← Book details Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 85

Sashe 16

Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yana cikin mota yayi jigum hnklinshi amatukar tashe yarasa inda xasu kaishi tafiya sukai mai nisa sannan yaji alamun xasu tsaya suna tsaya suka fito dashi suka ingixa keyarshi cikin wani waje Wanda baisan ko inane ba suka tsayar dashi hade da bude masa ido ya bude idon shi da sauri ya rufe sbd hasken wajan da yaiwa idonshi yawa ahankali ahankali ya bude idonshi ya sauka a tamfatsetsen falo me dauke da kujeru jajaye da labulaye ja komai na falon jaa ne babu sirki da sauri ya mike yana kallon garadan dasuka kawoshi nan wajan cikin daga murya yai magana me yasa kuka daukoni kuka kawo ni nan ?? Me nai muku suwaye Ku ?? Ko kallonshi basuyi ba bare su bashi amsa haushi ya kamashi yai musu ashar ko xai tunxirasu su kulashi daga karshe ma GAM suka Sa suka rufe mishi baki suka kuma daure masa ido suka ingixa keyarshi cikin wani waje suka rufe

Yana cikin wannan halin xuwa wasu awanni sannan yaji alamar bude kofa suka shigo suka bude masa idanu da bakinshi hade da tura masa plate dankaren da abinci wani mugun kallo yake binsu da shi hade da yiwa abincin kallon ko inkula dam Sam bayajin yunwa asalima halin daya ke ciki baxai barshi ya iya cin wani abinciba xugum yayi yana son tuna wanne irin laifi yai aka kawoshi nan ?? Shigowa suka kuma yi hade da ingixa keyarshi xuwa inda suka fara kaishi da farko maza ne manyan garada xagaye da ita dukkansu suna dauke da muggan bindigu tana sanye cikin wando jeans blue black da riga baka gashinta asake ta Dora kafa daya kan daya kana kallonta xaka hango bindigun dake sarkafe jikin aljihunan wandonta fuskarta amurtuke tana masa kallon tuhuma ya wurga mata harara hade da fadin ke wcece ?? Me kike nufi da rayuwarmu ?? Wanne laifi mu ka aikata miki kike kokarin ganin bayanmu ?? Magana nake miki jennifer meyasa kike wasa da hankalina ki fadamin wacece ke ?? Meyasa kika yaudari yangidan mu kika je musu a matsayin Yar aiki ?? Jennifer meyasa kike bibiyarmu duk inda mukaje ?? Ya fada cikin tsawa da daga murya bata ce komai ba in banda mugun kallo da take binshi da shi nakasa gane miki Hindu a Dubai Jennifer a 9ja Sul........... Yayi shiru hade da rufe kunnanshi sakomakon karar harbi me karfin gaske da sukaji a guje wani katon mutn ya shigo madan da matsala fa shareef al Hussain ya kawo mana hari mikewa tayi adake kowa ya shirya ta nuna daya daga cikin garadan duk rintsi ka maida guy din nan gida ta nuna haisam muje taxaro bindigunta tai waje suka bita haisam ya mike katon nan ya tura shi suka fita ta baruniyar hanya yana jin karar fitar harsashi hnklinshi ya tashi sosai katon yasashi a mota sai da sukai nisa da wajan sannan ya cillo haisam daga mota yatafi ya barshi cikin mutuwar jiki da fargaba ya tari taxi ya maidashi gida da kyar ya shiga gida ya xarce toilet yai wanka ya dauro alwala yai sallolin da baiyiba ya baje a gado yana maida numfashi lallai babu komai afashi face rayuwar wahala da fargabar harin makiya sai yanxu yakejin tausayinta xaiso dalilin dayasa take wannan rayuwar xaiso kuma dalilin dayasa bata cutarda shi ba tabbas da tana son cutar dasu da tuni tayi to meyasa ? Kansa ya daure meyasa bata bashi amsar tmbyoyinsa ba xuwan da su shareef all hussani sukayi ne ya dunkule hannunshi hade da kaiwa iska naushi daren nan da kyar yai barci

Shiru shiru yana jiran ko xata dawo yaji babu alamunsu har ya gama avinda xaiyi baiji dadi ba Sam yaso ace sun kuma haduwa karo na biyu ko dai su shareef al Hussain sun sami nasarar kasheta ?? Gabansa yai mummunan faduwa nan da nan ya tsinci kansa cikin mugun yanayi no ! No ! No ! Baxaki mutuba Jennifer ina bukatar jin ke wacece ?? Yana xaune a airport hnklinshi atashe jikinsa asanyaye dolene yaje yai addu'a sosai a dakin Allah kafin wannan tunanin yafara yi masa illah ahaka ya shiga jirgi yana addu'ar Allah yasa Jennifer tana cikin kwanciyar hnkl muddin tana lfy dole ta sake nemanshi lumshe ido yayi ranshi na suya idan har tana cikin mugun yanayi bai xama lallai ya taradda da ita a saudiyya ba shi dai babban fatansa Jennifer tana nan araye dan yana jin sautin fitar karar bindigar su shareef al Hussain mai ban tsoro da firgici

By

*UMMEEYY*

[7:22PM, 12/5/2016] Fatima Garba:
'<Øûß
'<Øûß
'<ØûßJENNIFER
'<Øûß
'<Øûß
'<Øûß

27&28

Tun xuwanshi saudiyya ya dage da addu'a sosai kullum yana masallaci yana adduar samun falala da kuma rahma awajan ubangiji xuciyar shi tafara haske damuwar dayake ji akan sanin wacece Jennifer ta taragu fiye da da dan da wani irin abu yakeji ya tsaya masa arai kansa ya kulle tunani ma rasa wanne iri xaiyi yanxu kam xuciyarshi tayi tass yasamu kwarin gwiwar da xaiyi binciken asalinta da kuma manufarta na munafuntarsu sai dai tunda yaje basu haduba daya idar da ibadarsa aikin nemanta yake tafiya haryanxu basu haduba

Kwanakin daya kesonyi sun kusa karewa xuciyarshi ta fara taradda din ko shareef al Hussain y samu nasarar kasheta ?? Dam gabanshi ya buga ya salam ! Dukkan mai rai mamacine amma baxaiji dadin mutuwar ta ba yaso ace ta musulunta ta tuba sannan yana son jin lbrinta dafa kanshi yayi shikam baita ba cin karo da wannan al'amarin ba koda kuwa a films tashi yai ya koma masallaci yai addu'a sosai sai dare ya dawo gida ya shirya kayansa a jaka dan gobe yake son wucewa ranso bai soba tunaninshi Jennifer bata raye ya kwanta ranshi abace

Washegari ya shirya ya fito ya hau motar daxata kaishi airport ya sauka daga motar ya shiga ciki

Bayan sungama masa komai ya xauna jiran time dan sai 1 jirginsu xai tashi wata mota ya hango mai Kyau sosai ta shigo tai parking ya kalli motar tai masa Kyau a ido ya kauda kansa ya cigaba da kallon shuke shuken da ke wajan dai dai lokacin daya ji sanarwar passengers wayanda suka da wo daga Egypt sun sauka ya sunkuyar da kansa kasa yana dagowa yaga wata mace mai kiba fara irin farin 9ja ya kuma kallonta yana son tunu inda ya santa wata ya hango sanye cikin riga da wando Pakistan ta yafa kyalen kayan akanta bayanta ya hango baiga fuskarba rungume juna sukayi suna dariya kana ganinsu kaga jin dadi da kwanciyar hnkl waiwayor daxatayi gabansa yai mummunan faduwa da sauri ya mike hade dayin Hamdala ya nufo su yana jin dadin sake ganinta kafin ya karaso har ta budewa babbar macen nan mota ta shiga itakuma ta xagayo tana kokarin budewa ta shiga Jennifer ! Ya kira sunanta ta waiwayo sbd yaxo gab da ita ta galla mishi harara tana mishi kallon raini fuskarta cike da tsiwa meyasa kike wasa da hankalina ? Dakata tace mishi baka da hnkl ya xaro ido yana mata kallon mmk ko kana da shi ?? Ta tambayeshi da rainin wayo shiru yayi yakasa bata amsa dan yasan da rainin wayo murmushi tayi ta bude mota kadan kaji ka kuma gani ta fada mota driver yaja ya wuce mmkinsa ya karo me yarinyar nan take nufi da kadan kaji kadan kuma ka gani ?? Tana nufin xata kuma cigaba da wahalar masa da tunani ?? Girgixa kai yayi zaiyi watsi da son sanin ko ita wacece koma metake son yi musu Allah ya fita hk time yayi ya hau jirgi ransa abace

Daki ta shiga ta xauna kusa da suwaiba tana kokarin kishingida suwaiba hnklinta nakan novel tana karantawa hannu Jennifer tasa ta warce buk din da sauri suwaiba ta kalleta tana murmushi dan Allah bani Jennifer in karasa haba a tsurawa buk ido ba'aji ba'a gani karatun novel kawai hmmm baxaki gane bane bakisan dadin da yake cikin karanta novel ba far Jennifer tayi da ido hade da tungura mata buk din gashi nan ki cigaba da aikin kurawa buk ido da sauri suwaiba ta dauka ta dago kai takalli Jennifer gobe Mr coffee xaiyi tafiya dariya Jennifer tayi hade da gyarama xama ya khaleel ba ina xaije xaibi dadi Singapore daxu ina babban falo zan kunna turaren wuta naji suna hirar Jidda tana ta zabga shagwaba Momy tana lallashinta kinsan abin ban haushi ? Jennifer ta girgixa kai kanshi na kan waya yana danne danne baice cikanki ba abin ban haushi tsaki Jennifer taja su suka Sani suwaiba ta cigaba da mgn nafuskanci khaleel din nan miskiline na karshe ace budurwarka na kukan missing dinka sbd xakayi tafiya ka kasa ce mata komai hmmm tabbijam ina son miskilin namiji amma na Mr coffee yayi yawa ajiyar xuciya Jennifer tayi tana jinjina xancen wayar hannunta ta duba kinga lokaci yayi tashi muje mu fara aiki mikewa suwaiba tayi ta cigaba da mgn duk cikinsu mahboob yafi sauki amma kinga Mr pepper karshe kenan haisam tunda ya dawo dai naga kamar yarage wulakanci Jennifer tai dariya watakil inda yaje ne suka Konya masa daraja dan adam sukayi dariya dukansu suka shiga kitchen dan fara aikin abincin dare
Chapter 16 · 0% Book details