← Book details Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 85

Sashe 45

Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wani axababban hawaye ya sauko mata haka ta dinka jin xubar hawayen kamar fanfo sam takasa tsaida hawayen, daga kanta tayi ta kalli sama cikin xuciyar ta tana addu'a akan Allah ya kawo musu sauki, ya Allah ka tsare bayinka ya Allah ka karemu daga sharrin makiyan mu wayanda muka sani da wanda ba mu sani ba gareka na dogara kuma gareka nake neman taimako ya Allah ka kara tsaremu daga dukkan abinki Allah kada kabawa makiya nasara ya Allah ka rushe mummunan nufinsu akanmu, haka ta dinka jero addu'o'i kala kala tanayi tana xubar da hawaye sam tarasa gane laifin da sukai da ba'ason haduwarsu da iyayensu, tanayi tana girgixa kai sbd abun ya matukar dauri mata kai, haka su momy suka dawo suka tadda ita cikin wannan yanayin, arud'e suke tambayarta, ta kwashe labari ta fad'a musu xama sukai awajan suna mmk da ta ujjibi kansu gaba daya ya daure, kowacce tagumi tayi tana mmkin yadda alamarin yake tafiya arikice da kyar momy tace wai ni way'an nan mutanen way'anne irin axxalumai ne ? dole musa matakan tsaro sosai a gidan nan salati kawai take nanatawa da kanta tashi taje wajan danjuma tai masa gargadi kada ya kuma barin wata tashigo gidannan sannan duk wanda ya tambayeshi jannat yan biyune yace ita kadaice agidan a tsorace ya amsa mata dan shi gani yake kamar ya tafka wani babban kuskure na barin matar ta shigo yai wa momy rantsuwar baxai kuma barin wani ko wata tashigo sai da ixininsa balle ya basu lbrn jannat su ukune, ta dawo ta samesu suna kuka sun rungume juna tausayinsu ya kamata ta dade akansu ba su san taxoba surutai sukeyi na jimamin halin da suke ciki da kyar ta lallashesu sukayi shiru suka koma falo babu wanda ya iya yin lunch aranar duk a tsorace suke, sai yamma dady ya dawo ganinsu cikin jimami yasa ko d'akin shi baije ba ya xauna ya na naxarinsu yasan akwai bak'on al'amarin daya shigo cikin gidan, da kyar momy tace,

alhaji narasa gane laifin daya rannan sukai akeson wulakanta su akeson tarwatsa rayuwarsu,hawaye ya xubo mata koma waye Allah ya isa,

ta kwashe lbr ta fad'a masa xura mata ido yayi cikin mmkin xancen nata,

ya girgixa kai, wannan abin yana matuk'ar bani mmk wannan somin tab'in tonuwar asirin koma waye tabbas asirinsu ya kusa tonuwa, karfin addu'a ne yake fito da wayannan misalan, firdausi makiya basai ka musu komai ba wasu ma basu da dalili xasu ji kawai sun tsaneka bakuma xasu barka haka ba har sai sundinka jifan ka da sharurruka iri iri dana baki dana karkashin kasa kai dai babban burinka Allah yai maka tsari daga sharrinsu, kuyi hkr yayana jarabawa ce bakusan irin baiwar da Allah yai muku ba nan gaba, Allah baya jarabtar mutanen banxa sai na arxiki koma wanda Allah xaiwa wata gagarumar baiwa duk wani k'usa kowani shahararre baya xama haka banxa sai Allah ya jarabceshi ya gwada imaninka gwargwadon imaninka gwargwadon jarabawarka da kuma shahararka,

kuyi hkr kuxuba wa sarautar Allah ido shiru sukayi suna jinshi suka d'ai suka san irin bakin cikin dake cikin rayuwarsu da kyar ya rarrashesu da nasiha suci abinci, cin abincin suke tamkar suna xuba wa cikinsu mgn kowacce ta kagu tasan kanta takuma san wanne irin abu taiwa mutanen nan da suka jefa rayuwarsu a wahala suka hanasu jin dadin duniya,

************

da daddare tana kwance bayan ta idar da sallah shafa'i da wutr tayi lamo kan gadonta xuciyar tana jinta wata iri tmk mad'aci sam bata san shigowarshi ba sbd dogon tunanin da ta tsinci kanta aciki jitayi an rungumota asanyaye ta kalleshi yai mata murmushi kad'an ta kauda kanta hade da ajiyar xuciya da ita kadai tasan tayi ta kwantar da kanta yayi ajikinsa, cikin muryar lallashi yake mata nasiha had'e da lallashi tayi lamo ajikinsa dan dai dai kunnanta yake mata mgnr tana jinshi kuma nasihar tana ratsata sun kai kusan 11:00 na dare yana lallasarta har sai da yaga ta gamsu da nasiharsa dan jikinta yai matuk'ar sanyi haka ya kwantar da ita ajikinsa tamkar yar baby a hnkl a hnkl bacci mai nauyi ya fusgeta,

***********

ganinta tayi cikin wani rami ita dasu sulthana da hindu suna gudu xasu fita daga ramin kag da xasu fita suka ga wannan matar da tagani a mota ta taho da gudu itama daga wani gefe na jikin ramin tana ce musu koxo yayana kuxo na ganku kada a rabani daku saura kiris taxo kusa dasu wasu mutane suka xo wajan fuskokinsu a daure basa iya ganinsu suka biyo su, suka rirrik'esu wasu suka rik'e matar wasu suka rik'e su tana ihu ga mutane birjik amma sunki suxo su cetosu firgit ta farka da sauri ya rungumeta gam ajikinsa tuni gumi ya jiketa fincike jikinta tayi daga nasa tana nishi da ajiyar xuciya wani irin kallo yake mata, beautyna menene? kallonshi tayi idonta cike da hawaye ta girgixa masa kai muryarta na rawa tace, nayi mummunan mafarki, mik'ar da ita yayi shima ya mik'e ya nuna mata agogo 3:59 muje muyi alwala mu fad'awa Allah bukatarmu kiyi addu'a sosai dan haka annabinmu ya koya mana duk lokacin dakayi mummunan mafarkin anfison katashi kayi sallah raka'a biyu kayi addu'a sosai akan Allah yai maka tsari da abin ki na cikin mafarkin ya kuma sadaka da alherinsa dan shi mafarki bushara ce babba, alwala suka d'auro sukayi nafilfili har asuba sannan yabar d'akin nata,

************

washegari misalin 1:0 tana daki hannunta rik'e da kur'anin mai ixfi takwas dan shi ake koya mata karatu tana ta hadda dan tayi nisa sosai hayaniya taji sosai a falo ta k'arasa karatun ta ajjiye kur'anin ta sakko falon abinda tagani yasa gabanta fad'uwa umman jidda ce da d'ayar matar nan da suka xo kwanaki da kuma wata daban amma tana kama dasu dady sun sa momy agaba suna xabga mata ruwan masifa tayi tagumi tana kallonsu d'aya matar da bata tab'a ganinta ba cikin masifa take mgn, kinga firdausi shiyasa bana xuwa gidannan yaya bashir wana ne amma sbd ina bakin cikin naxo na ganki cikin gidan nan yasa bana xuwa duk girman wannan gidan ace ke kadaice ? sbd mugun abu sannan kin kwasu wasu shegun yara kin kawo su gidan nan da xummar wai taimako har an daura wa daya daga cikinsu aure da Ibrahim mu bamu sani ba sai aka fake da auren gaggawa to bamu san da wannan yarinyar ba kuma har avada bata cikin danginmu auren shi da jidda kawai muka sani, shiyasa muka had'u kanmu mu nuna namu ikon, da sauri jannat takoma baya dan batasan d'orawa kanta wata damuwar wacce take cikima ta isheta d'aki ta koma tasaki wani marayan kuka ta durk'ushe bakin kofa cikin wani mugun yanayi kuka take sosai tana mmkin wannan wahalalliyar rayuwar data ke ciki su kam ai abin tausayine lallai cikakken mai imani dole ya tausaya musu dan suna cikin wani mugun yanayi wanda duk bai tausayawa rayuwar ba imaninshi ragaggene son xuciya ya hana yan'uwan dady gane cewa su na buk'atar taimako, haka tai ta sambatu hindu ce ta shigo hannunta rik'e da na sulthana tana ta haki da fusge fusgen hindu ta kyaleta taje taci mutuncin matan da sauri jannat ta tashi ta rufe kofa tamau tana kuka, plx sulthana kiyi hkr ya xama dole a goranta mana danmu abin gorine ki barmu da abu daya ki kyalesu Allah yana jinsu yana kuma kallonsu ramuwarki sam bata da amfani, itama sulthanan fashewa tayi da kuka anty jannat na fasa xuwa nikad'ai nasan me nakeji araina xuciyata kamar ana babbaka wuta haka nakeji wayannan mutanen magangamin su nasa naji na tsani kaina na tsani rayuwata, karar wayar hindu sukaji ta amsa wayar, osasa plx mu hadu dakai agidana na hotoro, araxane suke kallonta kasa daurewa jannat tayi, idan kinh hadu dashi me xaki masa shiru tayi bata amsa mata ba, a kufule sulthana tace malama mgn ake miki kina da kudin daxaki iya biyanshi banxa still ta kuma yi musu, gidan ubanwa xakije ki samu kudin ? uban me xaki fad'a masa idan kun hadu?

ubanki xan fd'a masa ! tafad'awa sulthanan cikin tsawa da fad'a kina min mgn kamar wata y'arki ta xaro ido cikin wani mugun yanayi ta koma da sak tana kallonsu tana nunasu da yatsa, kada wacce ta kuma shiga rayuwata babu wacce nake tmbyr ta abinda bai shafeni ba kuyi harkarku nayi tawa, dama kuna yi min kallon wata bare a cikinku kuyi rayuwarku kada ku shiga tawa ta mik'e ta rab'e ta jikin jannat ta bud'e kofa ta fice da mmk suka kalli junansu, suna xubar da hawaye,

***********

da daddare bayan sun gama dinner gaba d'ayansu sun koma falo, cikin isa matar da jannat bata tab'a ganinta a gidan ba tafara mgn yaya bashir gamu munxo da tamu mgnr muhimmiya akan sa ranar jidda da Ibrahim da ance sai bayanta gama nysc dinta to yanxu mgn ta tashi mun dawo da sa ranar sati uku mai xuwa, kowannansu sai da gab'ansu ya fad'i, tunda ta fara mgnr yake danne dannen waya jin ta ambaci bikinshi da jidda nan da 3 weeks ya mik'e afusace ya fice daga falon, ta kalleshi akai kaice cike da mmk iyyye ! sannu Ibrahim lallai na yarda hadiza ba'a bar yaron nan banza hk ba, ta dawo kan dan'uwan nata yaya bashir me xaka ce? murmushi yayi yana jin takaicin bakin hali irin na kannansa me zance Aisha ? ku iyayensa ne kun gama mgn Allah ya kaimu ranar, ya mike kana kallonsa kasan yayi mgnr ne amma ba ta kai xuciyar saba, ya wuce bangarensa, wata guda umman jidda tayi ta kalli su jannat dan bata iya tantance su ta galla musu harara jaraba kike ko Jennifer sai adaina yiwa y'ata gadarar aure dan itama nan da 3 weeks xata zama amaryar sa sai ki mutu dan bak'in ciki ta dawo da kallonta wajan momy hjy firdausi kinga tamu isar ko ?
Chapter 45 · 0% Book details