← Book details Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 85

Sashe 40

Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da sauri ta nufo bangaren su jidda ta hango idonta sunyi jaa tana kara sowa hijab dinta ta kuma fincika, tsaki jannat tayi tana mata kallon sama da kasa, ganin irin kallon da jannat din take mata yasa tace iyye sannu yar matsiyata kinxo gidan arxiki kin bude kafa kina cin maiko har kin auri d'an masu gida, kinyi kuskure Jennifer sai kinyi danasani kina tak'ama da auren shi kike shiyasa kike min gadara to wllh sunan aurenki matacce, tab'e baki jannat tayi wannan ne kuma baki isaba sbd Allah shiyake da ikon komai ba wani ba, sannan niba sunana jennifer ba sunana jannat kada ki kara kira na da wannan sunan rufemin baki kona wanka miki mari jidda ta katseta,ba'a canxawa tuwo suna agurina har gobe sunanki Jennifer dashi zan kiraki, jannat ta galla mata harara ba mmk dan daga ganinki baki san ciwon jikinki ba idan kin saba hada jiki da ballagaxaxxu irinki nidai ba ballagaza bace kije kiyi da wanda kika sabayi dasu ta wuce afusace jidda ta kuma janyo hijab dinta, ki kare min kallo kinga nayi kala da ballagaza ?? wannan kuma ke xaki ba kanki amsa dan baki isa na kalleki ba, sakin hijab dinta tayi wllh baxan iya kishi da yarinya karama irinki ba akan ya khaleel babu abinda baxan iya ba banza yar tsintuwa mara asali, har jannat ta juya xata tafi ta dawo baya, meyasa kika bari mara asali ta rabaki da wanda kikeso ? alhmdllh ina gdw Allah da yayine a haka bani da asali amma ina tsoranshi kuma ina alfahari da jarabawarsa agareni dan nasan mumini na kwarai ake jarabta keda kike yar asali ni da bnda asali bamu da banbanci tunda dukkaninmu yan adam ne kuma mata, ta wuce ta barta anan tana mmkin ta batayi tunanin tana da baki haka ba da gudu ta karasa daki wajan ummanta tana xuwa ta fada jikinta ummana zan iya mutuwa,bakin ciki xai kasheni umma tunkina da ranki bakin ciki xai halakani araxane umma take jijjigata me ya faru jidda ? menene ? sai da ta gama kukanta hnklin umma atashe ta rarrasheta ta kwashe karya da gasky ta fadawa umman, ran umma ya baci sosai kwantar da hnklinki y'ata khaleel xai xama naki ki juyashi son ranki na miki alkawarin sai yadda kikayi dashi

by

*Ummee Garkuwa*

[9:10PM, 12/8/2016] Fatima Garba:
'<Øûß
'<Øûß
'<ØûßJENNIFER
'<Øûß
'<Øûß
'<Øûß

65&66

Ngd ummana ina son ya khaleel yaji ni kad'ai yakeso arnsa bana son kishiya ummana araba auren khaleel da Jennifer,

Share mata hawaye ummanta tayi cikin kwarin gwiwa kada ki damu da wannan jidda ni kaina ban xauna da kishiya ba balle ke guda daya tal koxan tafi tsirara sai na cika miki burinki bani da farin cikin da ya wuce naki ki kwantar da hnklinki zanje wajan malamina na nan kano ya iya aiki kamar yankan wuk'a duk xasu Sani dukansu dariya jidda tayi cike da farin ciki Dan tasan ummanta ta akwai bin yan tsibbu babu abinda baxata iya ba, idan xata sama mata farin ciki,

**********

Washegari da safe sulthana tana breakfast dinta ita kadai sbd bata tashi ta wuri ba tana cikin yi zahra taxo kanta tai k'erere tana mata kallon raini, Jennifer dama baki da kuny'a?

Tunanin zahra ko jannat ce, tacigaba da cewa,

jiya Anty jidda ta fada min kin mata rashin kuny'a kina mata gadara da kina auren ya khaleel idan ma banda k'addara me ya khaleel xaiyi dake ? Mtswww banxaye marasa asali Anty jidda ba sa'arki bace sai dai ni kiyi dani banda ma jaraba da shishshigi ku xo gidan mutane Ku tare ba dangin iya ba na baba keda wasu banxayen yan uwan.......... Marin da sulthana ta wanka mata ne yasa ta yin shiru bata k'arasa ba dai dai lokacin da jidda da ummanta suka dawo daga unguwar da suka tafi tun duku dukun safiya, da sauri jidda sukayo wajan ita da ummanta, umma tai wa sultana wani katon xagi, Dan ubanki me ya Sa kika mareta shegiya dangin dangi ro kixo gidan mutane kina cin arxikinsu har ki daga hannu ki mareta ? Ke y'ar gidan uban waye ? Koda yake ke kanki ba kisan kanki ba balleki San ubanki,

wani mugun kallo sulthana tai mata, ke kika damu da wannan abinda nasani ke mutun ce ni ma mutunce kuma haihuwa ta akayi ba daga sama na fado ba rashin kunya tai min shiyasa na zabga mata mari saura waccen muciya da xanin, ta nuna jidda, sakin baki sukayi cike da mugun mmk, umma tace kan bala'i daga cin arxiki kixo gidansu kina cin arxikinsu kike wannan zak'ewar?

Rik'e k'ugu tayi su arxik'in ubanwa suke ci ?

Ke ina mgn kina mayar min ni sa'arkice

Fari tayi da ido kema ba girmama na sama dake kike ba, ta murgud'a baki, jidda cikin tsawa tace, ke Dan ubanki ummana kike fadawa wannan mgnr, kallon banxa sulthana tai mata ita ummantaki meyasa ta fada min mgn ?

Dalla rufemin baki kixo gidan ubanmu kike k'ok'arin takamu to ba ki isa ba,

A wulakance sulthana ta ya mutsa fuska ubanki ko uban wasu ? Me ya hana ki xauna gidan uvanki kiyi gadara dashi nan gidan uban wasu ne ba naki ubanwa,

Umma ta kwatsa mata tsawa wannan yarinyar baki da tarbiyya,

A ya tsine tace ga Mara tarbiyya cen kin Haifa data kebin saurayi daki tana shishshige masa yana wulak'anta ta,

Hannu umma tasa akai lallai bashir ka kwasowa kanka masifa,

Kiga masifa akanki shi da ganin masifa har abada

Baxata sab'uba dole yaya bashir ya kori yaran nan tunda basa girmama manya

Kema ba girmama su kike ba kuma xama gidan dady daram ba shegiyar da ta isa ta koremu,

Salati umma tasaki

Da karfi xuciyar ta kamar ta fashe Dan takaici batayi tunanin cin mutuncin daga gun yaran ba,

Daga kaina kin daina nuna mutane da yatsa xaki gane kuranki sai nayi kaca kaca dake,

Oho wannan kuma ke kika yadda dashi avinda na yadda dashi Allah shine mai komai ba bawansa ba,

Momy da dady suka sauko daga sama cikin tashin hnkl umma tana ta zage xage jidda tana rik'e da hannun zahra tana xubar da hawaye Dan marin ya shigeta, hindu ta sauko jannat na tsaye akan upstairs tana kallon rigimar

Hindu Hannun sulthana ta rik'o tana ja dady yace

Subhanallah sulthana me ya faru ?

A kufule tace dady Dan kawai bamu san iyayen mu ba sai a tsanemu ? Waccen banxan zahran tunda mukaxo gidan nan take mana kallon raini shine yanxu take xagin Anty jannat wai Mara asali shegiya wllh dady banda sulthana y'arka ce kaida Momy dana koya mata hnkl, girgixa kai dady yayi to shikenan muje sama ya sata agaba had'e da galla wa zahra harara, sakin baki umma tayi cikin d'aga murya tace yaya bashir ina son mgn dakai bai waiwayo ba yace anjima xamuyi mgnr yanxu zan rarrashi sulthana, salati umma ta saka

Momy ma hararar zahra tayi had'e da k'wafa tai sama

Nashiga uku ni hadiza xama tayi akan kujerar dining had'e da cire d'an kwalinta cikin tashin hnkl tabbi jam ! Wannan masifar har ina ga y'arka data sha mari katafi lallashin wata cen futsararriya, way'an nan yara basu bar yaya bashir haka ba dole akwai k'ullalliya, xonan zahra kiyi hkr na fuskanci yanxu dadynku ta way'ancen shegun y'ay'an yake kaf sun juyar masa da hnkl wllh munsa k'afar wando d'aya dasu baxan bar gidannan ba har sai na karya wannan asirin ina xama bai kamani ba,

Daki suka shiga dukansu, jannat tace sulthana meya Sa kika mari zahra ? Haba sulthana ana barin halak dan kunya kada ki manta tarin alkairan iyayenta akanmu,

Tsaki sulthana tayi Anty jannat baxan iya jure cin mutunci ba kawai ina xauna ina breakfast ta hau xaginki tunaninta ko kece dama haka suke miki wannan cin mutuncin ?

To idanke kin jure kin San ni ba xan iya jurewa ba,

Hindu tace abinda yafi damuna sulthana ki xage kina fada da babbar mace bafa sa'arki bace ki k'yaleta ko Dan girmanta,

Baxan iya bane kun San halina kun San yanda nake idan ina cikin wannan halin bana iya tantance babba da k'arami hkr ne kawai banda shi amma bana Neman rigima muddin kuwa ka tab'ani sai kayi Dana sani, jannat tace Allah ya kyauta suka amsa da amin

***********

Da yamma suna xaune a falo dukansu bayan sungama dinner umma cikin ya tsina tace Ibrahim, yad'ago kai ya kalleta, meya had'aka da y'ar'uwarka ? Kana son nuna banbanci tsakaninta da Jennifer ? Kasani fa xaka iya rabuwa da Jennifer jidda kuwa har abada yar'uwarka ce, katseta yayi,

umma plx kidaina min fad'a agaban yara ? Ya kallesu fuskar shi a d'aure Ku tashi kuba mutane waje, kowacce tashi tayi tabar wajan,

Ya dawo da kansa wajan umma, ta cigaba da fad'anta haba Ibrahim kafin kasamu Jennifer wa ka fara samu kashe wayarshi yayi daya ke dannata, umma ya kira sunanta, jannah matata ce jidda kuma k'anwatace baxaiyi yu nak'i kowaccensu ba sbd d'aya sannan abaya na fad'a miki kuma kin Sani yanxu ba Jennifer bace sunan Momy gareta ta musulunta, ya mik'e tsaye ni bana son mgn akan abu d'aya me jiddan tace na mata ? Ko ma menene bai kamata kina min fad'a agabansu ba ya fice ta bishi da kallo cike da mmki, innalillahi wa inna ilaihi raji'un ta kalli momy, Firdausi ki biya malaminki, momy murmushi tayi ta mik'e ta bar mata falon gaba daya hnklinta yai mummunan b'aci kai ta dafe dole tai musu gagarimin aiki Dan idan tayi sake wataran khaleel xai iya mata cin mutuncin da batayi tsammani ba

2days ago

***********
Chapter 40 · 0% Book details