← Book details Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 85

Sashe 53

Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"baiwar Allah nasan ke kika xamewa jikokina uwa keda bawan Allahn cen mijinki bamu da bakin da xamu iya biyanku ko gd muku sai dai kawai muce,Allah ya.... ta fashe da kuka Allah ya biyaku,

sarki ne ya gyar murya,

"dr bashir Allah yai maka Albarka Allah ya raya maka xuri'a Allah ya albarkaci rayuwarka da xuri'arka lallai kayi namijin k'ok'ari na jinjina maka ina son ka kwashe labarin rayuwar yaran nan mai ban ta ujjibi kafad'awa iyayensu,

jikin dady asanyaye dan muryarshi ma sai da tayi mugun laushi sbd tausayi suna kukan yana rayawa aransa ace shine a irin yanda suka samu kansu tabbas xai iya yin fiye da abinda sukayi,

ya fara da gdy ga Allah sannan ya kwashe labarin komai ya fad'a musu,

kamar ya xugasu suka kece da sabon kuka na ban mmk,

sarkine yace,

"ku dakata ! ku dakata kukan ya isa haka Allah xa mu gode masa,

" hjy na nabila ta kalli jannat datake gefe guda tayi ta gumi,

"y'ata xo nan xo kirabu da jikina plx kixo na ji guminku duka a cikin jikina,

jannat tana xubar da hawaye ta girgixa kai tana wa uwar wani kallo wanda ya bawa kowa mmk,

" baxan iya xuwa ba naganku tabbas ku iyayena ne amma har yanxu xuciyata bata dai daita da tunanin yadda muka tsinci kanmu ba,

sulthana da sauri ta fincike jikinta ta matsa kusa da momy hade da sakin wani sabon kuka,

"momy kina jinsu wai sune iyayenmu kalli irin kukan da sukeyi dan muji tausayinsu su sam basu ji namu ba shiyasa suka watsar damu a bola momy ki kalli irin rayuwar da anty hindu tayi ita da Jennifer wai muna da iyaye masu sanmu wllh ban yadda ba tayi dariya wacce tafi kuka ciwo ta kalli jannat " anty jannat kinji fa kin yadda ?

irin dariyar da sulthana tayi irinta jannat tayi

" ina fa zan yadda nifa kallonsu kawai nakeyi, cike da mugun mmk suke kallonsu,

hindu itama xare jikinta tayi tana dariyar wacce tafi kuka ciwo,

" baxan iya yadda ba fa sam shekara nawa ina cikin kunci da masifa lokaci d'aya na yadda da ta tsuniya ta yaya sulthana jannat ?

mik'ewa sulthana tayi cike da tsiwa da rashin kunya,

" ko kunya bakuji ba kuke kiranmu y'ay'anku wanne laifi mukai muku kuka kasa xama tare damu ? idan ma sace mu akayi tayaya kukayi sake har hakan ta faru ? kaina fa bai d'auki wannan ba, khaleel ne yace " sulthana meyasa kike haka ne iyayenki nefa,?

xare ido tayi

" iyaye ? su wa din ? iyaye xasu watsar da y'ay'ansu abola ? kasan yadda mukeji kuwa ta girgixa kai tan xubar da hawaye masu k'una kada kace komai dan bakasan xafin rabuwa da iyaye ba,

kwatsa mata tsawa yayi,

" ya sheki iyaye ba abin wasa bane ba kowacce mgn ake musu ba,

itama tsawar tayi,

"plx ya khaleel ! dan kaga ina tsoranka kada ka shiga wannan maganar kabarni dasu kamanta wahalar da Jennifer da hindu suka sha !! ?

kallonta kawai sarki yayi yai mata alama ta xauna,

a tsorace had'e da kid'ima ta xube a wajan tana kuka mai ban tausayi, tsohuwar nan da sauran matan suka sa kuka tsohuwar ta rarrafo ta rungume sulthana yi shiru jikata bamu da laifi a b'atanku sanadiyyar rasaku sandin xamana kan wannan keken shekarata goma sha takwas ina xaune akanshi sbd bak'in cikin rasaku, waccen ita ce mahaifiyarku, tunda kuka bace take rashin lafiya sai yanxu inaga xata warke,

mahaifinku rabonshi da dariya tunda aka rasaku waccen hajiya murja matar babanku ce tafi shekara tana suma ayanxu haka tana da ciwon xuciya sanadiyyar b'atanku munfiku bakin ciki da damuwa kiyi hkr yanxu kuwa xakiji komai abakin hjy murja matar babanku,

a daddafe hjy murja ta iso kusa dasu ta janyosu jikinta inshaa Allah xakuji lbrn ku mai ban ta ujjibi da mmk idan sarki yai min ixni,

gyran murya sarki yayi,

" nayi miki ixini murja

muryar ta asanyaye ta fara

CHED'E FAMILY

wani babban dangine wanda yayi fice afadin kasar nan harda kusan duniya fulani ne su usul, Alhaji yahaya ched'e shine mahaifin adamu yana da tarin dukiya wacce tasa sunanshi yayi fice a duniya yana da mace d'aya hajiya zainab ched'e wacce take y'ar'uwa awajansa sai d'ansu guda d'aya tal da suka haifa shine Adamu ched'e wanda suka dauki son duniya suka dora masa kasncewar shi kadaine hajiya zainab ita da mijinta suka haifa,

sun so suk'ara samun haihuwa amma Allah baiyi ba musamman hajiya tana son y'a mace arayuwar ta dan ko lokacin da tana da cikin Adam addu'a ta dink'ayi Allah ya bata mace cikin ikon Allah kuma ya bata d'a namiji ya taso cikin gata da soyayya taban mmk kasancewar shi kad'aine duk da gatan daya samu hakan baisa ya xama fand'ararre ba sbd iyayensa tsaye suke a kansu da kuma kulawa ta dangi dan atare suke xaune waje d'aya ched'e estate nan cikin g.r.a basa xama ararrabe sbd kansu a had'e yake komai nasu acikin ched'e estate yake, hakan tasa suke kula da junansu da tarbiyyan y'ay'annsu,

adamu mutun ne mai tausayi da taimako da son y'an'uwa uwa uba mai son addini, dalilin dayasa yai fice cikin dan ginsu kowa na sonshi da nan nan dashi a kullum burinsu su kyautata masa Allah yasa ya kai mun xalin aure nan da nan dangi sukayi caa kowa yana so yabashi y'arsa sanadiyyar hakan rikici ya fara k'ulluwa dan kowa gani yake adamu da y'arsa ta dace tun abin ana yinshi a b'oye har takai takawo ana gaba da jin haushin juna hakan tasa mahaifin shi Alhaji yahaya ched'e ya tara yan'uwanshi dukansu yai musu nasiha sannan yace,

"Adamu ba yaro bane yana da hnkl da ilmin da tunanin da xai zab'awa kansa wacce ta dace dashi yanxu fa ba xamanin da xa'a xab'awa yaya abokan rayuwar su bane ku barsu su xab'awa kansu dukkannin mu nan jini d'ayane xuri'a d'ayace har abada muna tare babu mai rabamu kuyi hkr nabawa d'ana damar ya xab'i duk wadda yaga ta dace dashi kuma kuyi hkr ku bari y'ay'anku su xab'i wayanda suka dace dasu,

haka dai yai musu nasiha suka gamsu jikinsu asanyaye suka watse bayan sunyi addu'a

ranar talata adamu yana b'angarenshi akwance mahifinsa ya shigo dakin ya sameshi akwance idonshi a bud'e cike da kulawa yakalleshi,

" Adamu lafiya kake ?

mik'ewa yayi daga kwancen yana murmushi "Baba lafiya nake,

"toh alhamdulillah ka shirya anjima kad'an xaka rakani fada wajan sarki,

" toh baba,

ya fice yana fita yashiga toilet yai wanka ya sa manyan kaya yayi shiga irin ta mahifinshi wacce yake so fararen kaya abinka ga farin mutun kayan sukai masa kyau sosai bayan ya gama ya je babban falon su ya tadda mahaifinshi da mahifiyarshi suna hira, ta d'ago kai ta kalleshi

" oh dannan,

da ke bata kiran sunanshi,

"ina xakaje haka ?

" kodai xakaje wajan y'ata surukuta ne ?

dariya sukayi shida babansa,

" unguwa xai rakani wannan d'annaki inaga matsoracine yakasa fidda mata,

"baba adai tayami da addu'a

murmushi baban yayi,

" Adam addu'a dolece taxama dole ko bamu haifa ba dole miyiwa y'ay'an dangi dana musulmai Allah yai maka albarka Allah yabaka mace ta gari shida hjy suka amsa da, "amin,

hjy tace "nidai in an fita yau adawo min da lbrn surukata, suka fice suna dariya bayan tayi musu addu'ar Allah ya dawo mata dasu lfy

By

*Ummee Garkuwa*

[5:44PM, 12/18/2016] Fatima Garba:
'<Øûß
'<Øûß
'<ØûßJENNIFER
'<Øûß
'<Øûß
'<Øûß

83&84

basu b'ata lokaci ba suka isa gidan sarki falon shi suka isa na tarar bak'i kasancewar akwai babbar sanayya atsakaninsu cikin girmamawa da biyayya suka gaishe shi ya amsa had'e da sakin fuska,

suna cikin gaisawar sarki yai bak'i dan'uwan shi wanda baya k'asar yaxo shida iyalinsa matarsa da y'ay'ansa hud'u biyu maza biyu mata,

bayan sungama tattauna abinda ya kawosu sukai sallama da sarki da bak'insa suka taho kan hanyar su ta dawowa Adam yakasa daurewa har sai da yaiwa babansa maganar,

" baba kasan wannan wanda ya shigo fadan sarki ?

"a'ah adam ya akayi ?

sosa kansa ya farayi yana murmushi,

"naga babbar y'arsa ne naga kamar tana da hnkl,

dariya baban yayi

"d'an nema kafad'i mgnr ka kai tsaye kasan dai ni ba surukin ka bane,

dariya shima adam din yayi

"baba da gaske nakeyi ina ga tazama surukarku idan zan samu,

cikin murna baban yace,

"Alhmdllh haka akeso inshaa Allah gobe zanje na tambayo lallai ashe dai hajiyanka da gaske take tunda tace fitar yau axo mata da lbrn surukarta gashi xa a je mata dashi ubangiji Allah yasa adace,

cikin xuciyarsa ya amsa da "amin

ba'a d'auki wani dogon lokaci ba suka dai dai ta kansu sai dai an samu matsala daga wajan dangin yahaya ched'e fur suka k'i yarda da auren akan baxaiyiyu ya auro musu bare ba duk tulin danginsu ace babu wacce tai masa, suka dink'a k'aramar mgn suna aibata rashin dacewar abin, ran Alhaji yahaya ya b'aci ya tarasu duka yai musu fad'a had'e da nasiha ya kuma ce babu wanda ya isa ya hana auren Allah ne ya had'ashi, ganin yanda ranshi ya b'aci yasa suka amince dan suna gudun b'acin ranshi suka saki komai akayi auren mai ban mmk,

auren Adam ched'e da amaryarsa Nabila Idris sarki,

amarya ta tare nan cikin ched'e estate tasamu soyayya da gata wajan y'an uwan mijinta yanda suke sonshi haka itama suke nan nan da ita,

kwanci tashi asarar mai rai sai da suka kwashe shekara goma da aure batayi ko b'atan wata ba hakan ya dami dangi sosai akayi ta rokon Allah akan Allah ya bashi haihuwa hajiya Nabila da surukarta Hajiya zainab sunfi kowa damuwa dan kullum atafe suke k'asashe daban daban ana duba hajiyan Nabila duk inda sukaje amsa d'aya ce bata da matsala Allah ne dai bai kawo ba kwatsam Allah ya dauk'i ran Alhaji yahaya ched'e sakamakon y'ar rashin lfy ta sati biyu, mutuwar ta gigita kowa dan kaf arewa babu kamarsa haka danginsa kamar suyi me basu da yadda xasuyi ubangiji ya amshi abinsa haka akai zaman makoki xuciyar kowa akarye akayi aka watse akabar iyalanshi da azabar rashi ba kad'an ba,
Chapter 53 · 0% Book details