← Book details Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 85

Sashe 50

Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kai dai baka dashi uwarta ma bata dashi xama da wannan ta nuna hadixa yasa tana k'ok'arin komawa ita sak Allah ya shirye ku addu'ar da xan muku kenan, zahra ta fashe da kuka hajja tabige mata baki yi mana shiru munafuka,

Alhaji musa ya kalli agogon hannunsa inshaa Allah yau ana idar da sallar axahar za'a daura auren ya mik'e tsaye dady yayi addu'a suka tashi ya khaleel ya mik'e shima had'e da kiran danjuman yabi bayansa dakinsa yaje kayan shi da dady ya dinko masa sbd bikin shi da jidda set 30 ya d'auko ya had'a masa da hula da takalma harda agogonsa wannan dady ya siyo masa ya bashi, danjuma gashi nan aje ayi hidimar biki dasu, gdy sosai danjuman yakeyi, shikam ya khaleel farin ciki fal ranshi shiyasa ya had'a kayan da aka siyo masa dan d'aurin auren ya bada su dan ko kallonsu bai son yi tunda Allah ya rabashi da alak'a k'ai

ana idar da sallar axahar aka d'aura auren danjuma sani gexawa da amaryarshi hauwa'u musa kan sadaki nera dubu d'ari biyar wanda ya khaleel ya biya sbd farin cikin daya keji ko miliyan nawa ne xai iya biya Allah ya rabashi da jidda bai tab'a jin soyayarta aransa ba yana kulatane kawai sbd yar'uwarsa ce, wani vangare na xuciyarshi yana wa Allah gdy akan tsareshi da yayi da makircinsu yau jinta yake kamar sallah

tunda saka bar falon hajja take ta musu fad'a da nasiha,

hajiya amina da hjy Aisha da umman jiddan lokaci d'aya suka fita hayyacinsu dan sun bala'in kad'uwa da abinda ya faru lokaci d'aya Allah ya nuna musu ishara hajja tana xubar da hawaye tace,

kun bani mmki dukanku, kun xubar min dak'imata ngd wa da ubangiji da yasa mahaifinku bai ga wannan masifar ba duk irin soyayyar daya nuna muku da yanda ya koya muku kaunar juna, ace har daya daga cikin xai yi yunkurin cutar dan daya innalillahi

da kyar momy ta lallasheta tayi shiru, ta kamata tai bangaren ta da ita sbd rashin lfyr ta ba'a son ranta ya dink'a b'aci,

hjy amina ta kallesu nikam wannan abin yasa ni dana sanin da bantab'a jinshi ba hawaye ya sauko mata sbd haka hajja take xubar mana da hawaye nayi nadama, haka suka dinka tattaunawa a tsakaninsu kowacce tana dana sani k'arara

daki jannat ta shiga ta xaune gefen gadon ta tagumi tayi tana tuna abin kamar mafarki ko shirin film lallai Allah shine mai kare bayansa abincin da ta fita tabar shi adakin ya khaleel ashe bashi da maraba da tarwa tsa farin cikin raywarta ? tasaki ajiyar xuciya sulthana ta shigo jikinta asanyaye tana xama hindu ta biyo ta, sulthana tace wai naga drimer mai ban mmk,abinda ya bani mmk ba wannan ne karo na farko ba lokacin data fara barbaden ni naganta na sauya abincin, sbd bata daddara ba sai da ta kara ni wllh banso asirin ya tsaya akan danjuma ba naso ace wani tutturna baki mai katon ciki da katon baki da mummunan fuska ta samu danjuma dayake bafillace me kyau da yaji wanka murjewa xaiyi, hindu tace, kina da matsala sulthana wananna fa ishara ce kiyi addu'a kawai daga Allah yake ba awajan dan'adam ba, murguda baki sulthana tayi

eh kaikayine ya koma kan mashekiya,

knocking door sukaji a hnkl aka bude kofar suka kalleta jikinta asnyaye ta karaso kusa da su fuskar ta tasha kuka, cikin rawar murya tace anty jannat plx ki ya femin nayi danasani sosai yanxu na tabbatar da dan'uwa suna ya tara wani dan 'uwan naka bashi da abin nema sai jin ka wulakanta wani baren sai ya kaunace ka kaunar da dan'uwanka bai nuna maka ita ba, ki dubi halin da umma taso saka ya khaleel wai ahaka kanwar dadynmu ne, ta fashe da kuka yanxu na gane ku yan'uwane na yadda ku yafemin plx,

ayatsine sulthana tace munji anyafe atashi a k'ara gaba saura ke dan kema sai kinga naki isharan wanda ya tuba dan wuya ba lada, hindu tace, me ye haka sulthana ? ba inda xata dan duk duniya in banda ku bani da wata bayan su, jannat tace bakomai zahra Allah ya yafe mana gaba d'aya, kasa tashi tayi dan kunya ce ta kamata yara kanana sun fita hnkl tasan ko kad'an su jannat ba sa'anninta bane da kyar ta mike jikinta ba kwari ta fice xuciyrta cike da xullumin itama wa xa'a daura mata aure dashi ?

momy tana komawa d'aki ta saki ajiyar xuciya tai hmdl tun farkon soyayyar jidda da khaleel ba so take ba sbd halin uwarta cikin ikon Allah sai gashi Allah ya raba, ta d'ago hannu sama tanawa ubangiji gdy kan tsare mata danta da yayi wayarta ta dauko ta kira kanwarta hjy safiyya ta bata lbrn komai sun dad'e suna hira suna jajanta lamarin sannan sukayi sallama ta tashi ta dauro alwala tai sallar la'asar

da daddare gidan tsit kowa ka gani da abinda ke damunshi

jannat tana zaune gefen gado sulthana tana kusa da ita hindu na xaune kan stool suna hira,

sallama tayi suka amsa mata da mmk suke kallonta, gaba d'ayanta asanyaye take idanuwanta sun kumbura sbd kuka fuskarta tayi jaa ta xauna kusa da jannat ta kalleta tayi wani mugun murmushi kana kallonsa kasan na bak'in ciki da takaicine,

jannat kinga yanda Allah yayi dani ko ?

girgixa mata kai jannat tayi,

kada kice hk jannat wannan abin daya sameni ishara ce babba, dan wannan ya xame min babban darasi wasu guntun hawaye suka sauko mata, ta kare mata kallo, ina mmkin yarinya karama dake amma kin san rayuwa tunda dad'ewa nasan ya khaleel yana sonki,

xaro ido jannat tayi,

plx ina son ki bani shawara dan ni yanxu daga jiya xuwa yau na dauki wani babban darasi arayuwata,

rik'o hannunta jannat tayi, ki daina kuka anty jidda komai kika gani daga ubangiji yake gaba d'aya rayuwar nan a tsare take gun Allah ki godewa Allah kina da iyaye suna gabanki kina kallonsu kina da rabin jin dadin duniya, jidda ta share hawayenta, hakane anty jannat ina son kibani shawarar yanda ya khaleel yake sonki duk da na san rik'akk'en ra'ayi irin nasa,

jim jannat tayi tana tunani a sanyaye tace anty jidda kema kin san shi sai dai mutuna sar da juna dan duk wata mace tasan da wannan,

*biyayya*

itace ke saurin jefa kauna axuciyar mutun idan har xakiyi biyayya ga wanda yake sama dake to tabbas xai k'aunace ki k'auna bata wasa ba,

rashin biyayya shi ke kawo kiyayya da tsana axuciyar mutun

meyasa xakiga wasu matan suna kula da kansu da tsabtace jikinsu da shan magani dan gyara da iya abinci duk wani abu na jan hnkl ta iya tana ganin ita ta cika mace lokaci d'aya mijinta ya kuntata mata yai mata abinda inkikaji sai kinyi mmk, idan kika binciketa sai kinga ne bata masa biyayya amma fa tana kyautata masa

akwai banbanci sosai, duk yadda kike kyautata wa mijinki muddin bakya masa biyayya tofa kyautatawar nan abanxa take,

misali ko baki da miji kina da kanne acikin k'annanki duk wanda yafi miki biyayya kinfi sonshi kinfi son ki kyautata masa haka ma ayayanki wanda yake miki biyayya kinfi kaunar sa haka dangantaka take arayuwa mata plx adage da yi miji biyayya kada ki manta Allah da kansa yace da ace xa ayiwa wani sujjada bayan ni dana umarci mata taiwa mijinta,

By

*Ummee Garkuwa*

[6:53PM, 12/16/2016] Fatima Garba:
'<Øûß
'<Øûß
'<ØûßJENNIFER
'<Øûß
'<Øûß
'<Øûß

79&80

Asanyaye Jidda ta kalli jannat ngd anty jannat nagane rayuwar ma gaba dayanta tana tafiya ne akan biyayya, da babu ita baxa a xauna lafiya ba, ta mik'e hawaye Na xuba, inshaa Allah xanyi aiki da ita, ta kalli su sulthana ngd k'annena ta fice daga d'akin,

Sulthana ta kawo wani gwauron numfashi,

Oh ! Duniya kenan lokaci d'aya Jidda ta koma abin tausayi, tabani tausayi sosai,

Hindu tace, shiyasa idan xaka gina ramin mugunta ka gina shi daidai kai, mace mai ixxa da ji da kai irin Jidda itace take xubda hawaye a gabanmu,

Jannat tace, hmmn ikon Allah kenan abinda kk tunanin baxaiyiyu ba cikin kudirar Allah sai kaga ya faru, damb'ashe shiyar mace irin Jidda ace ta auri danjuma,

Ta jinjina kai ni kaina Na dauki babban darasi abinda ke baka tausayi wataran xai baka tsoro, Allah ya karemu daga sharrin shaid'an, wayarta tayi k'ara tana dubawa taga ya khaleel tana d'agawa yace ta kawo masa abinci wunya yakeji, ta mik'e sulthana ta kwashe da dariya ai maxa kai idan ba haka ba kuma ayi biyu,

Hararar ta jannat tayi ta fita, tana sauka kasa suka ci karo da mahboob daya shigo

"Anty jannat nemanki nakeyi ya fada yana dariya,

taxaro ido mahboob Allah yasa lfy,

" haisam ne ya aikoni wajanki, ta ware ido haisam ?

gyada kai yayi kamar xai tun tsire da dariya,

Akan sulthana wai ki bata hkr yanxu ta daina kulashi,

Lokaci daya sukayi dariya dukansu,

" ni Na isa yaxo da kanshi ya lallasheta,

Xama mahboob yayi akan kujera, abinfa ya dameshi sosai, ki taimaka ina son nai mata mgn Ina tsoran karta taramin jama'a,

Dariya suka kumayi,

"Shikenan xan mata,

"Yauwa anty jannat, ta wuce tana murmushi

Kitchen ta shiga ta had'a masa coffee ta d'ebi abincin ta nufi b'angaren sa sallama tayi ya amsa ta shiga, yana xaune akan kafet yana kallon news,

Ta sunkuya ta ajjiye abincin tacire hijab dinta ta gaishe shi ya amsa yana kallonta,

Ta xuba masa coffee ya amsa yana shaa, ta koma gefen shi ta yi shiru tana tunanin abinda ya faru,

Ya gama sha ta xuba masa abinci yana ci yana kallonta, ya fahimci jikinta asanyaye yake, ya janyota jikinshi, tayi lamo,

"Beautyna me ya sameki ??

Muryarta a sanyaye tace masa ba komai,

Dariya yayi,

"Kina tunanin ankusa rabani dake ko ?

Da sauri ta xamo kanta ta kalleshi,

Daga mata gira yayi,

Ta koma kirjinshi hade da sakin ajiyar xuciya,

Har sai da yaji,

Dad'i yakamashi ya k'ank'ameta ajikinshi, yana jin kamar ana k'ara mishi soyayyarta,

a hnkl ya sa bakinshi daidai kunnanta,

" Allah yana tare damu babu Wanda ya isa raba wannan soyayyar ki kwantar da hnklinki,
Chapter 50 · 0% Book details