← Book details Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 85

Sashe 52

Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sulthana ta bud'e k'ofa ta shigo da sauri jannat tai k'ok'arin janye jikinta k'am taji ya rik'eta,

Xaro ido sulthana tayi tana in ina tace,

" ah ah yi hkr ta juya da sauri ta fice,

Dago kai jannat tayi had'e da turo baki,

" kaga fa sulthana ta gammu,

Tab'e baki yayi to menene ?

Kefa matata ce,

K'ara turo baki tayi

Hancinta yaja "gyara bakin kona gyara shi yanxun nan ,

Da sauri ta saki fuska suka kalli juna sukayi dariya ta kaiwa kafad'arshi duka kad'an

Accchh ! Ya fada had'e da dafe wajan da ta kaiwa duka "Sai Na rama

Matsawa tayi had'e da xaro ido,

Ya dawo da ita jikinshi,

Suka d'ai suka San yadda sukeji a xukatansu

Ranar alhamis tunda sassafe suke xaman jiran kiran sarki dukkan su suna had'e waje daya, kowa ka kalla cike yake da annuri, shiru shiru sarki bai kiraba har akayi sallar la'asar gaba d'ayansu jikinsu yai sanyi jannat da sauran y'an'uwanta kamar su fashe da kuka shi kanshi dady jikinshi yayi sanyi ya fara jin ba dad'i yana feeling din wasu abubuwa da shi kad'ai yasansu, sunyi jigun a falo wayar dady tai k'ara gaba d'ayansu suka kalleshi,

Sbd gaggawa ko duba number baiyi ba,

Muryar abban A.K Garkuwa yaji

Dr gamu nan muna jiranka kaxo kaida y'ay'anka,

Kashe wayar dady yayi yana kallonsu Ku tashi mutafi,

Da murna suka mik'e suna Allah Allah suga fuskokin iyayensu mota suka shiga suka d'au hanyar gidan sarki

Basu b'ata lokaci ba suka isa jannat da sulthana da Hindu tuni jikinsu ya hau rawa sunajin wani yanayi Na musamman falon ganawa da manyan bak'i suka shiga sarki suka gani da Abban A.K Garkuwa da shi kanshi Prince A.k,

Cikin biyayya suka gaishe da sarki da murna had'e da walwala sarki ya amsa ya kalli prince " jeka kira min su gaba d'ayansu,

Cikin gaggwa ya mik'e ya fice daga falon

Rawar da jikinsu jannat yakeyi ya k'aru suka k'urawa k'ofar falon ido suna kallon isuwar iyayensu,

Bai jima ba ya dawo tare da mutane su hud'u mata uku manyan mata d'ayar turata ake a keken guragu me shegen kyau kamar Na xinare sai Adam ched'en shine farkon shigowa, lokaci d'aya jannat ta mik'e tsaye tana kallonshi kamarsu daya karaf suka had'a ido jikinshi yai masa wani mugun shock, da sauri ya shigo sulthana da Hindu ma mik'ewa sukayi bai kula dasu ba sbd suna cen gefe jannat ce take xaune facing din kofa,

Cikin matukar raxana Adamu ched'e ya nuna jannat da hannu idonshi yayi jaa

" wannan jini nace jikina ya bani tsokata ce,

Dai dai lokacin da sauran matan suka k'araso suma idonsu kan jannat ya sauka wacce take tura tsohuwar a kid'ime ta k'araso da gudu tana kuka, wannan y'atace ta rungomata jikinta had'e da tsurawa fuskarta ido araxane cikin masifaffan kuka tace AFRAH ! wannan afrah tace

By

*Ummee Garkuwa*

[12:11AM, 12/17/2016] Fatima Garba:
'<Øûß
'<Øûß
'<ØûßJENNIFER
'<Øûß
'<Øûß
'<Øûß

81&82

a kid'ime take sbd rikicewar da tayi,daya matar itama da sauri ta k'araso kusa da jannat cikin wani masifaffen yanayi ta rungumota jikinta had'e da fashewa da kuka mai tsuma rai, Adamu ched'e kasa mgn yayi wani farin ciki ya keji wanda bai tab'a jinshi ciki ba, tsohuwar matar da take xaune kan keken guragu,tana wani irin kuka ta mik'e a duk'e tana taka k'afar da kyar ta k'araso kusa da jannat tana surutu mai cike da ban tausayi,

"ashe kafin na mutu Allah xai nuna min jiko kina ashe ina da rabo ?ashe bak'in cikina ya guje daga yau ? wannan ranar taxama ranar cikar farin cikina innalillahi wa inna ilaihi raji'un, la ilaha illallah, subhanallah Allah shine abin gdy, tana fad'a tana wani irin kuka mai had'e da gunji,

hawayen kafi ciwon xuciya ciwo adamu ched'e yayi hawayen ido daya tal,duka wajan xuba musu ido sukayi,

da sauri ya kalli sauran mutanen cikin falon har idonshi ya kai kan su sulthana da hindu da suke ta uban gunjin kuka, a kid'ime ya xaro ido cikin wani mugun chock da ta ujjibi da sauri ya k'arasa kusa dasu yana kallon su cike da mmk, araxane yace "Aysha fateema ?had'esu yayi ajikinsa yana salati da k'arfi yana hamdala,

"Alhamdulillahi bini'imatihi ta tummusalihun, Allah ngd maka, narasa y'ay'a lokaci d'aya kabani har guda biyu, sannan karaba ni dasu ba tare da sun mutu ba ka kara bani kuma still kara bani da ita batare da ta mutu ba, yanxu kuma ka dawo min dasu lokacin da banyi tsammani ba ka axurtani da baiwar ka Allah kaine abin gdy Alhamdulillah,yana surutun ne sam bai san me yake fad'a ba sbd kid'ima da firgici na ban mmk, da rarrafe d'aya matar tak'ara sa kusa da hindu tana gunjin kuka,

"ashe ba afra kad'ai bace y'ay'a nane suka dawo gareni plx idan mafarki nake kada atashe ni akyaleni nayi ta yinshi ina jin dad'in ganinsu a mafarkin har mutuwa ta taxo ta riskeni kada ku tasheni tana rarrafen tana wannan maganganun masu karya xuciya,

itama tsohuwar da rarrafe ta nufo su jikinta na mugun rawa,

tana fad'in "nabilata ba mafarki bane hawayen da muka shafe shekara sha tara munayi ne yaxo k'arshe k'uncin mu ya k'are ayau b'akin cikinmu ya yanke,

d'aya matar da sauri ta mik'e a daddafe bari na xo na tab'a jikin y'ayana masu albarka yan baiwa babu abinda xamuyi wa Allah sai gdy addu'ar da muka shafe shekaru munayi yau ta amso hasbunallahu wa ni'imal wakeel, alhamdulillah Alhamdulillah,

duk wan da ya kallesu sai ya xubar musu da hawaye dan sanbatu kawai sukeyi suna kuka mai gunji da wani irin sauti na ban tausayi,sam sun manta a inda suke,

dady ta maza yayi yagoge guntun hawayen daya sauko masa, shi khaleel kasa jure ganin kukan jannat yayi ya karasa kusa da ita yana lallashinta, sam bata jin me yake fad'a gaba d'aya hankalinta nakan iyayenta da danginsu,

sarkine yai gyran murya dan shi kansa xuciyar sa ta karye momy kuwa tuni ta biye musu suna kukan tare su rubayya da zahra ma kukan suke cike da tausayi mai narkar da xuciya, mahboob da haisam ma xuciyoyinsu akarye suke

gyaran muryar da sarki yayi shi ya fara dawo da hnklinsu suka fara nutsuwa har suka fahimci inda suke dan sun manta sbd yanayin dasuka tsinci kansu ahnkl cikin karyewar xuciya sarki ya fara mgn dan yaga alamar aka dad'e ana wannan maganganun da koke koke tabbas kowa na gurin sai ya kuka,

" alhamdulillah ! Alhamdulillah ! Allah shine abin gdy dan shiya dawo mana da farin cikinmu da yaranmu garemu shekara goma sha tara ana cikin k'unci da damuwa da b'acin rai da tashin hnkl lokaci d'aya kuma Allah ya dawo mana dasu ta hanyar da bamuyi tsammani ba shin baxa kuyi mamakin ganinsu atare lokaci d'aya ba ? wannan wata baiwa ce ta musamman daga rabbil ixxati daga ubangiji mai rahma mai jin kai, yaran nan an sacesu daban daban amma Allah da ikonsa ya dawo mana dasu a tare a had'e alokacin da xuciya ta cire tsammani alokacin da jikkunan mu suka xama tamkar basa tare damu sai ubangiji mai hikima ya dawo mana da jikinmu da farin cikinmu kai Allahu akhbar ! lallai shine gwani sarki mai hikima akan komai mu kuma gode masa da wannan falala da baiwa da albarka da yai mana,

Allah mun gode maka,

ya yi shiru sannan yaci gaba da bayani " adamu nasan kai da mahaifiyar yaran nan a yanxu kun sami kwanciyar hnkl wanda baku tab'a tsammaninshi lokaci d'aya ba cikin wannan ranar acikin irin wannan yanayin shin tashin ku a yau ko asatin nan kun tab'a tunanin Allah xai nuna muku fuskokin y'ayanku cikin wannan sigar ?

fashewa da kuka hajiya na nabila tayi " kokad'an ranka ya dad'e,

shikam adamu girgixa kai yayi dan ya kasa mgn sai yarfe hannu da yayi,

murmushi sarki yayi,

"Allah kenan aduk lokacin da ubangiji ya hanaka abu ka gode masa dan idan ka gode masa to tabbas gaba kad'an xai maka wata hamshakakkiyar baiwa da bakayi tsammanin ta ba lokacin daka fidda rai, wannan shine babban misali addu'a bata fad'uwa k'asa banxa kai tayinta kada kagaji ubangiji yana jinka kuma ya na amsa akwai wahalar da xai yanke maka ita wacce xata xame mk baiwa da farin ciki nan gaba,

ga bayin Allahn da suka had'a maka y'ay'anka adamu su baka lbrn komai,

a kid'ime suka kallesu dukansu, adamu ched'e ya girgixa kai ya cije lebe sam yarasa wanne irin kalan harafi xaiyi mgn dashi cikin girgixa kan ya fara mgn dan muryar shi ma sai da ta canza

" ban san wacce irin gdy zan mk ba kayi min abinda duk yawan tarin dukiyata batai min ba dole na jinjina maka kaxama mutum mai k'ima da daraja a wajena ka xama mutun na musamman wanda baxan manta tulin tarin alherin da kaimin b duk wanda ya kalli yaran nan yasan sun sami gata kasa k'arasa wa yayi dan muryar shi rawa ta farayi tabbas in ya cigaba da mgn xai iya kecewa da kuka, da sauri abban A.k ya dafa kafad'ar shi yana girgixa kai,

a hnkl adamu ya sauke ajiyar xuciya yana magana jikinsa asanyaye,

" kabeeru ina jina cikin yanayin da bantab'a jinsa ba ashe farin ciki iri iri ne ? yau nake tantance yadda kake jin sa arayuwa, zan iya yin komai dan tabbas ina jin bak'on al'amari na musamman atare dani,

hajiya nabila cikin kuka tace,

" bawan Allah kayi mana gata wanda muka kasa yiwa kanmu duk yawan dukiyar mu da yawan danginmu shekara sha tara kenan ana bincike ba'a gano komai ba amma cikin ikon Allah ka dawo mana dasu lokaci k'alilan, kuma dukansu, da sauri d'aya matar tasa gyalenta tana share mata hawaye tana kuka,

" anty ki daina kukan nan yau fa ba ranar kuka bace a wurinmu rana ce ta musamman na Allah ya kawo mana farin cikinmu Allah ya had'amu da yaranmu,

tsohuwar da suke tare ce tayi wani guntun murmushi ta kalli momy,
Chapter 52 · 0% Book details