← Book details Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 62

Sashe 9

Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikeda karfin hali da bushewar zuciya tad'ago kanta,
Ga mamakin ta
saitaga yatsareta da idanunsa wacce
suka kankace suka Kuma sauya kala,da wannan alamar kawai take iya fahimtar yanayin sa idan yana hannu,
"Jiya bakiga miscall
Ina bane".
Yy tanbayar yyn da ida nunsa yake kafe a kanta,
Numfashi tasauke a kasan zuciyar ta
Dan tafahim ci halin da yake ciki Kuma ta tabbata da
shi yakwana,
ta ce "nagani mana".
Ya ce "to meyasa Baki d'agaba Kuma Baki zoba".
Yy maganar fuskarsa a murtuke
tace "Nazo nayi maka meye bayan ka auro wacce zata maye
maka gurbina ai zuwana baya da
wani am fani
meyasa baka kirata
taje tabiya maka bukatar nakaba".
Tafaɗi maganar ne cikin karfin hali da tsoron a bin da zaije ya dawo dan kuwa karshe ita zai ɓare mata, dan dai tasan koshi waye duk da kasan cewarsa mabukaci yakan iya danne bukatar sa har idan ba ita ta neme shiba, in zasu shekara bazai taɓa neman taba, wani bin takanyi tunani da zargin taya yake iya jure bukatar nasa ko dai yanada mai biya masane a gefe tayi duk wani iya binciken ta daga karshe dai duk amma ɗaya ce babu.👌🏻 kariyarsa shine AZUMI. takan gane zallar bukatarsa ne ta ƙwayar idanunsa.
Had'e Rai Yakuma yi yajanyota jikinsa
yad'an ja da baya
yazauna saman kujera tare da zaunar da ita a gefen sa yakalleta
da kyau ya ce
"Kinsan me kk fad'a
kuwa? HAMDAH d'ince zan kira? Me kike nufi ma tukun?".
Kawar da kanta tayi gefe har lokacin hannunta dake rike da wukar namakale
a bayan ta dad'a mikashi tayi tabaya
sosai,
ta cusa wukar tasakankanin kujerar dasuke Kai ta ce "tun da har
kariga da ka a mince a ka kakaba maka ita to mekuma yarage,tun
da Wannan ya'iya kasan tuwa to meye
bazai iya faruwa ba".
Takarashe cikeda gatsali tayun kura
tana kokarin mikewa,
yaki Bata da ma tahanyar sauke hannun sa a
kafad'arta ya dad'a suke fuska tare da tsareta da ido Yana d'an kyakykyafta su.
kallonsa tayi idanunsa duk sun kankance murmushi tayi a cikin ranta, tace "Dama an faÉ—a min zaka kawo kanka da kanka".
Wannan ma wata kofa ce na mafita a gareta.
Kawar da kanta tayi tamike tsaye tanafad'in
"Kyaleni inada abin yi".
Mikewa yy tareda riko hannun ta yakuma d'aure fuska cikin nuna Isa
da bada umurni ya ce
"Kafin kiyi wani ai kin sai kinyi nawa tukun Dan haka muje".
D'an zabura tayi ta
ce "wa ni?ai Wannan Kuma babushi ai SALEEM tun da kaje ka auro
wata ka ajeta cikin gidan Nan to babu
Wannan maganar sakanina da kai sai
dai karika kunshe abinka kokuma kaje can kasaukeshi cikin mararta".

Kansa yashafa tareda furzar da iska daga bakinsa ransa ya b'aci datake Dan gantashi da kanwarsa, duk jarabarsa bazaije gun HAMDAH da bukatarsa ba to ta inama zai fara 'yarda a ka haifeta a gaban idon sa, yakuma rasa dalilin da yasa yakasa iya danne abinsa har kuma yake kokarin nuna mata halin da yake cikin. Dogon tsaki yaja tare da
Fizgo hannun ta yanufi cikin bedroom in sa, suna
shiga yasaki hannunta yanuna Mata gado yy Mata
alama da tahau.

Wani kuka tasake
Mai cikeda zunzurutun makirci da tsigar Jan hankali tazube bakin gadon har da
Jan sheshsheka cikin muryar kukan takefad'in
"SALEEM tun yanzu
harkafara nunamin cewa kakaro aure A she kaima kana daga cikin mazaje masu irin Wannan halin?,nasan Dan ka
kuntatamin kanunamin ni ba komai bace zaka kwanta Dani,wlh
SALEEM idan ka cutar Dani dan kana tunanin kana da wata Allah sai
yasakamin".
Wani kukan takuma sakewa Wanda duk
Wanda yaganta saiyaji tabashi tausayi.

Kallonta yatsaya yi
hanikam tadage take rusar kukan,
Tabbas yasan ko wata mace irin haka yakasan ce da ita bazato bb sammani a karo Mata abokiyar Zama dole tagirgiza, musamman Na'ima da yasan halinta da kafurin kishi wasu matan sukan iya b'oye kishinsu a wasu lokutan Na'ima kuwa batadaga cikin irin wad'annan matan.
Sai dai a yanzu yanayinta ya banbanta da na sauran lokutan yanayin ta nayanzun yabashi tausayi,
musamman dayaga kishin gauraye da rauni a tattare da ita.

Asannu yamaso in da take yazauna
kusa da ita Yana fuskan tarta ya ce
"Meyasa kk son tada hankalin Ki a kan Wannan?, HAMDAH fa kanwatace kisa a ranki HAMDAH an kawota gidannan ne
Dan ta tayaki wasu ai'kace-ai'kace nagida,
duk wasu a bin da
yakamata ita zata
Rika miki to meye
wani abun tada hankali".

"tabbas Wannan
damace".
tafad'a a kasan zuciyarta
Ganin yadage da lallamin ta gashi
Kuma a bukace yake sai tarika basarwa tana jam
Masa aji.

Rungumota yy yashiga kokarin samarwa kansa nutsuwa Nan ma
Bata bashi dama ba bukatar ta dai yacigaba da fad'ar
magana maraddad'i a kan HAMDAH a hakadai harya samu yabiya bukatarsa.
Bayan komai yalafa
tana kwance a gefen sa hannunta na d'auren saman kirji sa cikin salon yaudara da kirsa da kisisina tanarke
murya tasoma magana.

"My SALEEM ni a ganina ace yarin yarnan tazauna a gidan Nan kawai Dan d'an wani 'yan ayyukan da bazasu gagareniba kuma ga Rufa'ila ma tananan, inaga hakan zai iya zame Mata takura kawai a maidata gida in yaso tarika kawo Mana ziyara lokaci zuwa lokaci, Kar yazamo mun takura mata".

Janye hannunta yy daga kirjinsa yamike zaune ya ce
"hakan
bazai yuwuba bakuma zanso su Abbu su sami wanna
labarin ba, hakan bazai yuwuba tacigaba da zama a
hakan kawai".
D'an shuru tayi zuciyarta na kuna, "dama nasan za'ayi haka shegen wani son biyayya da wani nuna shi Mai iyaye sai yarika nuna shi yafikowa yiwa iyaye biyayya".
Tayi maganar a cikin zuciyarta.
Tabbas tasan abune
Mai wuya ya amince da Wannan kudurin natan Dan SALEEM mutun ne
Mai matukar Jin maganar iyayensa da yimusu biyayya ko da bayason a bu
har idan suka nuna Amin cewarsu a kan
a bun tofa shima ya Amin ta.
Tab'e Baki tayi a je a
haka wataran wanna biyayyar taka sai ta
durkushe.

Saukowa yy daga saman gadon yashige bathroom Dan sarkake jikin sa.

★★★★

Tun bayan fitar
Aunty Na'ima dana koma saman gado ban tashiba saima
kwanciyar da nayi tunani narikayi ta yadda zanyi nafita a
gidan batare da taganni ba, Dan ni banji kamar zan
cigaba da zama watarana ciwon haukanta Yakuma
tashi takasheni babu Wanda yasaniba, gara
kawai nakoma Dass gun Inna.
Mikewa nayi nazauna tare zuro
kafafuna kasa namike tsaye,
gaban wardrobe na Isa da zummar d'iban kayana natafi
Dass, daga in da nake tsaye ina iya hango tajikin window kasan
cewar glass in windown da labulen duk abud'e suke,
Mai da marfin wardrobe in da
nabud'e nayi narufe natako jikin windown, Ido naware hango Mai
baiwa fulawa ruwa yanata zagayi cikin fulawa nazuba musu ruwa,
Washe Baki nayi,
Nan take namance dawani batun tafiya,
Dasauri nabar jikin windown nanufi kofa nafita waje,
da sassarfa na Isa inda
Mai baiwa fulawa ruwa yake banyi wata-wataba na wafci tiyon hannunsa nad'agashi sama
Ina sallen murna, ruwan Yana dawowa jikina,
Na ce "la Salele
Ashe dama kazo garinnan kana irin ai kin da Baba na lambu yakeyine?, ai daga yau kullum
zan Rika tayaka Yasin."

Da sauri Salele yamika hannu Yana kokarin amsar tiyon, nasauke hannuna
nayi baya dashi
ya ce "Æ´ar gidan Inna bani nacigaba da ai kina tun oga
bai fito".
Ban saurareshiba saima watsawa furannin ruwa Dana
soma cikeda Jin dad'in ganin abin kaunata ruwa.

Salele d'an Dass ne
unguwarmu d'aya dashi, ta hannun Inna yabi harya Sami aiki agidan Ya
SALEEM.

Duk yanda yaso
nabashi tiyon fir naki na ce nidai yabari zan tayashi
ne,haka narika d'aga tiyon sama ruwan nasauka a kaina dakuma cikin fulawan tsalle narika yi cikeda Jin
dad'i, karshe dai hakura yy yatsaya Yana kallon ikon
Allah.

Ya SALEEM ne tafe Yana gyara d'aurin tsadadden agogon
dake d'aure a hannun sa, Ga dukkan alamu sauri
yake Dan yanayin tafiyar da yake yanuna hakan.
Da sauri wani dattijo dake share mota yy hanzarin bud'e Masa marfin motar tareda d'an risinawa tun kafin yakaraso in da motar take.

Da sauri Salele yamasa kusa da ni yamiko hannu Yana kokarin amsar tiyon tare da fad'in

"Yargi dan Inna bani Kinga Oga yafito".

Da sauri najuyo Jin ya am baci Oga, dai-dai lokacin Ya SALEEM yakarasa sauka daga saman step in sashin sa, da zai sadaka da farfajiyar gidan.

Idona nasauke kan fuskarsa bb ko alamar rahama a tattare dashi, mayar da dubana nayi jikina daga sama zuwa kasa gaba d'aya najike.

Rai b'ace Ya SALEEM yanufo in da nake Yana maganar zuci,
"Kaduba shashanci irin na yarin yarnan da wannan tsanyin tafito tana jika jikin ta yanzu idan mura yakama ta Ina ni za'abari da damuwar siyan magani tun da an kakabamin da muwa, yarin ya saikace wata mayya
wannan uban sanyi tafito tana zuba ruwan sanyi ajikin ta!".

A zafafe ya dunfaro in da nake.
b'ari jikina yasomayi Dan nasan yau Kam banida wani mafaka bamu tare da Inna bare tahanashi dukana.
Wayar dake rike a hannun sane yafara tashi da wani sassanyan sauti alamar shigowar Kira, batare da ya tsaida tafiyar da yakeba yad'ago wayar tareda kallon fuskar wayan,
Sunan Abbu ne yabayyana kan screen in wayar,
Cikin hanzari yaja yatsaya.

Ganin ya tsaya Da sauri na wurgar da tiyon najuya a guje nayi ciki.
Chapter 9 · 0% Book details