannat dan sai da suka sa akai nata test anan asibitin aka tabbatar da tana da shigar ciki wata 2 da sati uku farin ciki kam ba'a mgn kaf dangi sai da suka san da zaman cikin dan ched'e family har d'an k'aramin biki sukayi shi kam Alhaji Adam ched'e kallon dangin nasa kawai yake amma xuciyar sa na k'in amincewa dasu sbd cike yake da xargin su.

tana kwance jikin ya khaleel tana cin magarya dan bata laulayi ko kad'an sai d'an karan kwad'ayi kusan komai ta gani birgeta yake suna kallon tashar libarty tv bayan sun gama news suka fara na farashin kasuwa suna nuna hotunan kayayyakin abinci karaf idonta ya kai kan gwarin kwaki tuni taji tana sha'awar shi musamman jik'ak'k'e me siga da gyada mai gishiri irin had'in dasukeyi lokacin da tana gidan maman david abinka ga renon yare

tuno had'in tayi

ta had'iyi yawo da sauri ta kalli ya khaleel daya ke k'ok'orin canza wata channel d'in

"ya khaleel ina son garin kwaki plx yanxu"

ajjiye remote d'in yayi da sauri yana kallonta

"ok beautyna duk abinda kikeso cikin sauri zan kawo miki sbd bana son ajiyata ta wahala"

ta xame daga jikinsa ya mik'e ya sunkuyo dai dai cikinta ya shafa shi kamar yanda yake kullum.

" babyna zanje na siyowa mamanka garin kwaki yanxu zan dawo bana son na dink'a nesa da kai amma zan bar amanarka a hannun mamanka ta kula min da kai,"

ya k'ara shafa cikin

"me zan siyo maka?"

kwab'e baki jannat tayi.
Chapter 74 · 0% Book details