← Book details Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 85

Sashe 32

Jennifer Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Itama Momy abinda take sakawa kenan aranta da tana da yadda xatayi da tayi dan ganin yaran nan sun hadu da iyayensu tunda taji lbrnsu kullum sai tai musu kuka tana matukar tausaya musu sbd halin da suke ciki tana jinsu tamkar yayenta na cikinta

*******************

Da daddare dady ya sameta a daki tayi xugum tarasa me ke damunta, Jennifer ! Ya kira sunanta ta dago kai ta kalleshi da sauri ta sunkuya ta gaishe shi cikin girmamawa,

Ya amsa da tausayinta fal aranshi,

Kina da Wanda kikeso acikin masu sonki ?

Cikin matukar karfin hali ta masa da ah ah dady, kallonta yayi naya naxarin ta,

babu Wanda kikeso?

Eh dady, bavaka xabi ka xabi duk Wanda yai maka in dai ka yadda da ingancin addininsa,

Gyada kai yayi Allah yai miki albarka Jennifer,

Ta amsa da amin yace jibi juma'a nake so da an idar da sallar juma'ar a daur auren ubangiji Allah yasa albarka a rayuwar aurenku,

Ta kyar ta iya amsawa da amin,

Ya fice yana jin dadin biyayyar yarinyar yana kuma tausaya wa halin da suke ciki,

Tunda ya fita ta fashe da kuka shikenan yanxu tarasa ya khaleel dinta ? Tarasa farincikinta tarasa Wanda take matukar so ? Baxata iya fadawa dady shi take so ba baxata iya ba ! Cikin kuka take maganganunta,

Rayuwa tana xuwar min abaibai abinda nake tunanin yiyuwarsa baya yiyuwa yaushe zan fara rayuwar farin ciki ? Yaushe burina xai fara cika ? Yaushe xan fara son abu na samu ? Meyasa duk abinda nakeso ban fiya samuba ? Kuka take sosai tana sambatu

***************

Washegari ranar alhamis gaba daya ranta acunkushe take jinshi tana xaune adaki sulthana ta shigo,

Amarya bakya laifi ko kin kashe dan masu gida, kallonta kawai jenny tayi hinduma ta shigo dakin,

Gobe muna da shagali a gidan nan,

Bata rai jenny tayi,

Hindu tace wai plx jenny waye mijin naki nifa ban San Wanda xaki aura ba,

Hawaye ya saukowa jenny tace nabawa dady xabi nasan baxai xabamin mutumin banxa ba,

Da sauri hindu tace dama abaki wannan dan xafin kan dan kun dace da shi,

Wani irin kallo jenny tai mata hade da sauke numfashi tasan ba xa ataba bata shiba hawaye ya sauko mata shine burinta shi takeso amma ina yai mata nisa,

Sulthana tace wannan dan xafin kan yanda ya keji da kansa tunaninshi xai iya bashi ya wuce da ajinta dan dai kawai jenny mai Kyau ce, karar bude kofa sukaji kan jenny akasa tana tunanin wanne irin miji xa a bata ?,wa xa'a aura mata ? Muryarshi taji kubani waje xanyi mgn da ita ! Da sauri ta dago kai ta akalleshi fuskarshi a daure

Mikewa sukai har xasu fita sulthana ta kalleshi

Plx xan baka shawara, kallonta yayi

Da sauri tace shikenan ma ba komai, ta fice

Murmushi Jennifer tayi tace lallai sulthana rijiya ba wajan wasan makaho bane,

Ya jima yana kallonta baiyi magana ba kanta akasa jikinta na karkarwa jira kawai take taji da me yaxo,

Muryarshi a sanyaye yace Jennifer! Naam ta amsa, tana sauraronsa,

Kin fadawa dady xabinki ? Wanda kikeso ?

Ah ah ni babu wanda nakeso nabashi xabin ya xabamin wanda yaga yadace dani,

Kwaba yayi cikin facin rai haka kikeso ?

Meyasa kikeson cutar kanki ? Kin gwanmace ki auri wani da soyayyar wani ?

Mikewa tayi a dake dan tafara gajiya da titsiyen daya ke mata, ta kalleshi idonta cikin nashi,

Nifa ya khaleeel ba wanda nakeso

Karya kike ! Ya katseta kina dashi ya xuba mata ido wani abu yaji ya na bin jikinsa,

Ya matso gab da ita numfashinsu na karo kowanne najin fitar na kowa, gabanta ya fadi da karfi ta sunkuyar da kanta yasa hannu ya dao fuskar suka kalli juna,

Muryar shi adashe kin San xuciyarki kinsan abinda takeso kada ki kuntata kanki har yanxu kina da lokaci kije ki fadwa dady kina da xabin ki shiru tayi dan tarasa me xatace,

Kura mata ido yayi yana kallon lip dinta ya runtse ido bayason rasata bayason rasa komai nata bai son rasa dan karamin lip dinta me matukar taushi da xaki, gabanta na faduwa tarasa yadda xatai ya tsura mata kyawawan idanuwansa a hnkl ya sauke faskarta daga hannunshi ya matsa nesa da ita kada ki kuntatawa rayuwarki ki faranta mata da samun wanda kikeso sbd shine nutsuwarki ya fice daga dakin

By

*Ummee Garkuwa*

[7:22PM, 12/5/2016] Fatima Garba:
'<Øûß
'<Øûß
'<ØûßJENNIFER
'<Øûß
'<Øûß
'<Øûß

53&54

Bin bayanshi tayi da kallo tana mmkin wannan hali nasa jagwab ta xauna a kan gadonta hawaye ya sauko mata a hnkl ta furta ina sonka Mr coffee amma baxaka tabajin haka daga bakina ba, ita yanxu ya daina bata mmk dan tarasa inda yasa gaba, sulthana ce ta shigo tana mita,

Shi wannan dan xafin kan sai yaita cika yana batsewa kawai dan yasan shi me Kyau ne wai plx jenny anya kuwa yana dariya ? Afusace tace bansani ba !

Ta harareta karkisani,

Hindu ce ta shigo tana waya bayan ta kashe ta kallesu ta ya b'una buska yaushe xamu koma gida ?

Jenny ta kalleta da mmk wanne gida ?

Gidanmu mana hotoro,

Sulthana tace gidanki dai tunda kin saba xaman kanki baxaki iya xama a karkashin wasu ba babu inda xani,

Hindu tayi murmushin yake ta girgixa kai, idonta ya ciko da kwalla, sulthana meyasa kike son yimin gorin abinda bada son raina nake aikata shi ba ?

Harararta sulthana tayi sai ki fadamin Wanda yakeyi da son ransa?

Karya akayi ? Baza man kanki kike ba ?

A kufule tace mata kinsan ma'anar xaman kai kuwa ?

Murguda baki tayi wannan kuma ke ta shafa,

Zaman kai fa shine kamar karuwa,

Tabe baki sulthana tayi kina da banbanci da sune ?

Kafin ta kai karshe hindu ta wanka mata mari hade da nuna ta da hannu,

Baki da kunya Sam niba karuwa bace ! Kina kallona ne bakisan wacece ni ba xama tayi tana goge kwallar da take xubo mata,

Sulthana tana rike da kuncinta ranta abace kukan da hindun takeyine ya Sa taji tausayinta tai shiru tana danasanin goranta mata, bata da yadda xatayi da jin kiyayyarsu lokaci xuwa lokaci babban burinta shine kawai suyita fada da yan'uwanta, hawaye ya xubo mata tana son taga Allah ya yaye musu wannan fitinar,

Jenny juya musu baya tayi ita kadai tasan me ke damunta komai ya cakube mata,

Hindu ta riko hannun sulthana ta riko na jenny,

Asanyaye tace wllh wllh banta ba xina ba sbd nasamu kyakkyawar rayuwa daga gun marikina,

Tun ina yarinya yake fadamin shi ba mahifina bane kuma duk lokacin dana girma xai kaini na dau fansan abinda akai min yafada min kwana na arba'in a duniya aka bashi ni akan cewa kada ya kuskura yace shi ba mahaifina bane,

Idan kuwa ba haka ba to kashe shi xasuyi,

Marikina ya koya min fada ne dan kare kaina sbd abokan gabanshi gani suke ni yarshi ce koda nake fashi ko damfara bantaba kisa ba !

Da tausayawa suka kalleta,

Zan fara kisane akan Wanda ya jefa rayuwar mu cikin masifa,

Jikin sulthana asanyaye ta taba kafadar hindu kiyi hkr Anty hindu duk abinda kika ga inayi ba ason raina nakeyin shi ba,

Ni kaina ina son naga mun xauna lfy,

Babban burina shine naji waye yai mana yankan kauna ya hanamu jin dadin duniya ya rabamu da iyayenmu ? Kan wani dalili ?

Jenny ta budi baki da kyar tace ni kaina ina son jin yadda akayi aka rabamu da iyayenmu me muka aikatawa mutum muna kwana arba'in a duniya, plx hindu ya xa'ayi muga marikinki a kurkuku?

Zaro ido Hindu tayi sosai Jenny ? Xamu Sa kanmu a bala'in daya fi wannan, tabbas shi kadai yasan suwaye iyayena amma yana daure babu Wanda ya isa yaje nemansa, duk Wanda yaje shima sai anbin cikeshi sannan hukuma xatayi xargin duk aikinsu daya, addua kawai xamuyi,

Ajiyar xuciya dukansu sukayi, suna yiwa juna jimamin halin da suke ciki

*************

Yana Barin dakinta ya nufo bangarensa ya xauna ya dage kansa idonsa arufe cikin wani yanayi itace last hop dinshi kuma taki amincewa da bukarsa me yasa xatai masa haka alhali yasan tana sonshi ? Why ? Ita ma tasan yana sonta why take son wahalar dashi ? Oh ya rabbi ! Yarasa ya xaiyi da wannan masifar da ta tunkaro shi baitaba tunanin haka ba Sam ! Baiyi tunanin haka xata faru da gaggawa ba ya xaiyi ?, mecece mafuta ? Meyasa dady xai furta mahboob xai bawa jenny akan me bayan dashi ta dace

Anya kuwa xai iya ganin wannan masifar ? Ya kalli agogo 4:00 na yamma ya hurxar da huci ranshi na suya cikin yanayi Mara fisaltuwa yake furta ina sonki so me tsanani rashinki yanxu xai iya tarwatsa rayuwata ban San soyayarki tai min yawa haka ba sai da naga da gaske zan rasaki ! Allah shiyake tsarawa bawansa rayuwa ba bawa ne yake tsarata ba ! Baiyi tunanin xai so yarinya kaarama kamarta ba yau gashi cikin soyayyrata dumu dumi sannan kuma xai rasata rasawa ta har abada dady ne ya shigo dakin, da kyar ya khaleel ya tashi,

Dady ya kare masa kallo, sannan ya xauna khaleel ya kira sunanshi,

naam dady,

Meyasa meka kwana 2 ? Shiru yayi dan bashi da amsar bashi,

Girgixa kai dady yayi ya xuciyar taka bata fito ba ?

Da mmk ya kalli dady sai kuma ya jinginar da kansa jikin kujera,

Kafadamin khaleel me ya ke damunka ?

Sauke numfashi yayi dady bakomai,

Da ge kafada dady yayi in tayi wari naji koma menene?

Ga kayanku cen haisam ya karbosu daga wajan dinki set 20 20 ne akwai kuma wasu na daban xuwa anjima telan xai kawusu gobe nakeso mu sakasu, ya mike xai fice sai kuma ya tsaya,

Khaleel bani numb din sageer,

Ya juya kai ya lalubo wayar yakaranto masa numb din ya amsa ya fice,

Wani irin bacin rai ya tasowa khaleel shi kam barin gidan xaiyi gobe dan baxai iya jure yanayin daxai shigaba baya son rasa ta kuma gashi xai rasata,

Haushin kansa ya kamasa meyesa shi bai ce yana sonta ba ?
Chapter 32 · 0% Book details