← Book details Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 62

Sashe 20

Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Menake gani haka HAMDAH yaushe kika dawo Æ´ar wanke-wanke da shara?, tana zaune kina yimata ai ki HAMDAH. daga yau kada nasake gani ko jin cewa kina yimata ai ki, ko tasaki kice bazakiyi ba".
Ido na waro
"Aunty Rafee'at Ya SALEEM fa shi yakece nayi mata".
Da mamaki ace
"Ya SALEEM É—in".
Nace "Ai in ta kirani tace nazo nayi mata shara in naki sai yace nayi".
Shiru taÉ—anyi sai kuma tace
"Ina sai in yana nan ne yakece kiyin ko shine yake kiranki kizo kimatan".
nace
"A'a ita ne".
tace
"To ko takirakin kada kije tun da sai in takirakin kafin yakece kiyin, kuma bari kiji matsayin ki da nata É—aya ne a cikin gidan nan, ke kinma fita matsayi
da iko da gidan nan ke matar sa ce kuma jinin sa,ita kuma aure ne kaÉ—ai
ya haÉ—a su, nan gidan kine ke yakamata kisa wasu ba a sakiba
kikula HAMDAH!".

Ranar wuni Aunty Rafee'at tayi bata bar gidan ba sai dare.

★★�

Bayan ƙwana biyu

Ina zaune a parlour Aunty Na'ima tashigo cikin parlour'n kamar wan da a ka wurgota tana zuwa ta kai hannu ta............

😂🤗 *Wasa farin girki yanzu za a fara wasan*

*Zakujini shiru na ƙwana biyu daga kan gobe Alhamis zuwa ranar Monday saboda bikin da zamuyi daga kan gobe zuwa ranar Lahadi kafin mugama so sai ranar Monday zakujini inai ma kowa fatan alkhairi*👏🏻

*Sai a hankali banyi editing ba*👌🏻

Mommyn Twins ce

*🌺HAMDAH🌺*

*NA*

*RASHEEDA S DIRECTOR*

_(Book one)_

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍�*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*

MARUBUCIYAR👇🏻
*BA ABIN DA BAN GANI BA*
*INA SANE DA HAKA*
*ALFARMA*
*BAZAWARA CE ITA*
AND NOW👇🏻
*HAMDAH*

*Free page*

My no 08034690723

*Sadau karwa gare ki My sisi ƴar'uwa rabin jiki Aunty na na kai na ZAINAB S DIRECTOR*🥰🤗

🅿�11

Tabigi cokalin da naÉ—ibo a binci zan kai bakina,da sauri na mike tsaye naÉ—an ja da baya. cikin masifa tanunani da hannu ta ce
"Ke har kin isa nace kizo kice baza kizo ba. yau ƙwana biyu ina turawa a kira ki kiki zuwa, bayan kin san ai kin kine. tukun na yau zan tura kizo kice wai baza kizoba, ke har kin isa nasa doka cikin gida na, ki ketare?.
Oya wuce kije kiyimin shara ke bari ma jiki har bedroom ina yau sai kin gyare".

She ke-ke nake kallon ta sai kuma nasaki wata Æ´ar karamar dariya ganin yan da take maganar tana wani girgiza wane mai shirin yin rawa.
sai kuma na gimtse dariyar na ce
"Nifa ba Æ´ar ai ki bace, gacan Æ´ar ai kin ki Rufa'ila jeki sata tayi miki dan ni daga yau bazan sake yiba,
Kuma dai gidan nan a iya sanina bai zamo nakiba ban san dalilin da yasa kike son dan gan ta kanki da abin da ba naki ba,
Idan can dakike zaune a cikin sa an am bace sa da naki, tofa ba shi zai sa yazamo nakin ba,
gida na Ya SALEEM ne kuma nasan kinsan meye matsa yin sa a gurina,
Idan can yazamo naki to nan nawane".
Ina kai wa nan najuya da sauri nashige bedroom na Mai da kofa na rufe.

Ina jinta tarika zazzaga buhun a shar da wasu irin muggan kalaimai wan da a karancin shekaru na nagaza iya fassara su.
da fari magan-ganun nata sunata yimin yawo cikin ƙwaƙwalwa daga bisani na watsar da su.

Fuuu tafice cikin parlour'n takoma part É—in ta da bakin ciki da tarin takai ci,
A parlour tarika zarya takasa zaune takasa tsaye, tayi mamakin jin waÉ—annan magan ganun a bakin HAMDAH.

Zuwa can kuma tanimi guri tazau na tana girgiza kafa
Abin da bata taɓa zoto da tunani a rayuwar taba
shine zuwan wata mace cikin gidan SALEEM a matsayin matar sa, amma sai gashi yau har HAMDAH na kokarin dan ganta kanta da wani sashi na gidan a matsayin nata, bayan nan kuma har take faÉ—a mata tasan matsayin sa a gurin shi.
Wannan batu yagirgiza Na'ima ba kaÉ—an ba sai dai a bin da take tunani kan maganar HAMDAH ko kaÉ—an a gunta ita a bun ba haka yake ba,salon maganar HAMDAH ce dai bata fahimtaba, dan ita dan gan takar Æ´an uwan taka take nufi bana aure ba.

Tunani daban-daban suka rika zuwar mata
har tafara tunanin to ko SALEEM yafara saurarar tane bata saniba tana nan ta buÉ—e baki a na can a na cin a manan ta,
Saurin kawar da wannan tunanin tayi tamaye gurbin hakan da tabbacin cewa SALEEM bazai taɓa sau rarar taba sai dai zata daɗa sa ido sosai,
zata kuma ɗau mataki bazata taɓa bari wata mace ta rabi mijin taba,
duk da yau karon farko HAMDAH ta dirar mata da wani a bu a cikin zuciyar ta mai suna fargaba......

Tun daga ranar bata sake turowa a kirani ba, sai dai cikin zullumin gamuwar mu da shi nake dan nasan iyanzu ta sanar masa, nayita zuba ido dan jin kiran uban gayyar wato Ya SALEEM É—in jin shiru sai na sake a bina......
tun daga lokacin harkar karatu na nasa a gaba baji ba gani.

Haka rayuwa taciga ba da tafi, kamar yanda Abbu yayimin alkawari su Fauzan suna samin hutu a ka kawo min su,har sai da hutun su yakare kafin suka koma, duk kuma karshen sati suna zuwa min wato Saturday and Sunday.

Haka dai ƙwanaki suka taja suna juyawa izuwa maƙwanni maƙwanni izuwa watanni.

★★�

*Bayan wata 6*

Zaune suke gaban wani kasurgumin boka sun naɗe kafa sunyi tsit wani masu ɗaukar darasi, sun zuba wa wata faranti da ƙwarya dake gabansa ido.
shiko bokan sai zane-zane yake kan kasan dake cikin farantin idan ya zana sai ya goge yasake zana wani, yayin da hannun sa ɗaya kuma ke rike da wani gashi yana bubbuga ƙwaryar,
Lolaci zuwa lokaci sai ya zaro ido tare da sakin dariya.
Raliya da Na'ima kuwa sai su kalli yuna su girgiza kai sukuma gyara zama, dan sun yar da da ai kin bokan nasu wan da yajima yanayi musu aiki tun da daÉ—ewa.

Wani dariyar ya kecewa da shi yaÉ—a go yana dubansu, cikin wannan kazam tacciyar dariyar da yake ya ce
"An gama komai sai dai a jira lokaci".
Zama Na'ima ta gyara ta ce
"Ban gane ba boka wancan lokacin ma haka kace har yanzu shiru, ni kawai a yi mai yuwuwa in ma kuɗi kake so na kara maka ni bana da matsala da su a ƙwaisu, ni dai kawai na dai na ganin ta cikin gidan".

Raliya ta amshi zancen
"Ƙwarai kuwa boka mu dai a fitar da ita a gidan shine kawai, zamu kara maka kuɗi kasan zuba kuɗi har idan ai ki zaici ba a bune mai wuya a gurin muba".

Wani irin ihu mai haÉ—e da fito bokan yayi kana yace
"Aduk cikin buka tunku da kuke zuwa da shi kufaɗa min wannene bai taɓa ciba!?".
YafaÉ—a cikin karaji da sai da suka razana, kana yanuna Raliya da gashin dabbar da ke hannun sa ya ce
"Ke wani irin kuɗine baƙya karɓa a hannun manyan attajiran garinnan duk ai kin wanene?".
Yakuma faÉ—a cikin muryar nan nasa mara daÉ—in ji da sauraro.

Yakuma nuna Na'ima yace
"Mu mukayi miki ai ki da har kika samu *Parmsec* *ABDALLAH IDRIS ABDALLAH* a matsayin miji kinfi kowa sanin haka".
da sauri ta ce
"A gafarce mu boka basai an yi tone-tone ba zamuje muciga ba da jira sai a bin da kace".

Yakuma kecewa da dariya yakara karkaɗa gashin dabbar da ke hannun nan na sa kan ƙwaryar, kana yaɗa go yana faɗin
"Aljani Durkus ya hatsala kunimi gafarar sa."
yafaɗa yana nuna cikin ƙwaryar wan da sai fidda wani irin bakin hayaki yake,
Da sauri suka sunkuyo da kan su kan ƙwaryar suna faɗin
"A gafarce mu ai mana afuwa".
Shiru yayi kamar mai sauraran wani abu sai kuma yashiga gyaɗa kai yana washe haƙora kana yace
"Aljani Durkus yagafar ta muku kutashi kuje".

Da sauri Na'ima tabuÉ—e jaka taciro kuÉ—i masu yawa ta a je gaban bokan kana suka mike suka nufi in da suka faka motar su,
A cikin motar Raliya da ke jan motar tajuya ta kalli kawar tata da ta jingina da jikin kujera sai taunar baki da girgiza kai take,
ta ce
"Kawata ya dai naga kamar har yanzu hankalin ki bai ƙwanta ba?".
Da sauri Na'ima kamar mai zaman jiran tambayar ta ce.
"Ba dole hankalina ya kasa ƙwanciya ba, wata uku na ɗibarwa yarinyar nan, sai gashi har yau kimanin watan ta 6 kenan'
ke sanin kankine tun tana wata uku muka zo gun boka kan ya fidda ta a gidan, yace muje an gama amma har yanzu shiru, still yau ma irin abun da yafaÉ—a mana wata uku da suka wuce shi yau yakuma mai-maita mana,
Nifa har nafara tunanin an ya bazan canza wani malamin ba kuwa?".

Raliya ta ce
"Duk faÉ—in garinnan babu bokan da yakai malam na kan tudu iya ai ki kamar yankan wuka, ke kanki shai da ce wani irin guraren malamai ne bamu leka ba waya kai shi ai ki kamar yankan wuka,
Yanzu haka kiran da a ke tamin tun dazu É—in nan wani Alhaji ne da zamu haÉ—u yanzu haka kuÉ—in shi ya isa cikin account É—ina,
Duk wasu manyan garin nan masu bukatar harka babu wan da bana gogawa da su, duk kuma ta sana diyar ai kin malam na kan tudu ne. ke kanki kinsan yayi miki babban ai kin da mamanki da baban ki ma ba zasu iya yimiki shi ba,
dan haka bai ma kamata ki karaya da abin da yace miki ba, kidai jira É—in kamar yan da yace".

Numfashi Na'ima tasauke ta ce
"To shike nan amma wlh ko muryar yarinyar nan naji yana sani faÉ—uwar gaba, bare kuma na ganta bana kaunar nabuÉ—e idanuna na ganta cikin gidan".

Haka suka rika tattauna matsalar su da kulle-kullen su wan da su suka san ma a nar sa,sai da Raliya tabi gidan Na'ima tasau keta kafin tawuce gun Alhajin ta da ke jiran ta.

★★�
Chapter 20 · 0% Book details