← Book details Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 85

Sashe 19

Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Tun 11: sukaje airport tarar shi Jennifer ma ta bisu dan yanxu sun maida ita tamkar tasu janta sukeyi sosai ajiki sbd sunji tana muradin addinin musulunci itakam taji dadin wannan mugunta ta xahra tunda gashi ta dalilin haka tana samun kulawa da kuma tausayawa tana ganin ta haka ne babban burinta xai ciki 12:10 jirginsu ya khaleel ya sauka suna tsaye wajan masu jira suka hangoshi hannunsa dauke da jakar shi dayan hannun kuma rike da iphat cikin kasaita da isa yake jefa kafarsa Jennifer na hangoshi gabanta ya fadi yayi Kyau yayi haske ya danyi kiba yana karaso wa Jidda tasa kukan shagwaba ta fada jikinshi yayi murmushi ya dan ture ta kadan hade da rike mata hannu yan uwan ma rungumeshi sukayi suna fadin oyoyo 1 week kawai amma kowa yayi missing dinka bai kula da itaba sai da ya kusa shiga mota ya ganta arakube ya kura mata ido bai San lokacin da yace kinyi rashin lfy ne ?? Turus sukayi gaba dayansu cike da mmkin tambayar da yai mata ganin jikinsu yayi sanyi yasa yace kin koma gefe kin rakube kamar Mara lfy oya Ku shigo mota mutafi nagaji ina son hutawa suka shiga mota dukansu suka bar wajan

*******************

Bayan kwna 2 da dawowarsa daga Singapore suna xaune basu Dade da gama yin breakfast va duk da yaga sauye sauye akan Jennifer bai nuna ya lura da hakan ba sbd miskilanci Jidda sai shishshige masa takeyi duk inda ya xauna tana kusa da shi Jennifer tun tana damuwa har tafa ra hkr ta xuba musu ido yauma tana kusa dashi tace sweeter ina tsaraba oh ! Ya fada na manta ke ! Yacewa Jennifer ta kalleshi ya miko mata key din dakinsa kije ki daukomin wata karamar jaka ta amsa tafice haushin shi duk ya kamata ta dauko ta kawo masa ya ciro wayoyi masu Kyau da tsada iPhone last ta wannan year din ya raba musu suka hau murna dukansu abin mmk ya dauko irinta sak ya mikawa Jennifer sororo sukayi dukansu ita kanta Jennifer mmk abin ya bata ciki kuwa har da Momy Jidda kasa boye kishinta tayi ya xakayi hk khaleel ka hada bamu kyauta da Yar aiki zahra ma mugun kallo tabi Jennifer ta shi ita kanta Momy da Rubayya wani rikitaccen kallo sukewa Jennifer ta sunkuyar da kanta kamar ta fashe da kuka tsawa Jidda tayi masa ganin bashi da niyyar amsa mata tmbyrta me kake nufi !? Ya dago kai hnkl kwance ni kikewa tsawa ? Sbd kin maidani danki ko ? Abinda kikeso xanyi ? Xaki iya hidimta min kamar yadda takemin gyaren daki girkina duk itace kifada min kintaba min daya daga ciki?? cikin jin haushi tace ai biyanta akeyi afusace yace ke kike biyanta abinda naga dama shinakeyi bakuma Wanda ya isa yace min danme idan kina so mushirya kibi tsarina idan kuwa ba haka ba ki kuka da kanki ya mike yabar falon tasa kuka ta mike tana sane ta takwa Jennifer hannu harda murxawa tai sama tana kuka

By

*UMMEEYY*

[7:22PM, 12/5/2016] Fatima Garba:
'<Øûß
'<Øûß
'<ØûßJENNIFER
'<Øûß
'<Øûß
'<Øûß

33&34

Cikin mutuwar jiki ta mike ta hau sama suka bita da mugun kallo musamman zahra daki ta koma ta jingina ajikin kofar dakin nata tana kallon wayar me shegen Kyau murmushi tayi najin dadi ta karaso kusa da gadon dakin ta xauna hade da kunna wayan abinda ya bata mmk layin da ta gani na mtn ta xaro ido dariyar farin ciki da kufce mata kwanciya ta yi hade da rungume wayar ajikin taji dadin wannan kyauta ta kuma yi mmkin ta yadda akayi yai mata kyauta iri daya da budurwarshi da kuma kannansa amatsayinta na Yar aiki danne danne ta farayi ta shiga nan ta shiga cen cikin matukar jin dadi ta duba account taga ful da kudi har 30k dariya ce ta kuma kufce mata tayi far far da ido tana addu'ar Allah yasa ka mishi da alheri wayar tai mata duk abinda take bukata ta samu taji dadi sosai ta mike agado ta cigaba da danne dannen wayar xuciyar ta fal farin ciki

********************

Tun daga lokacin suka fara takun saka da Jidda ga yawan sata aiki da takeyi shima kamar ana turashi dan kullum cikin sata yi mishi aiki yake girki gyaran daki da coffee Sam bata gajiya tunda ta saba dashi tana kitchen dafawa yaya khaleel grilled chicken and Indian drink juice Momy ta shigo yawwa Jennifer kin gama ?? Eh Momy na kusa OK yanxu dadyn su zahra yai min waya yana nan dawowa ki gama kixo muyi aikin tare toh Momy agurguje ta gama ta kwashe ta kai masa sannan ta dawo suka hadu suna aikin girkin tarbar dady kamar yadda aka saba basu dade ba suka gama Jennifer ta gyara gidan ko ina ya dau kamshi da sheki

Some hours later

Motocin da sukaje tararsa suka dawo gida ya rude da murnar dawowar dady gaba dayanmu ma'aikatan gidan muka fito mukai mishi barka da xuwa duka yayansa suna jikinsa cikin farin ciki da murna tamkar xasu shiga cikin cikinsa suka mike suka nufi bangarensu Jennifer dakinta ta wuce ta xaune tayi tagumi tana tunanin yanda ta gansu cike da birgewa familyn nan nasu yana matukar birgeta wayar ta ta janyo tayi murmushi duk lokacin da kalleta sai taji farin ciki ta kuma tuna da yaya khaleel

***************

Bayan kwana 2 da dawowar Abba da daddre bayan ta kwashe kayan da suka ci abinci ta dawo xata wuce dakinta ta gansu xaune suna hira dukkan su a falo Jidda tana kusa da ya khaleel dady yana tsokanarsu tana shiga ta wuce toilet tai wanka ta kwanta bacci ya fara surarta daka mata duka taji anyi a firgice ta farka ta xaro ido tana kallansu xahra da Jidda suna karkade karkadan jiki na jin bala'i tashi malama ansamu waje anji sanyin a.c an narke a gado zahra ta fada tana mata yatsinan nan kallo Jidda tace mike ware ido albishirinki ?? Ta cewa Jennifer shiru tayi tarasa ce musu kala sbd mamakin da suka bata ranar juma'a jibi Sa ranata da ya khaleel dai dai da birthday dinshi idan kinsa wani abu aranki game dashi sai ki cire sbd ya khaleel ba mijin karamar mace bane bagidajiya dangin su ojuku makiya Allah taja tsaki zahra ta cigaba da inda Jidda ta tsaya wannan shine warning na karshe tsakaninki dashi ke dama maxan gidanmu gaba daya ki fahimci wani avu mana taya xa'ai me tsarki ya hada iri da kaxanta ? Idan ma a nayi to banda gidanmu ke abubuwa sun hadu sun miki yawa ga tarin datti na kaxantar kafurci sannan ga talauci kina manta matsayinki na Yar aiki ?? Idan bakiyi wasa ba xaki tsinci kanki agaban iyayenki dan wllh sai mun hada miki bala'in da xaisa kibar gidan tai tsaki Anty Jidda muje suka fice ta bisu ta kallo hawaye na sauko mata baccin da batayi shiba kenan takwna tana juye juye

*****************
Chapter 19 · 0% Book details