← Book details Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 85

Sashe 72

Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

musamman mata wllh duk abinda kikayi sai ammiki kada ki raina matar wanki sbd kina k'anwar mijinta kema naki k'annan mijin suna jiranki kada ki kuskura kiyi balle aimiki ki xauna lfy da ita dan matsayin yayarki take idan kuwa ba haka ba xakiyi dana sani lokacin da komai ya cab'e miki sbd hak'k'in matar wanki baxai barki ba sai Allah yasaka mata.

Rowa:

masifa ! bala'i !

rowa itake haddasa muguwar k'iyayya awajan abokan mu'amalarki idan kina da rowa baki da sauran k'ima ko mutunci balle kwarjini awajan mutane asalima kowa haushinki xai d'ink'ayi ki xama saniyar bare acikin alummah.

kin manta babbar illar rowa ? itafa kyauta yalwace idan kika kasance mai kyautatawa to baxaki tab'a xama cikin rashi ba domin ita kyauta tana bud'e k'ofofin arxik'i rowa kuma tana toshesu ne

kin b'oye kin hana kowa kin ji dad'i

baki san kanki ki kaiwa illah ba kin toshewa kanki da kanki k'ofar wani arxik'in daya tunkaroki.

sai kiji mace ta tak'ark'are tana fad'awa kowa dangin mijinta basa sonta ki ganta abar tausayi kina yin bincike xaki ga babbar marowaciya ce. tana yiwa dangin mijinta rowa .

tayaya xa su soki ? ko ba su bama wllh mak'otanki ma baxasu soki bah sannan bake ba rahamar Allah sbd hadisine ingantacce mai rowa baxai shiga aljannah ba !

subhanallah ga babbar illar toshe k'ofofin arxik'in ga rashin samun rahamar ubangiji uwa uba ga k'iyayyar kowa ina xaki sa kanki ?

tayaya xakiyi rayuwa mai dad'i Allah baya tare dake? tayaya xakiyi rayuwa mai dad'i kowa najin haushinki ?

bari na tuna muku wani abu dan nasan duk kunsani tuni ne kawai nawa.

rowa tana farawa tun yaro yana shekara 2

yes hakane da kin fuskanci d'anki marowacine ki cire soyayya ki rabashi da ita misali:

kin bashi biscuits sai kikace "sanwa y'an uwanka" ya d'age miki kafad'a baxai baxasu ba ko kikace "sanwa abokananka" yak'i cire soyayya agabansu ki kwace biscuits d'in kiraba biyu ki bawa abokanan nashi idan ke ka d'aice

dan kiraba shi da wannan masifar ta rowa kice ya sammiki in ya k'i ki kwace

da kin kwace xai fasa kuka sosai kina jin sautin

i hun kukan har cikin kwakwalwarki ki daure ki cije ki shanye wannan soyayyar ki taimakeshi ki cire masa wannan mugun ciwon na rowa idan yai xuciya ya wullar da biscuits d'in sbd kin d'iba d'auki ki k'ara rabawa xai xo da gudinsa ya amsa yana kuka ki kyaleshi kada ki rarashesa ki barsa yayi ya gaji ki daure plx ki taimaki kanki ki taimaki al'umma dankece malamar y'ay'anki na farko aduniya washegari ma ki maimaita hakan kice ya y'an miki in ya hana ki kwace ki raba biyu ki d'au rabi

idan yai kukan ki cije kiyi masa haka sau hud'u ko sau uku ajere

wallahi baxakiyi sau shida ba kafin kice y'an min da kanshi xai raba yanda yaga kinyi ya baki koya bawa abokansa ko y'an'uwansa ko ya baki da kansa kafin ma kice ya yanmiki xai ce umma gashi.

Alhmdllh kinga shikenan kin taimaki kanki kin taimaki y'an'uwansa duk abinda ya samu baxai banbanta kansa da su ba

xai xama mutum mai taimako da rashin kyashi musamman ma mace sbd marowaciyar mace bala'i ce sbd har y'ay'anta sai ta koya musu

iyaye adaure araba y'ay'a da rowa tun suna yara anuna musu kyauta dole ce dan idan kika kwace wannan abun xasu tabbar da kyauta taxama dole

ayi hkr acire soyayyar nan ta d'an wannan lokacin idan inkikayi haka kin taimaki kowa ta dalilin alherinsa sai kiga kema kin samu rahama

idan kika fuskanci d'anki ko y'arki tana da son kanta bata so kowa ya tab'a abinta ko tana zaluntar y'an'uwanta had'a musu kwanan abinci d'aya kada ki raba wajen kwanciyar su ma ki had'a musu in dai jinsin su d'aya suturarsu ma ki had'a kisawa wannan ta wannan tun suna jin haushi akwana atashi xasu daina jin haushin hakan kin had'a kan y'ay'anki baxa su tab'a jiwa kansu kyashin sadaukar da komai nasu akan junansu soyayya da shak'uwa xata k'ullu tsakaninsu da wuya kiga suna wannan fad'an nasakonni xasu xama abin sha'awah agun kowa amma fa sai an daure

agurguje agurje bari mu tab'a y'anmata:

mutattauna abinda ke damunsu yawancin y'anmata 98% an tab'a yaudararsu kusan kowacce budurwa tana da ciwon k'irji sbd damuwar soyayya sai saurayi ya yaudaremu daga baya kuma mu komawa Allah bayan tun ada yakamata musan da Allah ba sai mun fad'a cikin halin ha'ula'i

shawarar da xan bamu idan har kina son ki kare kanki daga yaudarar saurayi lokacin da kikayi sabon saurayi kika ganshi da irin qualities d'in da kikeso had'uwar ku ta farko kada kiyi sanya sallolinki na wannan ranar kiyi addu'ar ya Allah wane sabon saurayin danayi idan alkairine aratuwata Allah katabbatar da alkairin idan kuma ba alkairi bane shi ya Allah kahad'ani da wanda yake mafi alkairi

had'uwarku ta uku ki tabbata kinyi addu'ar istikhara akansa cikin sauk'i idan shi ba alkairi bane Allah xai rabaku batare da ciwon xuciya ko b'acin rai haka kawai xakiga kun rabu kirasa dalili kiji ya fice miki arai duk kuwa da had'uwarsa kinga kinsa Allah alamarinki Allah kuma ya taimakeki

idan kuma alkairinr sai kiga kin aureshi

tayaya xakiyi addu'a akan wani sha'ani nada ban?

yanxu yanxun nan kikai sallar nafila kika dad'e kina addu'a bayan kin idar kika kunna music indian music ko na hausa kinayi kina gyad'a kai kina jin dad'i tayaya Allah xai kalleki alhali kin had'a rayuwarki da shagala?

addu'a fa kika gama kuma kin koma sauraron wak'a keda kanki kinsan bai dace ba. kiyi tawassali da sunan Allah ki kiyi imanin ubangiji xai amsa miki addu'ar ki ubangiji Allah ya bamu maxaje nagari

kada ki cika babban buri wajan xab'an wanda xaki aura ko bashi da arxik'i in dai yana da abinda xai ciyar dake kin yadda da addininsa da kyakkyawan mu'amalarsa ki auresa kawai akwai ingantaccen hadisin dayace wa iyaye

ku aurar da y'ay'anku koda maxajen basu dashi Allah xai axurtaku dan shine mai axurtawa.

ta dalilin wannan auren sai kiga Allah ya baku arxik'i na ban mmk.

saudaya wa xakiga kin kwashe shekaru kina soyayya da saurayin ki lokaci 1 kiji ance ya auri wata abinda xai baki mmk shine my b wacce ya aura kinfita komai ya barki ya aure ta.

kin san babban kuskurenki rashin taka tsantsan shifa namiji inyana sonki duk dad'ewarku wllh ki d'ink'a kaffa kaffa sbd yana lura da komai naki yana sa miki ido ba ke kad'ai ba har tarbiyyarku idan kika fiya ashar kina ganin kun xama d'aya babu abinda xaki b'oye masa duk yadda yake sonki xai iya rabuwa dake sbd tunaninsa bawai asoyayyarku ba a'ah akan tarbiyyan yaranki

baxai so ki d'ink'a xagin y'ay'anku ba ko wataran ma shi da kanshi xaki xaga haka inyaga gidanku ba tarbiyya duk yanda yake sonki ya gwammace ya hkr

dai dai da yanayin maganganunki ma in basuyi masa ba kyaleki xaiyi ko yana sonki yaya kike?

mai saurin fushi ce ? ko masifaffiya ce kina da raina mutum ? ko mai hkr ce

ko kuma a'ah ballagaxa ce baki da aji ko kad'an ko kuma gidanku ba tarbiyya k'annanki k'anana sun rainaki dan haka baku da tarbiyya

daya fuskanci abu mara kyau shikenan sai kiga yayi baya baya dake kirasa dalili wani ma baxaiyi bayan dake ba sai dai kwatsam kiji ance yayi aure

kice ya yaudareki alhali shi kuma akwai wata illa da ya hango duk k'ank'antar ta

ta dalilinta ya rabu dake da xaki samu wanda yake amininsa ki ce ya fad'a miki akan meyasa bai aureki ba idan har amininnasa yana jin tausayinki xai ce wai dan abu kaxa da kaxa ke aganinki ba babban abu bane idan har yana sonki baxai k'iki ba shi kuma tunaninsa wannan k'ank'anin abun watarana xai girmama ya wuce xatonsa misali:

kina hira dashi k'aninki yaxo yace "anty kixo inji mama"

dad'in soyayya ya kwashe ki bakyason abinda xai raba hirar ku dashi kikacewa k'anin naki "ina xuwa"

kawai kika cigaba da hirarki xuwa cen wani lokaci har sai yai miki tuni "mama fa tana kiranki"

kika basar "ai zanje"

my b ma shi xai

taku raki ki je sannan xaki tafi

kin k'i xuwa kiran mama sbd kina sonshi ba kyason abinda xai raba hirarku dashi

shi kuma yana kallonki a mara tarbiyya mamanki na kiranki kin k'i xuwa

ya tabbata bakya girmama iyayenki duk lokacin daya aureki idan kikayi bak'i haka xaita kiranki kina k'in xuwa.

amma da mama ta aiko kije kada kibar yaron yaje yace kina xuwa

ku tafi da yaron batare da kin nemi ixininsa ba kice masa

yi hkr bari naje mama tana kira ku tafi da yaron

xai tabbatar da kinsan darajar iyayenki kina daraja su koda ya aureki baxaki had'a hidimar sa da ta kowa ba.

mu dage da addu'a dare da rana safiya da maraice kixama mai tak'wah da tsoron Allah ki tsarkake harshenki ba ruwanki da yin gulmar wata kiji da kanki

kada burin duniya ya mamaye ruhinki babban burinki ya xamana samun falalar ubangiji babban burinki ya ka sance samun rahamar Allah.

dan me Allah ya haliccemu ? dan mu bauta masa ba don ki cikawa kanki wani buri na cen da ban

na neman duniya koda kina da wasu burikan tunda ba'a rasa mutum da buri manyan burikan ki yaxama shine na Allah samun falalarsa da rahamarsa da cetonsa da ceton annabin mu annabi muhammad sallal lahu alaihi wasallam.

akwai bayanai da yawa abakina ga lokaci na hararar mu dole na katse anan ma had'u agaba insha Allah.

tayi addu'ar rufe taro aka watse jikin kowa asanyaye dan malama

*Maryam Garkuwa*

ta sanyayar musu da jiki matuk'a.

yamma nayi aka fara shirin kai amare da jikinsu yake asanyaye kowacce tana tunanin rabuwa da junansu sbd shak'uwar da sukayi bayan sunyi wanka aka shirya su cikin less mai shegen kyau kowacce aka kaita d'akinta suna rusa uban kuka tamkar baxasu kuma had'uwa waje d'aya ba sai da suka karyawa kowa xuciyarsa mutane da dama xun xubar musu da kwalla sbd tausayin rabuwarsu bayan sun shak'u da juna sosai.
Chapter 72 · 0% Book details