← Book details Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 85

Sashe 62

Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sulthana kam b'oye fuskarta tayi jikin hjy murja, momy tace

"oh ni firdausi yaran yanxu ba kunya bare karah zamani kenan"

hajiyarmu tace "zamani fa kam in yaxo sai a zamance ai nan duk iyayensa ne idan yaji kunyar mu suwa xai fad'awa damuwar sa ? girgixa kai momy tayi,

dady yace,

"ina zan manta da mgnr aurenka da sulthana ? bayan nasan aranar ne ustaz khaleel xai cashe da rawa?

dariya sukayi suna kallonshi cike da rashin fahimta,

dady ya cigaba da mgn,

"in dai sulthana tana sonka haisam zanfi kowa farin ciki"

ware ido haisam yayi,

"dady kasanfa tana sona"

hajiyarmu tace,

"haba haisam meye na tsorata ?idan batayi ni inayi dan kyakkyawa kamarka ah ina so,

suna dariya hjy murja tace,

"ah'ah kin masa tsufa hajiyarmu shi sulthana yakeso itama tana sonshi"

Abbu ne yai mgn

"toh in dai hakane nasa ranar su ranar tarewar khaleel ayi gaba d'aya "

dad'ine sosai ya kama haisam itakam sulthana sai k'unshe fuska take ajikin hjy murja ammy tace,

" ikon Allah yau Allah ya nunamin ranar da sulthana take jin kunyar had'a ido dani"

yusuf ya xaro ido

"wai basabamba yaya mukarram ka manta? kace anty sulthana baxa ta rigaka aure ba gashi ita xatayi ta barka"

ajiyar xuciya mukarram yayi

"kada kadamu yusuf kajira nan da sati biyun ka gani ina nan akan mgn ta banjan ye ba"

Abbu yace,

"kai dai mukarram akwai kishi"

ammy tace

"yak'ara ta cen da kishin sa ita dai nan da 2 weeks shi kuma ko budurwar ma bashi da ita "

cike da birgewa suke kallonsu,

hajiya Nabila tace,

"kada amatsawa d'ana xai baku mmk ko mukarram?

"yawwa ummey barina dawo kusa dake na samu mai tare min kullum sulthana suke tarewa yau nima ga ummina nan ta shigar min"

suna dariya suna tsokanar junansu, nan dai suka tsaida mgn har bikin haisam da sulthana nan da 2 weeks masu xuwa

[3:06PM, 12/25/2016] Fatima Garba:
'<Øûß
'<Øûß
'<ØûßJENNIFER
'<Øûß
'<Øûß
'<Øûß

97&98

*Ummee Garkuwa*

kafin su tashi daga falon Abba yace,

"inshaa Allah nan da kwana biyar zamuje spine nida khaleel xai min rakiya ina dawowa xamu fara shirye shiryen bikinsu amma kafin nan sai ya fara xuwa abuja wajan president akwai taron da xai wakilceni ina son kuma su tattauna da wani bak'o da xanyi acen"

dukansu su kai addu'ar Allah ya dawo da shi lafiya,

kafin wani lokaci sun shak'u da junansu sbd xaman waje d'aya musamman Alhaji Adam ya maida y'ay'an dady dana Abbu harda na papa tamkar nashi duk abinda xaiyi sai yai shawara da dady kasancewar gidan babban gida ne duk yamma suna xama a gerden wanda wajan yake tamkar falo grass ne tsararru sukayi k'awanya awajan cen gefe fulowowi ne masu shegen kyau kala kala ga kukan tsuntsaye way'anda suke a wajan suka taimaka wajan k'awat gerden d'in duk yamma suna zama dukansu suyi hira suku ma tattauna abinda ya dace wajan matan ya nesanta da wajan da mazan suke zama abin gwanin ban sha'awah sai wanda ya gani

Saturday

tun da wuri ya khaleel ya shirya xuwa abuja taron da xai wakilci Abba sam xuciyar shi ba dad'i sbd baya son barin jannat bashi da yadda xaiyi ranshi ab'ace yake,

tana xaune a d'aki tayi jugum tana tunanin tafiyar da ya khaleel xaiyi a yau tausayinsa takeji ita kanta tana jin ba dad'i bata da yadda xatayi hjy murja ce ta shigo ganin tayi jigum yasa ta ware ido cike da mmk take kallonta,

"jannat baki shirya bane tun d'axu ?

da mmk take kallon hjy murja ta girgixa kai,

"to tashi maza ki shirya kina nufin shi kad'ai xai tafi ne ? tashi ki shirya ku tafi"

ajiyar xuciya tayi wani mugun dad'i ya xiyarceta ta nok'e kanta ak'asa kunya ta hanata tashi,

ganin bata da niyyar tashi yasa hjy murja tak'ara sa wajan kayanta ta janyo k'aramar akwati ta d'ebi kayanta ta xuba ta naimi duk wasu abubuwa da ake buk'ata ta xuba ta waiwayo tana kallonta,

"tun kafin rai na ya b'aci tashi ki shirya"

ganin ba wasa a fuskarta yasa ta mik'e ta canza kaya tunda bata dad'e da fitowa daga wanka ba batayi makeup ba mai kawai ta shafa da powder rik'o hannunta hjy murja tayi suka fito daga d'akin a babban falo suka tadda mutanen gidan cike da rashin fahimta suke kallon hjy murja da jannat da kanta ya ke a k'asa,

Abba ya kallesu yayi murmushi yasan murja akwai kula da yaran nan musamman akan abinda suke so,

hajiyarmu ce tace

"toh ina xuwa haka jannat ?da sauri hjy murja tace,

"hajiyarmu xasu tafi abuja ne ita da mijinta"

"oh hakane fa ubangiji Allah ya kiyaye hanya"

momy da dady murmushi sukayi suna jinjina kirki da kula irin na hjy murja hjy Nabila ma murmushin tayi tana jin dad'in kulawar murja akanta da y'ay'anta shiyasa take kara tunda tasan duk wata kulawa suna samu daga wajanta

waje suka fito tare da mutanen gida suka tsaya dai dai wajan da motar da xata kaisu airport

ranshi a b'ace ya fito daga b'angarensa hangosu yayi tsaye bakin motar daxata kaishi airport ya k'araso had'e da k'irk'iro yak'en dole Abba yace,

"yauwa khaleel ka fito ?

"eh Abba na shirya"

"ok toh ga security nan xasu bika sbd su baku tsaro yanda na fad'a maka dai haka xakayi ubangji Allah ya karemin ku ya dawo da ku lfy"

duka mutanen wajan suka amsa da "amin"

ya shiga mota idonshi akanta yana tuna adadin missing d'inta da xaiyi bai gama rufe k'ofa ba yaga hjy murja ta bud'e mata k'ofar motar ta shigo ciki a kunyace,

murmushi ya kufce masa tuni ya nemi b'acin ransa ya rasa da murna ya kalleta sam ya manta iyayensu na gefe suna kallonsu,

"beautyna zaki min rakiya ko ?

kyafta masa ido tayi, ina murna ta hanashi kula,

"Alhmdllh naji dad'i sosai da wannan rakiya" dai dai lokacin da driver yaja motar su hjy suna musu addu'ar Allah ya tsare,

suna fita daga gidan ya janyota jikinsa yana kallonta itama kallonshi take da murmushi a fuskarta

"harna fara tunanin halin da zan kasance na rashinki kusa dani"

far tayi da ido,

"ni kaina na shiga wani yanayi na rashinka da zanyi"

"wow!"

ya rungomata sosai yana murmushi mai sauti,

da sauri ta kufce jikinta had'e da xare ido kallonta yayi da rashin fahimta da ido ta nuna masa bafa suka d'ai bane a motar tab'e baki yayi ya janyo ta jikinshi a kunnanta ya rad'a mata,

"ina ruwa na dashi babu wanda xai hanani shak'ar k'amshin matata mai dad'i"

marairaicewa tayi shafa lip dinta yayi ya girgixama mata kai

"kiyi hkr baxan iya xama kusa dake ban jiki ajikina ba"

ta kalleshi ya kashe mata ido d'aya

a haka sukaje airport basu b'ata lokaci ba suka hau jirgi yana rungume da ita har suka isa Abuja tare da security d'in da aka had'asu kai tsaye gidan Abba na cen suka tafi dan anan yace su xauna shi kanshi gidan xagaye yake da security jinjina kai khaleel yayi yana tausayin Abba gaba d'ayan shi arikice yake axxaluman mutanen nan sun rikita shi bashi da kwanciyar hnkl ko kad'an

suna shiga cikin gidan alwala suka d'auro sukayi sallar la'asar suna idarwa ya mik'e yana kallonta,

"taso muje muyi wanka"

kwab'e fuska tayi kamar xatayi kuka

"kaje kafara yi in ka fito ni sai nayi"

zaro ido yayi yana kallonta,

"tashi muje"

nuk'u nuk'u ta tsaya yi da kanshi ya mik'ar da ita yana k'ok'arin cire mata kaya rik'e hannunshi tayi tana dariyar dole

"tsaya tsaya ya khaleel bari na cire da kaina"

sakin ta yayi yana dariya ta cire kayan tsab ta d'aura towel suka shiga toilet kallonshi ta tsaya yi tana tunanin cire towel d'in ganin haka yasa ya janyo hand shower ya jik'ata da shi tana dariya da kanshi towel d'in ya sub'uce ya fad'o kamar wasu yara haka su ka d'inka wasa da hand shower d'in daga hannun wannan xuwa hannun wannan sun dad'e suna wasan ruwan sannan sukayi wanka shi kanshi wankan haka suka d'inka facin facin da kumfa sun b'ata lokaci mai yawan gaske sannan suka fito kowanne jikinsa d'aure da towel yana rungume da ita suka k'araso wajan mirror ya janyo wani towel d'in na daban ya tsane mata ruwan jikinta sannan ya mik'a mata ta tsane na jikinsa suka shafa mai suna tsokanan junansa da man shafawar,

bayan sun gama shafa man ya kalleta,

" kwalliya xan miki da kaina"

ware ido tayi had'e da dariya tana kallonshi,

ya d'auko powder ya shafa mata tana kallon mudubi tana mmk ya d'auko lip stick ya shafa mata a leb'e xata gyra ya tsayar da hannunta,

"no ! ban yadda ba ni zan gyra komai na hutar da ke "

haka ya bar fuskar yana kallonta ta jikin mudubi silent makeup yai mata kyau sosai ta tashi tsaye,

"gsky ya khaleel ka iya makeup zan bud'e maka waje na musamman ka dink'a yiwa amare mskeup dan kaxama babbn arties"

dariya yayi shima yana kallon bayanta da ta juya tana tafiya wajan inda kayansu yake,

"matata kawai na iya yiwa banda ita baxan iya a fuskar kowa ba"

ta d'auko musu kaya su ka shirya,

"zan tafi meeting da bak'on Abba inaga baxan wuce 2 hours to 3 ba"

ya rik'o hannunta suka isa k'ofa ya janyota jikinsa suna kallon juna ya shafa lip dinta da yake so

"kinyi kyau da wannan kwalliyar"

itama lip d'inshi ta shafa tace,

"kayi kyau da wannan shigar"

dariya yayi,

"duk abinda nai miki sai kin min ko?

itama dariya tayi had'e da yin far da manyan idanuwanta daya k'ara mata kyau,

"kai ka koyamin"

tafad'a idonsu cikin idon juna,

shafa cikinta yayi yana kallonta yana dariya k'asa k'asa,

sunkuyar da kanta tayi had'e da jin kunya ,

dariya ta bashi sosai,

"ki rama mana"

girgixa kai tayi kanta ak'asa,

birgesa tayi ya kalli kanta data sunkuyar dashi,

yasa hannu ya d'ago fuskarta da sauri ta rufe idonta

fuskarta d'auke da murmushi,

har yanxu hannunshi d'aya na cikinta yana shafawa,

"bud'e idonki beautyna"

a hnkl ta bud'e idon suka kalli juna da sauri ta rufe harda sa hannu,

"d'ago kanki plx"

ya fad'a muryar shi asanyaye,
Chapter 62 · 0% Book details