← Book details Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 85

Sashe 28

Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Iska ya fitar daga bakinshi bazaka ganeba Nabila bata da kamun kai dalilin dayasa nake son jenny yarinya ce karama akansu bata kaisu ilmiba har yanxu a 0 label take wannan year din tagama secondary fa amma tafisu aji da kamun kai babu jan ra'ayin da man mata ba amma har yanxu takasa ce min tana sona yai tsaki bana son mace ta dinka hauka akaina koda tana masifar sona nafison ta dinka Jan aji haka nakeso, hakane khaleel wasu matan soyayya tana Sa su manta kansu, yanxu ya xakayi da auren Jidda ka Jennifer ? Gyara xama khaleel yayi yace jenny is too young kona aureta yanxu renonta zanyi, dariya sagir yayi ko kuma ita tare neka ba, dariya shima yayi kasan dai zahra itace autar mu ko ? To nesa ba kusaba ta girmi jenny, kaga dole sai reno, sagir ya buce da dariyar keta ina jiye mk abu daya ranar da yarinyar nan xata rikita ka, wani kallo ya jefa wa sagir anfada maka ni mayen matane irinka kajira kaga abin mmk nan da wata daya zata furtamin tana sona da kanta, wata dariyar sagir ya kumayi, ko kuma kai ka fada mata kana sonta ba, sagir bana son iskanci kaifa shege ne tayaya da girma na da ajina zancewa yarinya karama ina sonta ? Kana ganin xan sauya ne yadda nake ? Kaxuba ido xaka sha mmkina,

Sorry abokina yanuna idonsa wannan shine nawa, amma fa kasani soyayya ba'a yi mata alwashi,

Tsaki khaleel din yayi ya janyo musu wata hirar

***********

Bayan ta fito da ga wanka ta sauya kaya Momy tashigo dakin jenny kin shirya ? Eh Momy, OK in shaa Allah anjima malan Dr Ahmad Sani ningi xai xo kamar yadda muka tsara xai baki Kalmar shahada,

Wani dadi ya kama Jennifer, toh Momy ina jiranshi, tare suka jero suka sauko kasa babbn parlourn gidan suka xauna, Jidda da zahra suna aika mata harara, ta lumshe ido bata damu da kiyayyrsu ba sam dan tasan rayuwa baxta yiyu kowa ya sokaba dole akwai makiya, suna nan a falon suna hira jefi jefi ya khaleel yai sallama shida wani babban mutun gaba daya falon suka mike suka gaishe shi cikin farin ciki da fara'a ya amsa ya xauna yai sallama suka amsa masa,

Wacece acikin ? Suka nuna ta kanta akasa, baiwar Allah meyasa xaki musulunta ? Hawaye ya taru a idonta cikin rawar murya tace sbd nayi imanin shine addinin gaskiya sbd adalcinsu da mutuncinsu da taimakokon juna tun ina yarinya karama nayi imani da Allah na kuma yadda addinin musulunci shine addinin gaskiya,

Alhamdulillah, mungodewa Allah yanxu xan baki Kalmar shahada kafin nan zan fada miki rkunnan musulunci da kuma ahikanshi imani, addinin musulunci addinine na amince da salama da taimakon juna da kaunar junanmu, rukunann musulinci ya kasu kashi biyar Wanda dolene sai ka amince dasu xaka shiga addinin Allah

1 shahadatu an LA ilaha illalha wa'anna Muhammadan rasulullah

2 tsaida sallah

3 bada zakka

4 yin axumin watan Ramadan

5 da xiyartar dakin Allah .

A keeda ta muslunci tushenta shine imani da Allah, da mala'ikonsa, da littattafansa, da manxanninsa, da kuma ranar lahira, da yadda da akddara me Kyau ko mummuna

Lallai wannan magana da kika fadamin ta cewa tun kina yarinya kikai imani da cewar addinin Allah shine addinin gaskiya sai kika tunamin da hadisin manxon Allah (s.a.w) daya ke cewa, maa min mauludin illa yuladu alal fidrah, babu wani abin haihuwa face an haifeshi da imani ga Allah, fa abawahu, har sai iyayensa yuhawwidani au yunassiranihi aw yumajjisanihi, sun kasnce yahudawa ko banasare ko majusawa,

Wannan ba abin mmk bane dan dan malaman tauhidi sun kawo wannan, fa inna kulla maklukin kad fudira alal imani bi kalikihi min gairi sabqi tafkeer au ta'alim, Allahu akhbar, haka Allah ya ke halittar kowa da imani dashi batre da wani tunani ko koyarda shi ba, Alhamdulillah, Alhamdulillah Alhamdulillah. Ikon Allah ya wuce komai dan shiyake shiryarwa kuma shi yake fidda haske daga cikin duhu, baiwar Allah duk kin amince da hakan ? Cikin gwarin gwiwa tace eh Malan na amince, yai murmushi yace to Alhamdulillah, zan fada miki Kalmar shahada kamar yanda nai miki bayani afarko, duk abinda na fada sai ki maimaita Ash'hadu an la ila ha illallah ta bude baki da murna hade da imani harshen ta ya karye taji wani irin abu ya rufe mata ido da kyar tayi kokarin juya harshenta ta kasa bata San lokacin data mike tana kakari tana son maimaita wa gaba daayansu sukayo kanta luuuu tai kasa kafin ta karasa kasa ya khaleel ya riketa yana jijjigata dif yaga idonta ya rufe numfashinta ya tsaya cak cikin tashin hnkli suke jijjigata

By

*Ummee Garkuwa*

For comments

08037251895

[7:22PM, 12/5/2016] Fatima Garba:
'<Øûß
'<Øûß
'<ØûßJENNIFER
'<Øûß
'<Øûß
'<Øûß

47&48

A matukar raxane ya khaleel yake jijjigata da karfi yana kiran sunanta Malan ya mike yana mmkin al'amarin ya kalli idonta yaga yana motsi yayi ajiyar xuciya naya dan yagane inda matsalar take dukkamsu hnklinsu na kanta musamman Momy da ruby, Malan ya kalli ruby yace taje ta debo masa ruwa acikin cuf, da sauri ta tafi, bata dabe ba ta dawo ya amsa ya yayyafa mata bayan yai mata addu'a har yanxu bata bude ido ba, numfashinta ya kawo da karfi idonta arufe yana motsi, Malan yace nayi mmk sosai Ku xauna, Ku kwantar da hnklinku xata tashi babu abinda yafi karfin addu'a xama sukayi xuciyoyinsu cikin dimuwa, har yanxu tana hannun khaleel yakasa sauketa gani yake yana sauketa wani abun xai kara faruwa da ita,

Malan yace, dama tana da wata matsala ne ? Jikin Momy asanyaye tace gaskiya ban Santa da matsala ba lfy lau take, yayi Jim yana juya xancen yace to xata tashi inshaa Allah xuwa kuyi hkr idan ta tashi ta samu nutsuwa xamuji daga bakinta, kuma akwai wasu tambayoyi da xammata in shaa Allah xamuyi wa tubkar hanci, kada Ku damu, ya mike tsaye ya mikowa Ruby sauran ruwan addu'ar yace sukara shafa mata duk yadda ake ciki suyi waya kafin ya tafi sai da ya kuma yi mata addu'a ya khaleel ya dauketa, so Momy suka bi bayanshi ya sauketa a dakinta jigum sukayi hade da xuba mata ido ransu ajagule

Some hours letter

Har dare bata bude ido ba gaba dayansu suna dakinta kowanne ranshi ajagule haisam da mahbobb duk sunyi cirko cirko kowanne da abinda yake sakawa uban gayyar kuwa ya rasa kalar tunanin da xaiyi addua'a yake xabgawa ubangiji Allah ya tashi kafadun jennynsa, Malan Dr Ahmad Sani ningi ya dawo, har dakinta sukaje, cikin mmk yace wannan abu da muni yake nayi mmkin rashin bude idonta, Momy tace wllh Malan babu me kwanciyar hnkl acikinmu, mun rasa wane kalan tunani xamuyi kan mu ya daure tamau kwata kwata jenny bata tabayin irin haka ba, wani irin tari Jennifer ta fara yi da atishawa me karfin gaske idonta a rufe take yinsu, hnklinsu yadada tashi addua malan yai mata sannan ta daina sai kuma hamma, girgixa kai haisam yayi Momy kuyi hkr akwai abinda muke boye muku nida Jennifer amma yanxu dolene kusani jenny plx ki gafarceni yaxama dole su mom su Sani sbd awarware matsalar jikin khaleel ya fara rawa wani kishi mai karfin gaske ya taso masa ya cikumi wuyan haisam cikin fada da tsawa yace me ye atsakanin Ku Wanda kuke boyewa ? Menene ? Araxane Momy ta mike cike da mmkin khaleel din, kana lafiya kuwa khaleel ? Kasa keshi, cikin fada da jin haushi yace mom plx ki kyaleni, tayaya xasu munafunce mu su kintsa wani abun batare da sanin mu? Kasa keshi nace ! Da karfi yasakeshi har sai da haisam yai baya, ran khaleel ajagule gani yake ko soyayya suke shida ita, to me sukeyi ? Wani irin yanayi Mara fisaltuwa yaji shi aciki,

Momy tace muna jinka haisam girgixa kai haisam yayi cike da jin haushin dan'uwansa ya kwashe lbrin komai ya fada musu jinjina kai Malan yayi hade da fadin ikon Allah, kunga inda babbar matsalar take, lallai sihiri mai karfi na bata da kauce hanya hade da babaken jinnu ajikin yarinyar nan dole anemo sauran yan uwanta ayi musu magani gaba dayansu, wani irin shock khaleel yaji hade da danasanin cukumar haisam da yayi yana son jenny shi bakone asoyayya ya kasa controlling kishi mai xafi daya ta so masa, Momy tace amma haisam kunyi yarinta sannan kunyi kuskure, kuyi abu Ku kadai batare da sanin babba ba gobe dadynku xai dawo yanxu xan kirashi a waya na sanar dashi komai, ubangiji Allah ya kawo mana dauki wannan lamari da sarkakiya yake idan kana duniya xakaga abu kaji shi kuma kala kala,
Chapter 28 · 0% Book details