← Book details Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 85

Sashe 49

Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bai farka ba sai gab da sallar magrub, yana farkawa yaji duk duniya babu wacce yake son gani irin Jidda ya mike da sauri daga kwancen dayake ya fito kai tsaye falon gidan ya shige suna falon dukansu ita da ummanta ta yayyan mahaifiyarta su Hajiya Aisha yana hada ido da jiddan yaji kamar Ankara masa sonta kai tsaye kusa da ita yaje, ya takarkare ya fashe da wani irin axababben kuka da sauri suka kalleshi, umman Jidda tace lafiya kuwa kake danjuma yak'i mgn ya cigaba da rusa kuka da k'arfi haka ysa ya janyo hnklin y'an gidan sukayo k'asa dukansu harda dady da yayi alwala xai fita sallah shida khaleel, da sauri dady yake tmvyr danjuma dalilin kukan fur yaki mgn sai da khaleel yai mishi tsawa, cikin kuka danjuma yace INA MASIFAR SON JIDDA IDAN NA RASATA WLLH MUTUWA ZANYI, arikice suke kallonshi kamar tababbe, Umma tace kan uvancen, danjuma waye sa'anka anan ya rushe da wani savon kukan dayafi Wanda ya fara tun farko Hajiya hadiza ki taimaka min ni kad'ai nasan me nakeji da gudu ya nufi center table ya dauko wukar da ake yanka tuffa ko lemo ya ce, muddin kuka hanani Jidda kashe ta xanyi na kashe kaina caraf ya ruko ta yasa wukar dai dai wuyanta, Jidda ta fashe da wani mahaukacin kuka gaba d'aya sukayo kanshi, ummanta na kuka sosai, Dan danjuma babban hauka yakeyi, dady yai shiru yana naxarinsa, da muryar lallashi yace, tun yaushe kafara sonta ? Ya kalli dady hawaye na xuba yace yanxu bayan na tashi daga bacci,

Mmkin su ya karu nan da nan suka yadda danjuma ya haukace,

Dady ya kuma cewa, kafin ka kwanta kayi shaye shaye ?,sanina baka shan kwaya danjuma,

Girgixa kai danjuma yayi ko kad'an alhaji bana shaye shaye abinci kawai nasan naci kuma megida khaleel ne ya bani shi,

Wani k'aton ashar umman Jidda tayi ta kalli khaleel, a kidime shi kabawa abincin da Jidda ta baka? D'aga mata kai yayi cike da mmki dan duk sun rikici, d'ora hannu tayi aka wayyo na shiga uku ni hadiza, itama Jidda kuka tasaki da k'arfi, ummana naga da sunan Ibrahim a kai aikin, nan kowa ya fahimci abinda ya faru cike da bak'in ciki Mara misaltuwa dady yace innalillahi wa inna ilaihi raji'unn, danjuma meye sunanka na gsky,

Muryarshi na rawa yace iro Ibrahim sunana, da mugun bacin rai dady yace yaci sunan sihirin da kukayi yayi aiki dame irin sunan wllh sai Jidda ta aureshi, ya kalli shi danjuma anbaka ita

I dedicated dis page to u jameela mohd Ali (Maman bobo) happy birthday wish u many many more years masu albarka

[11:36PM, 12/13/2016] Fatima Garba:
'<Øûß
'<Øûß
'<ØûßJENNIFER
'<Øûß
'<Øûß
'<Øûß

77&78

zaro ido umman jidda tayi cike da kad'uwa da mgnr da dady yayi, da rarrashi dady yace, ajjiye wukar danjuma,

jikin danjuma a sanyaye ya ajjiye har yanxu hawaye na xuba daga idonshi danji yake xai iya yin komai akan soyayyar jidda, dady ya kallesu ranshi ab'ace

gaba d'aya kowa yaje yai sallah xuwa gobe xamu tattauna,bana son naji kowa yakara wannan mgnr

ya wuce, jikin kowa asanyaye suka bar wajan, daren ranar kam kad'an ne na gidan suka iya cin abinci sauran kam xuciyoyinsu kamar wuta jidda kuka take sosai,tana jin wani irin tuk'ik'i a xuciyarta,

washegari tun da sassafe baban jidda yaxo gidan dady dan tun jiya dadyn ya kirashi akan yana son ganinsa da gaggawa, haka ya taso hajja mahaifiyarsu wacce bata da lfy tana fama da hawan jini ba kowacce mgn ake fad'a mata ba,

dady ya tara mutanen gidan kaf a babban falon k'asa, kowa ka kalla yana cikin mmk, jidda har lokacin kuka take musamman dataga mahaifinta ita kanta umman jiddan arikice take ganin mijinta yasa ta shiga wani sabon tashin hnkln, danjuma yana xaune agefe ya takure cikin xuciyar shi yana jin takaicin yadda ya tsinci kanshi a wannan halin, cikin takaici mara misaltuwa dady ya fara mgn,

Alhaji musa nasan kayi mmkin kiran gaggawar da nai maka sbd jibi ne ranar da ta kama daurin auren Ibrahim da jidda,

kuka danjuma yasaka Alhaji kataima kamin,

dady ya xuba mishi ido cike da tausayawa, ya kalli umman jidda da harara,

sai kiyiwa mutane bayanin abinda kikayi,

sunkuyar da kanta k'asa tayi hawaye na xuba kunya sosai takamata tarasa ta ina xatai bayanin wannan abin kunyar,

ya daka mata tsawa a firgice ta d'ago kai jikinta na karkarwa wani b'akin ciki mai xafi ya tokare mata kirji,

sam takasa bud'ar baki tayi mgn,

cikin kuka hjy Aisha yayarta ta fara mgn xuciyarta akarye, kayi hkr yaya bashir kuskure ne da kuma kad'dara, shekaranjiya ne mukaje wajan wani malami akan ana so jidda ta mallake Ibrahim, tayi jim cike da danasani muryarta k'asa k'asa had'e da kuka ta cigaba,

shine yai aiki mai karfi ya bamu yace ta xuba masa a abinci ko a lemo in dai yasha to sai yadda tayi dashi dan ko uwarshi tace kada ya kara gaisheta baxai k'ara ba xata maidashi kamar d'anta sai abinda tace,

salati Alhaji musa yayi ya cire hula yana girgixa kai gumi yaji ta ko ina,

momy ma salatin tayi hawayen farin ciki ya sauko mata na Allah ya mayar musu da mummunan k'udirinsu,

jannat ma hamdala tayi ta godewa Allah xuciyarta cike da tsoron Allah, hajja kuka tasaka tana yiwa yarta mugun kallo,

hadiza ina bak'in cikin mugun halinki yanxu ko makiyinki xaki masa haka ? balle Ibrahim daya ke d'anki ? innalillahi wa inna ilaihi raji'unn kin cuceni hadiza kin gama da rayuwarki,ya khaleel daya ke kusa da ita ya riko mata hannu plx hajja yi hkr ki yi shiru, ta rik'e hannunshi sosai sannu khaleel kayi hkr kaji nasan kana da tausayi da imani da taimako shiyasa Allah yake tare da kai, d'aga mata kai yayi, ki daina kuka hajja,

tabe baki dady yayi yana yiwa hjy hadixa mugun kallo cike da tsanarta,

kinga yadda Allah ya nuna ikonsa ko ? Allah baya barin xalunci, Ibrahim d'ankine hadiza idan kin maidani d'an'uwanki kaf d'inku kun tsani firdausi mahaifiyar shi wai ta shanyeni, yar bin bokaye ce da malamai yanxu tsakaninku waye mai bin bokan ? tunda yaran nan suke xaune cikin gidan nan kuke xaginsu kuna aibatasu kuna ce musu yan asiri sbd kawai sun rab'eni,

sam bakwason kowa ya rab'u da jikina,

wannan shine babbar sakayya daga ubangiji yanxu sai ku gane abu d'aya duk wanda yake xaune dakai da kyakkyawar xuciya ubangiji baxai baka sa'ar ka cutar dashi ba,

Alhaji musa ya kalli dady,

Dr bashir yau yaxama dole na fadi abinda ke raina akan hadixa da y'ata hauwa'u ka gansu nan babu wanda na isa dashi hauwa'u ita kadaice mace tilo da Allah ya bani amma sai na shafe wata ko shekara ban sata a idona ba danayi mgn uwarta tace min tana gidanka bawai zan hanata xuwa gidanka ba amma amatsayina na ubanta yadace ace duk inda xataje a fad'amin, amma sbd ammai dani buje dantofi ya jinjina kai ban isa ba sai dai na xuba musu ido, hadixa ta rabani da yan'uwana tace duk mak'iya nane

Dr bashir na fad'a maka hakane dan kagane wannan kad'an daga cikin mugun hali irin na hadiza ta xamemin masifa bala'i a ratuwata narasa yadda xanyi da ita,

innalillahi wa inna ilaihi raji'un lokaci daya dady da hajja sukayi hajja ta k'ara rushewa da kuka , da kyar khaleel ya rarrasheta tayi shiru,

sai a yanxu dady ya tabbatar da hadiza ba k'aramar makira bace gdy yaiwa Allah daya tsare d'ansa daga makircinsu,

cike da jimami dady ya cigaba da mgn,

aikin gama ya gama khaleel Allah ya tsareshi daga wahala baici abincin ba cikin tsautsayi ya bawa danjuma ya nuna danjuman daya ke arab'e yaci abincin sai akayi dacen shima sunanshi Ibrahim,

dalilin haka ya shiga wani mayuwancin hali na kaunar jidda har yana ikirarin muddin aka hanashi xai iya kashe kanshi ya kasheta,

xaro ido hajja tayi hade da murmushin yake tace alhamdulillah Allah nagode maka,

Alhaji musa shima murmushin takaici yayi ya kalli danjuma, kwantar da hnklinka d'ana na baka auren ta kuma yau yau dinnan xa a d'aura maka aure da ita, wani ihu jidda ta kurma hajja ta kai mata rankwashi,rufewa mutane vaki makira ba uban da ya isa ya hana wannan d'aurin auren haka ba wanda ya isa yace baxa d'aurashi ayau ba, ngd maka musa nagd mk musa, haka akewa mutane masu mummunan xuciya ta fashe da kuka, wllh ban wa hadiza wannan tarbiyyar ba cen y'an bariki suka b'atamin ita Allah ya shiryar min dake, kuka hadizan take sosai dana sani na xiyartar ta ta ko'ina,

Alhaji musa ya kalli danjuma fuskarshi na nuna tausayinsa,

kana da sadaki a hannunka ?

asanyaye danjuma ya shafo aljihunsa dan bashi da kudi sai wasu yan canji, da sauri ya khaleel yace xan biya mishi sadakin,

dan shi ya fi kowa farin cikin wannan hadin waskewa kawai yake yana nuna ya damu amma xuciyarsa cike take da farinciki,

danjuma

ya kalle shi ngd oga khaleel

Alhaji musa yace ka katuro wakilinka

kana da mata ?

kanshi a k'asa yace mahaifina ya rasu sai mahaifiyata datake xaune da matata acan garinmu gexawa,

nan garin bani da kowa idan kuma xa'a jira wakilan nawa zan kirasu awaya, dady yace in dai wakiline zan zame maka Allah ya baku xaman lfy,

nagode dady,

kada kadamu danjuma kaima kazama namu tunda xaka auri yarmu,

Alhaji musa yace kana da inda xaka ajjiyeta ?

girgixa kai yayi jikinshi asanyaye sai dai gidanmu na gado na cen gexawa d'aki biyu ne anan matata da mahaifiyata suke xaune,

Alhaji musa yace nabaka gidane da yake rijiyar xaki nan kano ku xauna aciki,

idon danjuma fal hawaye yake gdy,

dady yace zan canxa maka aiki kadawo companynmu Allah ya baku xaman lfy,

fashewa yayi da kuka lokaci daya Allah ya axurtashi ta dalilin wannan auren yai gdy sosai, hajja tace saura waccen ja'irar ta nuna zahra, dady ya gallawa xahran harara itama cikin satin nan zan aurar da ita ga duk wanda na ga dama sbd itama na fuskanci wani irin hali gareta, da sauri hajja tace bakin hali kai,
Chapter 49 · 0% Book details